Magoya bayan masu da'awar Jihadi 'na jin daɗin' kutsen da Rasha ta yi a Ukraine

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Rasha da Ukraine.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Mustapha Musa Kaita

  1. Rufewa

    To jama'a a nan muka kawo karszhen labarai da rahotanni da muke kawo muku kai tsaye na yadda ta kaya a Ukraine da Rasha a yau.

    Sai kuma gobe da safe in Allah Ya kai mu za mu ci gaba daga inda muka tsaya.

    Amma za ku iya komawa kasan shafin nan don karanta dukkannin wainar da aka toya a yau din.

    Sannan akwai labarai da za mu ci gaba da wallafa muku a shafin namu duk kan wannan hali.

    Kar ku manta, BBC Hausa na kawo muku duniya a tafin hannunku a ko yaushe a shafukanta na intanet BBC Hausa da BBCHausa Facebook da Instagram da Twitter.

  2. Zanga-zangar ƙin jinin yaƙi ta ɓarke a Rasha

    Putin

    Asalin hoton, PA Media

    To can kuma a Rashar ana ta samun karuwar masu zanga-zangar ƙin jinin yaƙi a kusan garuruwa da birane 40 a fadin kasar.

    Hotunan bidiyo da aka sanya a shafukan intanet na nuna daruruwan mutane na maci suna cewa ba sa son yaki a Moscow sa St-Petersburg da Siberia da yammacin Rasha.

    A kalla mutum 735 aka kama a wuraren waɗannan zanga-zangar a faɗin Rasha a yau, da suka haɗa da fiye da 330 a Moscow, a cewar OVD-Info, da ke bin diddigin waɗanda aka kama a zanga-zangar ƴan adawar.

    Am ga hotunan dandazon mutane a kusa da fadar Kremlin ta Rasha.

  3. Za mu sayo na’urorin harba makamai daga Turkiyya don maganin 'yan binidiga - El-Rufa'i

    Gwamnan jihar Kaduna da ke shiyyar arewa maso yammacin Najeriya ya koka cewa matsalar hare-haren ‘yan fashin daji na dada kamari a shiyyar kuma kasar ba ta da isassun jami’an tsaron ke iya magance ta.

    Kan haka ne ya ce shi da wasu gwamnonin jihohi biyar na yankin suka yanke shawarar shigowa da na’urorin harba makamai da ake iya sarrafawa daga nesa daga kasar Turkiyya domin taimakawa sojojin saman a kasar wajen murkushe su.

    Gwamna Nasir El-Rufai ya bayyana haka ne a dazu yayin wani taron manema labarai a fadar Shugaban kasar da ke Abuja.

    Ga dai Karin bayanin ya yi wa Haruna Shehu Tangaza:

    Bayanan sautiHirar Haruna Tangaza da El-Rufa'i kan shigar da makaman yaƙi da ƴan bindiga daga Turkiyya
  4. Amurka ta sanya wa Rasha karin takunkuman da za su 'ƙuntata mata'

    Shugaban Amurka Joe Biden ya sanar da sanya wa Rasha karin takunkumi, da ya ce za su kara ƙuntata mata, a nan take da kuma nan gaba.

    A wani jawabi da ya yi wanda aka yada ta talabijin Mista Biden ya ce, Vladimir Putin ya zabi yaki, ya kawar da kansa daga dukkanin yunkurin gaskiya na shawo kan damuwar da Rasha ke nunawa ta tsaro.

    Shugaban na Amurka ya ce akwai sabbin tsauraran matakai na rage abubuwan da za a rika shigarwa Rasha.

    Sannan kuma kungiyar kasashe masu karfin tattalin arziki ta G7, za ta hana kamfanonin Rasha da sauran harkokin kasuwancinta cinikayya da manyan kudaden kasashen waje.

    Biden ya kara da cewa matakin da Amurka da sauran kasashe suka dauka zai illata tattalin arzikin Rasha tsawon shekaru.

  5. Daga Ukraine - halin da ake ciki zuwa yanzu

    Ukraine map

    Rahotanni na cewa an samu barkewar mummunan fada a gabashin Ukraine bayan da dakarun Rasha suka kutsa kasar.

    Ukraine ta ce manyan motocin yaki na Rasha sun shiga kasar ta wurare da dama, ciki har da ta yankin Crimea da ta mamaye sannan kuma da Belarus daga baryar arewa.

    Mazauna birnin na biyu mafi girma a kasar, Kharkiv, sun ce ana jin tagogin gidaje suna ta girgiza, sakamakon barin wuta da rokoki da ke ta fashewa, a ba-ta kashin da aka fara tsakanin sojojin Ukraine din da na Rasha.

    An bayar da rahoton mutuwar farar hula 'yan Ukraine sama da 30, wadanda suka hada da akalla mutum 18 da aka kashe a kusa da tashar jirgin ruwa ta Odessa a wani hari na makami mai linzami.

    Gwamnatin Rasha ta ce ta kai hare-hare da makami mai linzami a kan sansanonin soji da filayen jiragen sama da suka hada da, babban filin jirgin sama na Kyiv da kuma filin jirgin Ivano-Frankivsk da ke yammacin kasar.

    Da yake sanar da kaddamar da farmakin na soji Shugaba Putin ya yi gargadin cewa duk wani tsoma baki ko katsalandan da wata kasa za ta yi, za ta gamu da martanin da ba ta taba gani ba a tarihi.

    A martaninsa Shugaban Amurka Joe Biden ya ce za a dora wa Rasha alhakin duk abin da ya biyo baya kan hrin da ta kai b gaira ba dalili.

    A nan gaba ne zai yi jawabi kan matakin da Amurka za ta dauka a kan rashar.

    Dan majalisar dokoki na Demokrat Jim Himes wanda ke kwamitin bayanan sirri ya ce manufar ita ce mayar da Rasha saniyar ware a duniya.

    Ya ce Amurka za ta yi ainahin abin da ta yi alkawari, kuma Shugaban kasa zai tabbatar da hakan yau, wanda shi ne abin da za mu yi jagora da shi, abin da muke fata zai kasance tsattsauran takunkumin tattalin arziki.

  6. Magoya bayan masu da'awar Jihadi 'na jin daɗin' kutsen da Rasha ta yi a Ukraine

    jihadists

    Asalin hoton, IS

    Magoya bayan ƙungiyoyin jihadi a faɗin duniya sun yi maraba da kutsen da Rasha ta yi wa Ukraine.

    Yawanci sun yi ta bayyana ra'ayoyinsu ne a shafukan sada zumunta.

    A wasu kalamai da suka wallafa a shafukan sada zumunta, sun bayyana fatansu cewa yaƙin zai koma na Rasha ne da Amurka ta yadda ƙungiyoyi masu da'awar jihadi za su samu damar cin karensu babu babbaka ta hanyar faɗaɗa ikonsu.

    Da yawan masu wannan bayani na fatan yakin zai rage karfin ikon sojin Rasha a Syria da kuma tallafin da take bai wa gwamnatin Syriyan.

  7. Lamurra na ƙara hargitsewa a Ukraine

    Can a Kyiv babban birnin Ukraine din kuwa jin karar fashe-fashe da kuma jiniya da ke ta tashi, mazauna birnin sun shiga firgici, inda suke ta in-ba-ka-yi-ba-ni wuri, wajen neman mafaka a tashoshin jirgin kasa.

    Sannan kuma suna layi a wuraren cirar kudi na banki, da gidajen mai da manyan kantunan sayar da kayan masarufi.

    Yayin da 'yan Ukraine din suka wayi gari da abin da suka dade suna jin tsoro na harin na Rasha, can kuma a wasu sassan kasar, cuncurundon ababan hawa ne ake gani na wadanda suke kokarin ficewa.

    Mai magana da yawun fadar shugaban kasar, ya ce Rasha na so ta ribaci firgicin da ta jefa fararen hula ne kawai, yana mai shawartar jama'a da kada su karaya.

    To amma wannan ga alama bai kwantar da hankali ba, domin tuni wasu 'yan kasar suka fara tsallaka iyakar kasar ta kudu maso yamma zuwa cikin Romania domin samun mafaka.

    Ita ma Poland tuni ta samar da wurare takwas na karbar mutane, ko da za a fara neman tsira, inda za ta samar da abinci da kula da lafiya da kuma samar da bayanai.

    Kafafen watsa labarai a Moldova sun bayar da rahotannin gomman motoci da ke layi a kan iyakarta da Ukraine din.

  8. Takunkumai 10 da Birtaniya ta saka wa Rasha

    Waɗannan su ne jerin takunkuman da Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya sanar da saka su a kan Rasha:

    • Za a riƙe dukkan ƙadarorin bankunan Rasha kuma za a cire ta daga tsarin harkokin kuɗin Birtaniya. Wannan zai hana su samun damar amfani da kuma cire kuɗaɗe ta Birtaniya. Hakan ya haɗa da rufe bankin VTB ba tare da ɓata lokaci ba
    • Majalisar Dokoki za ta dakatar da manyan kamfanonin Rasha da kuma ƙsar daga aron kuɗaɗe a kan kasuwannin Birtaniya
    • Za a riƙe ƙadarorin mutum 100
    • Za a haramta wa jiragen kamfanin Aeroflot sauka a Birtaniya
    • Za a dakatar da lasisan ba da damar a yi abubuwan da suka shafi harkokin soji
    • A cikin kwanaki masu zuwa Birtaniya za ta dakatar da fitar da abubuwan fasaha da kuma kayayyakin tace man fetur
    • Za a ƙayyade yawan kuɗaɗen da ƴan Rasha za su iya saka wa a asusun bankunan Birtaniya
    • Ya ce akwai yiwuwar a cire Rasha daga tsarin aika kuɗaɗe na ƙasashen yamma
    • Irin wannan mataki zai shafi Belarus a kan rawar da take takawa kan yaƙar Ukraine da ake yi
    • Birtaniya za ta gabatar da dokar aikata miyagun laifuka da suka shafi harkokin kuɗaɗe gaban majalisa kafin a tafi hutun Ista.
  9. Shugaban ƙasar Ukraine Zelensky ya sanya kakin soja ya yi wa 'yan ƙasa jawabi

    Zelesenky

    Asalin hoton, AFP

    Shugaba Zelensky ya sake yi wa ƴan ƙsar Ukraine jawabi da rana a yau, inda aka nuna shi sanye da kakin soja maimakon baƙar kwat din da ya saba sanyawa.

    A jawabinsa na ɗazun nan ya bayyana yaƙin a matsayi "sautin labulen ƙrfe da ya faɗo yake rufe Rasha daga duniyar da ta ci gaba". yana mai cewa "aikinmu shi ne mu tabbatar wannan labulen bai faɗo kan iyakar Ukraine ba."

    Ya kuma yi magana a kan dakatar da ayyuka da aka yi tare da ikirarin cewa dakarun Ukraine suna samun nasarar kare yankin gabashin Donbas, da kuma yi faɗa a kusa da Kharkiv.

    Zelensky ya ce yankin da ya fi bayar da matsala shi ne Kherson a kudancin ƙasar, inda dakarun Rasha suka nausa arewa daga yankin Crimea da suka mamaye.

    A raewa, ya ce maƙiya na ci gaba da kutsawa cikin yankin, ya kuma bayyana tsananin yaƙin da ake yi a Chernobyl.

    Sannan ya yi magana a kan dakarun da aka rasa da kuma sojojin Rasha da aka kama.

    Zelensky ya ce an lalata da yawan jirage da motocin yaƙin Rasha, kuma mun lura cewa hakan ya kaɗa ƴan Rasha da dama.

  10. Kutse salon ƙasashen yamma na malkwaɗa zance ne in ji China

    XI China

    Asalin hoton, Getty Images

    Akwai matuƙar buƙatar jin ta bakin China kan irin martanin da za ta mayar.

    Martanin na farko kira ta yi da a daina amfani da kalmar kutse, tana mai cewa "salo ne da kafafen yaɗa labaran ƙasashen yamma ke amfani da shi".

    Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce "ba za mu yi riga-malam masallaci ba".

    Wani babban jami'in diflomasiyya Wang Yi ya ce China ta fahimci batun tsaron da Rasha ke nuna damuwa a kai.

    China da Rasha suna da ƙawance na ƙut da ƙut da nufin daƙile tasirin Amurka, wanda aka ƙulla a lokacin da Shugaba Putin da Shugaba Xi suka gana kafin Gasar Olympics ta hunturu a Beijing.

    China ta shaida wa ƴan kasarta da ke Ukraine cewa su yi ta ɗaga tutar China don kare kansu.

  11. An saka dokar hana fita a birnin Kyiv

    Ukraine

    Asalin hoton, Reuters

    A 'yan awannin da suka wuce ne Magajin Garin birnin Kyiv Vitaliy Klitschko ya sanar da dokar hana fita a fadin birnin.

    Ya ce: "Jama'a! Kyiv na gabatar da dokar hana fita daga yau. Za ta fara aiki daga tsakanin ƙarfe 10 na dare zuwa 7 na safe a kullum.

    "Hakan ya zama dole saboda tsaron al'ummar birnin a yayin da ake tsaka da rikicin soji."

    Motocin haya ba za su yi aiki a ba a yayin da dokar ke aiki, amma jiragen ƙasa za su ci gaba da aiki a matsayin mafaka.

  12. Me ke faruwa a yanzu haka?

    Ukraine

    Asalin hoton, AFP

    Lamari ne na yadda abubuwa ke faruwa da sauri-sauri, amma a takaice dai ga abin da za mu iya ce muku yana faruwa a yanzu haka.

    Dakarun Rasha sun kutsa Ukraine daga ɓangarori daban-daban, da suka haɗa da yankunan ƴan aware da Donbas daga gabas, Belarus daga arewa da kuma daga yankin Crimea daga kudu.

    Faɗan ya fi ƙamari ne daga gabas.

    Mazauna Kharkiv, birni na biyu mafi girma a Ukraine sun ce, tagogin gidaje sun yi ta rugurgujewa sakamakon ƙarfin fashewar bama-bamai, a yayin da dakarun Ukraine da na Rasha ke musayar wuta.

    Amma kuma ana yin faɗan ma a kusa da babban birnin ƙsar Kyiv daga arewa da kuma a tashar jiragen ruwa da ke gaɓar tekun Black Sea da kuma a biranen Odesa da Mariupol daga kudu.

    Rasha tana ta kai hare-haren sama a sansanonin sojin Ukraine da kuma filayen jiragen sama, inda faɗa ke ƙara ƙamari a kusa da wani muhimmin filin jirgin sama kusa da Kyiv.

    Dakarun Ukraine sun yi ikirarin cewa sun harbo a ƙalla jiragen yaƙin Rasha shida, yayin da Rasha ta yi ikirarin lalata fiye da sansanonin soji fiye da 70 a Ukraine.

    'Yan Ukraine da dama na neman mafaka ko ƙoƙarin barin manyan birane a faɗin ƙasar, inda dubban mutane ke tsere wa daga Kyiv.

  13. Abubuwan da suka faru zuwa yanzu kan rikicin Ukraine da Rasha

    Rasha and Ukraine presidents

    Asalin hoton, BBC/Getty

    Masu bin mu a wannan shafi na BBC Hausa barkanmu da la'asariya idan a Afrika kuke, idan kuma daga yankin Turai ne barkanku da rana.

    Na yankin Asiya muna muku barka da dare sannan muna yi wa na yankin Amurka barka da hantsi.

    Idan yanzu kuke shigowa shafin, to muna kawo muku labarai ne kan rikicin Ukraine da Rasha da yake ƙara ƙamari a yau.

    Kuna iya komawa ƙasan shafin don karanta abubuwan da suka riga suka faru waɗanda muka wallafa muku kamar;

    • Ukraine ta dakatar da sufurin jiragen sama na fasinja a ƙasar
    • Ayarin motocin soji na Rasha ya ratsa cikin Ukraine
    • Sojojin Ukraine sun yi iƙirarin harbo jiragen Rasha 6
    • Ukraine ta ce mutum bakwai sun rasu a harin bam ɗin da Rasha ta kai mata
    • Ukraine ta yanke duk wata hulɗa ta diflomasiyya da Rasha

    Za kuma mu ci gaba da kawo muku wasu sabbin bayanan.

    Sunana Halima Umar Saleh, zan ci gaba da jan ragamar shafin bayan da abokin aikina Mustapha Kaita ya rike shi tun da safe.

    Ku garzaya shafukanmu na sada zumunta da muhawara don bayyana ra'ayoyinku.

  14. Najeriya ta ce ta shirya kwaso ƴan ƙasarta da ke Ukraine

    Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa a shirye take ta kwashe ƴan ƙasarta da ke son barin Ukraine bayan Rasha ta kutsa ƙasar.

    A wata sanarwa da gwamnatin Najeriyar ta fitar ta hannun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, ta ce ta yi mamaki kan harin da Rasha ta kai ƙasar.

    Wata mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar Francisca Omayuli ta bayyana cewa ofishin jakadancin Najeriya a Ukraine ya tabbatar mata da cewa ƴan Najeriya da ke Ukraine za su kasance cikin tsaro kuma ana ɗaukar matakai na kwashe waɗanda suke so su bar ƙasar

  15. Jama'a na neman mafaka a Ukraine saboda firgici

    ..

    Asalin hoton, Getty Images

    A Kyiv babban birnin Ukraine, kuwa jin ƙarar fashe-fashe da kuma jiniya da ke ta tashi, mazauna birnin sun shiga firgici, inda suke ta in-ba-ka-yi-ba-ni wuri, wajen neman mafaka a tashoshin jirgin ƙasa, suna kuma layi a wuraren cirar kuɗi na banki, da gidajen mai da manyan kantunan sayar da kayan masarufi.

    Yayin da 'yan Ukraine ɗin suka wayi gari da abin da suka daɗe suna jin tsoro na harin na Rasha, can kuma a wasu sassan kasar, cuncurundon ababan hawa ne ake gani na waɗanda suke kokarin ficewa.

    Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasar, ya ce Rasha na so ta ribaci firgicin da ta jefa fararen hula ne kawai, yana mai shawartar jama'a da kada su karaya.

    To amma wannan ga alama bai kwantar da hankali ba, domin tuni wasu 'yan kasar suka fara tsallaka iyakar ƙasar ta kudu maso yamma zuwa cikin Romania domin samun mafaka.

    Ita ma Poland tuni ta samar da wurare takwas na karbar mutane, ko da za a fara neman tsira, inda za ta samar da abinci da kula da lafiya da kuma samar da bayanai.

    Kafafen watsa labarai a Moldova sun bayar da rahotannin gomman motoci da ke layi a kan iyakarta da Ukraine din.

    .

    Asalin hoton, Getty Images

  16. Shugaban Lithuania ya saka dokar ta-ɓaci a ƙasar

    Shugaban ƙasar Lithuania ya saka dokar ta-ɓaci kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito.

    Gitanas Nausėda ya bayyana cewa a shirye yake ya tura sojoji domin kare iyakokin ƙasarsa don guje wa abin da ya kira "yiwuwar takura da tsokana sakamakon adadi mai yawa na dakarun soji a Rasha da Belarus".

    Shi ma Firaiministan Estonia wato Kaja Kalas wanda ƙasarsa ke da iyaka da Rasha ya bayyana wa BBC cewa za su yi iya bakin ƙoƙarinsu domin taimaka wa Ukraine inda ya ce har makamai za su iya tura musu.

  17. Wuta na ci daf da hedikwatar hukumar leƙen asiri ta Ukraine

    .

    Asalin hoton, Reuters

    Game da labarin baya da muka kawo muku na baƙin hayaƙi da aka ga yana tashi daga hedikwatar hukumar leƙen asiri ta Ukraine, rahotanni na cewa wutar na ci ne a daf da ginin hedikwatar kuma ginin hukumar lafiyarsa ƙalau.

    Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana cewa an ga wasu mutane sanye da kayan sarki suna jefa jakunkuna a cikin wutar.

    Ukraine ɗin ta bayyana cewa an kai hari a wasu daga cikin sansanonin sojinta.

  18. Labarai da dumi-dumi, An hangi hayaƙi na tasowa daga hedikwatar hukumar leƙen asiri ta Ukraine

    ..

    Asalin hoton, Reuters

    An hangi baƙin hayaƙi na tasowa daga hedikwatar hukumar leƙen asiri ta Ukraine a birnin Kyiv.

    Ukraine ta bayyana cewa makaman roka da Rasha ta harba sun sauka a wasu daga cikin sansanonin sojinta a safiyarnan.

    Za mu ci gaba da kawo muku bayanai dangane da wannan labarin...

  19. Ghana ta buƙaci ƴan ƙasarta da ke Ukraine su nemi mafaka

    .

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma'aikatar harkokin wajen Ghana ta buƙaci ƴan ƙasarta da ke zaune a Ukraine da su nemi mafaka a gidajensu ko kuma wuraren da gwamnatin ƙasar ta keɓe na fakewa bayan harin da Rasha ta kai wa ƙasar.

    Sama da ƴan ƙasar Ghana dubu ɗaya ne ke zaune a Ukraine inda suke karatu ko kuma aiki, kamar yadda ma'aikatar ta bayyana.

    Sai dai ƙungiyar ɗalibai ta ƙasar tana buƙatar gwamnatin ta Ghana ta mayar da hankali wajen kwashe ɗaliban daga sassan Ukraine da ke cikin barazana har sai abubuwa sun lafa.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  20. Shugaba Buhari ya isa Jihar Nasarawa

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa Jihar Nasarawa domin ziyarar aiki ta kwana biyu.

    Shugaban ya je jihar ne domin ƙaddamar da wasu daga cikin ayyukan da gwamnan jihar, Abdullahi A. Sule ya yi a jihar.

    Gidan talabijin na Najeriya wato NTA ya wallafa bidiyon isar Shugaba Buhari Jihar Nasarawa inda aka nuna yadda gwamnan jihar da muƙarrabansa da wasu gwamnoni suka tarbi shugaban.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X