Mu kwana lafiya
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu haɗu da ku don ɗorawa daga inda muka tsaya.
Fatan alheri.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman game da yaƙin Ukraine.
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi.
Umar Mikail ke cewa mu haɗu da ku don ɗorawa daga inda muka tsaya.
Fatan alheri.
Amurka ta ware dala miliyan 350 na taimakon kayan yaƙi da za ta bai wa Ukraine, kamar yadda Sakataren Harkokin Waje Antony Blinken ya sanar.
Matakin ya biyo bayan amincewar da Shugaba Joe Biden ya yi ce a yau Asabar.
"Taimakon zai ƙunshi ƙarin makamai na kai hari ga Ukraine don ta kare kan ta daga harin sama da ƙasa da take fuskanta," in ji shi cikin wata sanarwa.
Tuni Amurkar ta ware wasu makamai daga rumbunta da za ta aike wa Ukraine ɗin a ƙarshen 2021 da kuma Disamba. A cewar Blinken, Amurka ta kashe dala biliyan ɗaya wajen taimaka wa Ukraine a shekarar da ta gabata.
Jamus za ta aika wa Ukraine makaman harbe tanka ko kuma igwa 1,000 da kuma makami mai linzami da ake harbawa daga ƙasa zuwa sama 500, a cewar gwamnatin ƙasar ta Jamus.
Wannan yanƙuri alama ce ta babban sauyin da aka samu a daɗaɗɗun manufofin Jamus na ƙin tura makamai filin yaƙi.
"A irin wannan yanayi, wajibinmu ne mu taimaka wa Ukraine da iya abin da za mu iya don kare kanta daga dakarun Vladmir Putin," a cewar Shugaban Gwamnati Olof Scholz.
Idan muka ja gefe daga filin daga, ana ci gaba da tsangwamar Rasha sakamakon hare-haren da take kai wa kan Ukraine ɗin.
Ga halin da ake ciki yanzu:
Yayin da yaƙin da Rasha ta kai wa Ukraine ke rana ta uku, ƙasashen duniya na ci gaba da Allah wadai da shi da kuma ƙaƙaba wa Rashar takunkumai.
Zuwa yanzu, an kashe 'yan Ukraine 200 a cewar ma'aikatar lafiyar ƙasar.
Sai dai har yanzu ƙasashen Afirka ba su tsoma baki cikin rikicin ba ƙarara, in ban da kiran a zauna lafiya kawai da suke yi.
Abdulbaki Jari ya yi bayani a bidiyon sama kan yadda yaƙin zai shafi ƙasashen na Afirka.
Rasha da Ukraine ne kan gaba wajen noman alkama a faɗin duniya.
Tun da farar safiya muke kawo rahoton harin da aka kai kan wani gini a Kyiv babban birnin Ukraine.
Yanzu hukumomi sun tabbatar da faruwarsa cewa mutum biyu ne suka mutu.
Hukumar agajin gaggawa ta Ukraine ta ce an jikkata wasu mutum shida yayin harin.
Gwamnatin Najeriya na shawartar 'yan ƙasar da yaƙi ya ritsa da su a Ukraine da su tsallaka zuwa ƙasar Poland mai maƙotaka don samun taimako.
Wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta fitar ta shawarci 'yan Najeriya su shiga Poland ta kan iyakoki huɗu tsakaninta da Ukraine.
"Ma'aikatan jakadancin Najeriya da masu aikin sa-kai na nan suna jira da motoci don kwashe 'yan Najeriya a kan iyaka," a cewar sanarwar mai ɗauke da adireshin da ta ce 'yan Najeriya su nuna wa jami'an kan iyaka idan sun ƙarasa.
Tun ranar Alhamis Najeriya ta ce za ta shirya aikin ceto na musamman amma daga baya ta ce ba za ta iya ba har sai an buɗe filayen jiragen sama na Ukraine.
A yau Asabar Ministan Harkokin Waje na Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce ya gana da jakadun Ukraine da Rasha a Abuja babban birnin ƙasar.
Gwamnatin Nijar ta saki wasu shugabannin ƴan bindiga ciki har da kwamandojin Boko Haram, ƙarƙashin wani shiri na sulhu a ƙasar.
Shugaba Bazoum ne ya sanar da matakin a ranar Juma’a a wani taron tsaro tare da jami’an soji da na gwamnatinsa da sarakunan gargajiya, kamar yadda kafar talabijin ɗin ƙasar ta ruwaito.
“Akwai shugabannin ƴan ta’adda guda tara, An ba mu shawarar mu sake su, waɗanda kuma na gana da su a fadar shugaban ƙasa saboda ina neman zaman lafiya, kamar yadda aka ambato shugaba Bazoum na cewa.
Wasu mjiyoyin gwamnati sun ce wannan ne karon farko da aka fito aka bayyana sakin waɗanda ake zargi da ta’addanci a Nijar.
Nijar ta daɗe tana fama da hare-hare daga mnayaƙan IS a yammaci da Boko Haram da Iswap da yankin kudu maso gabashi kusa da kan iyaka da Najeriya
Jam'iyya mai mulki a Kenya ta tsige mataimakin shugaban kasar William Ruto a matsayin daya daga cikin shugabanninta, a daidai lokacin da al'ummar kasar ke shirin gudanar da zaben shugaban kasa.
A wani gangami da aka gudanar a birnin Nairobi, jam'iyyar Jubilee ta bayyana shugaba Uhuru Kenyatta, wanda wa'adinsa zai kare a wannan shekara, a matsayin shugabanta na tsawon wasu shekaru biyar.
Mista Kenyatta ya amince da dan adawa Raila Odinga a matsayin dan takarar shugaban kasa; shi ma yana wajen taron.
Bayan jam'iyyarsa ta ki tsayar da shi, mataimakin shugaban kasa William Ruto zai tsaya takarar shugaban kasa, amma a wata jam'iyyar siyasa ta daban.
geMutane da dama na ci gaba da tsere wa yaƙi a Ukraine - kusan mutum 100,000 suka tsallaka zuwa Poland, kamar yadda hukumar kula da kan iyaka ta Poland ta bayyana.
"Masu gudun hijira na ƙara yawa," in ji mai magana da yawun hukumar Anna Michalska.
Sama da mutum 20,000 suka iso tun ƙarfe shida na safe a ranar Asabar, in ji ta.
Gwamnatin Poland ta yi alƙawalin karɓar masu gujewa yaƙi a Ukraine tare da ba waɗanda ba su san inda za su ba mafaka na wuccin gadi
A ranar Alhamis ne duniya ta wayi gari da abin da aka dade ana kokarin kauce mawa.
Rasha ta kaddamar da hare-hare kan birane da dama na kasar Ukraine.
Da alama Shugaba Putin ya nuna cewa da gaske yake yi, matukar kasashen yamma da kungiyar NATO ba su amince da bukatunsa ba.
Shin me hakan yake nufi, wane tasiri rikicin zai yi ga duniya, kuma mece ce mafita?
Wadannan ne abubuwan da aka tattauna a cikin shirin Ra’ayi Riga na wannan mako.
Gwamnatin Birtaniya ta ce da ita da ƙasashe 25 sun amince su samar da ƙarin agaji ga Ukraine.
Ministan dakarun Birtaniya James Heappey ne ya bayyana haka a hirar da rediyon BBC 4.
Ya ce suna da aiki da sauran ƙasashen kan yadda za a tabbatar da taimakon soji ya kai ga hannun Ukraine, sai dai ba yi ƙarin bayani ba.
Ya ce mai yiyuwa ne gwamnatin Kremlin ta kasance mai yin tunani kan tsayin turjiyar da Ukraine tare da amincewa da cewa akwai hatsarin da za ta iya fuskanta na ramuwa kan hare-haren da ake kai wa Ukraine.
Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Alhaji Atiku Abubakar ya kai wa tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ziyara a gidansa da ake Abeokuta.
"Na yi farin ciki da ganin tsohon maigidana, Cif Olusegun Obasanjo, a safiyar yau yayin wata ziyarar ban girma da na masa a gidansa na Abeokuta," kamar yadda Atiku ya rubuta a shafinsa na Twitter tare da wallafa hotunansa tare da Obasanjo.
Ko da yake Atiku bai fito ya ayyana cewa zai tsaya takara ba a zaɓen 2023 amma ana ganin ziyarar ba ta rasa nasaba da manufarsa ta takarar shugaban ƙasa.
Bayan ganawa da Obasanjo, ya shaida wa manema labarai cewa ba da daɗewa zai ayyana takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2023.
Atiku ne ya yi wa Obasanjo mataimaki tsakanin 1999 zuwa 2007, kuma ya sha tsayawa takarar shugaban ƙasa tun zaben 2007 da 2011 da 2019.
Kamfanin mai na NNPC a Najeriya ya ce yana da wadataccen man fetur don rarrabawa a faɗin ƙasar.
An shafe kusan mako biyu ana wahalar man fetur a sassan Najeriya.
A wata sanarwa da NNPC ya fitar ya jaddawa ƴan Najeriya cewa akwai isasshen man fetur kuma kamfanin na aiki da abokan hulɗarsa don tabbatar da cewa ya isa a kowane ɓangare na ƙasar.
NNPC ya kuma yi kira ga ƴan Najeriya su ci gaba da haƙuri yayin da ake ƙoƙarin ganin abubuwa sun koma daidai.
Ministan lafiya na Ukraine Viktor Lyashko ya ce jimillar mutum 198 aka kashe da suka ƙunshi yara guda uku kawo yanzu bayan ƙaddamar da yaƙin da Rasha ta yi.
Wasu mutum 1,115 suka jikkata, da suka ƙunshi yara 33, kamar yadda ya sanar da shafinsa na Facebook.
Shugaban sojin Chadi Mahamat Idriss Deby ya yi wa gwamnantinsa garanbawul, watanni tara bayan hawansa, kamar yadda shafin jaridar Tchadinfos.com ya ruwaito.
An naɗa wasu sabbin ministoci 11 da za su yi aiki ƙarƙashin gwamnatin Firaminista Pahimi Padacke Albert, a cewar rahoton.
Sauyin da aka yi ya shafi ma’aikatar tsaro da tsare-tsare da kuma man fetur.
Mahamat Deby ya naɗa Janar Idriss Dokony Adiker a matsayin ministan tsaron al’umma inda ya gaji Janar Souleyman Abakar Adam.
Yanzu Hamid Koua shi ne ministan tattalin arziki da tsare-tsare, wanda tsohon minista ne na kula da harakokin majalisa. Yanzu ya maye gurbin Issa Doubragne.
Magajin garin Kiev Vitali Klitschko ya ce mutum 35 suka jikkata a daren da aka shafe ana gwabza faɗa a Kiev
Sun ƙunshi yara biyu, in ji shi.
Ba a san ko yana nufin fararen hula ba ne kawai.
Ya ƙara da cewa babu wani sojan Rasha a yanzu haka a Kiev, amma ya ce akwai masu goyon bayan Rasha da ake aiki.
An samu hotunan yadda makami mai linzame da aka harba ya tarwatsa wani bene na rukunin gidajen mutane da safiyar Asabar.
Hotunan sun nuna yadda kusan hawa biyar na benen suka tarwatse.
Hukumomi ba su bayyana adadin hasarar rai da aka yi ba, yayin da ake kokarin kwashe waɗanda harin ya rutsa da su.
Makamai da kayan aiki na kan hanyarsu daga Faransa zuwa Ukraine, yayin da kasashen Yamma ke kai agaji ga Ukraine a yakin da suke da sojojin Rasha da ke ci gaba kutsawa ƙasar.
Shugaba Zelensky ya wallafa a shafinsa na twitter cewa ya yi magana da shugaba Macron na Faransa da sanyin safiyar Asabar.
"Ƙawancen yaƙi da yaƙi na aiki!" kamar yadda Mista Zelensky ya wallafa a shafinsa na Twitter.
A ranar Asabar, Mista Macron ya saka wani bidiyo na kansa yana bayyana cewa: "Yakin zai dore - dole ne mu shirya masa!"
An harba makamai biyu masu linzame a yankin kudu maso yammacin Kiev na Ukraine da safiyar Asabar, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito.
Hukumomin birnin sun ce ɗaya daga cikin harin ya shafi wani dogon gini na rukunin gidaje
Reuters ya ruwaito cewa ɗaya daga cikin harin ya shafi yankin da kusa da filin jirgin sama na Zhuliany