Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Magoya bayan masu da'awar Jihadi 'na jin daɗin' kutsen da Rasha ta yi a Ukraine

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Rasha da Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. Ukraine ta yanke duk wata hulɗa ta diflomasiyya da Rasha

    Ukraine ta ce ta yanke duka wata alaƙa ta diflomasiyya tsakaninta da Rasha bayan Rashar ta kutsa cikinta da niyyar yaƙi.

    Shugaban Ukraine ɗin Volodymyr Zelensky ne ya bayyana hakan a yayin wani jawabi ga manema labarai.

  2. Boris Johnson zai yi jawabi game da kutsen Rasha cikin Ukraine

    Firaiministan Birtaniya Boris Johnson zai yi jawabi ga Birtaniya kan yaƙin da sojojin Rasha suka ƙaddamar kan Ukraine da kuma martanin da Birtaniyar ta mayar.

    Jawabin nasa zai biyo bayan sanarwa da ƴan majalisar wakilai ta Birtaniya za ta fitar da misalin 17:00 agogon GMT.

    Ana sa ran firaiministan zai sanar da sabbin takunkuman da Birtaniya za ta saka wa Rasha bayan zaman da majalisar ministoci ke yi a safiyar yau.

  3. Ukraine ta dakatar da sufurin jiragen sama na fasinja a ƙasar

    Hukumar kula da sararin samaniya a Ukraine ta dakatar da sufurin jiragen sama na fasinja a daidai lokacin da ƙasar ke fuskantar hare-hare.

    Ta dakatar da duka jirage daga Kyiv babban birnin Rasha da misalin 02:45 agogon ƙasar sakamakon barazanar da ake fuskanta ta sararin samaniyar ƙasar.

  4. Ayarin motocin soji na Rasha ya ratsa cikin Ukraine

    Dakarun da ke gadin iyakokin Ukraine na DPSU sun saki wasu hotuna inda suka ce ayarin motocin sojin Rasha ne da suke tsallakawa cikin kudancin Ukraine wadda Moscow ta karɓe a 2014.

    DPSU sun bayyana cewa sojojin Rasha sun harba makaman atilari kafin suka tura motocin yaƙinsu suka tsallaka.

    Ukraine ta bayyana cewa ayarin sojojin Rasha sun ratsa ƙasarta ta arewa daga Belarus haka kuma sun shiga ta gabas daga Rashar.

  5. Putin ya dawo da yaƙi Turai - Ursula von der Leyen

    Shugabar Hukumar Tarayyar Turai, Ursula von der Leyen, ta soki Shugaban Rasha Vladimir Putin inda ta ce ya dawo da yaƙi nahiyar Turai.

    Ta bayyana haka ne a yayin da take jawabi a Brussels.

    Ta sanar da cewa za a saka takunkumai masu ƙarfi nan ba da jimawa ba domin raunata tattalin arziƙin Rasha da kuma ci gabanta.

  6. Ƙasashen Turai sun yi Allah-wadai da matakan Rasha

    Cikin gaggawa, ƙasashen Turai sun yi Allah-wadai da matakan da Rasha ta ɗauka na ƙaddamar da yaƙi kan Ukraine.

    Wani mai magana da yawun gwamnatin Jamus ya bayyana cewa shugaban gwamnatin ƙasar, Olaf Scholz ya yi magana da Shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy kuma ya tabbatar masa da Jamus za ta goya masa baya.

    Shi ma Firaiministan Birtaniya Boris Johnson ya ce ya kaɗu da harin da Rasha ta kai wa Ukraine inda ya ce Birtaniya za ta mayar a martani.

    Shi ma Firaiministan Italia Mario Draghi ya ce matakin da Rasha ta ɗauka bai dace ba.

  7. Labarai da dumi-dumi, Ukraine ta ce mutum bakwai sun rasu a harin bam ɗin da Rasha ta kai mata

    Aƙalla mutum bakwai aka sanar da mutuwarsu a wani harin bam da dakarun Rasha suka kai a Ukraine, kamar yadda ƴan sanda a Ukraine ɗin suka sanar.

    Hukumomin ƙasar sun bayyana cewa wani hari da aka kai wani sansanin soji da ke a Podilsk a wajen Odessa ya yi sanadin mutuwar mutum shida da kuma raunata mutum bakwai.

    Haka kuma akwai mutum 19 da ba a san inda suke ba.

    Haka kuma an tabbatar da cewa mutum guda ya rasu a birnin Mariupol.

  8. Sojojin Ukraine sun yi iƙirarin harbo jiragen Rasha 6

    Rundunar sojin Ukraine ta bayyana cewa ta harbo jiragen Rasha biyar da kuma jirgi ɗaya mai saukar ungulu na ƙasar.

    A wata sanarwa da dakarun Ukraine suka fitar, sun bayyana wa jama'a cewa su kwantar da hankalinsu kuma su yi imani da cewa za su ba su kariya.

    Sai dai ma'aikatar tsaro ta Rasha ta yi watsi da musanta wannan iƙirarin na Ukraine.

  9. Barkanmu da safiya

      • Marubuci, Mustapha Musa Kaita
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multi-Media Broadcast Journalist

    Jama'a barkanmu da safiyar Alhamis, 24 ga watan Fabrairun 2022. A yau ma za mu ci gaba da kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da wasu sassan duniya.

    Za ku iya ziyartar shafinmu na Facebook ko Twitter ko kuma Instagram domin bayyana ra'ayoyinku kan irin labaran da muke wallafawa ko kuma tafka muhawara a kai.