Zanga-zanga ta ɓarke a Morocco kan adawa da tsadar kayayyakin masarufi
Zanga-zanga ta ɓarke a biranen Morocco kan adawa da tsadar kayayyakin masarufi yayin da kuma ƴan ƙasar ke tuna shekara 11 da aka cika da ƙaddamar da fafutikar neman sauye-sauye a ƙasar.
A ranar 20 ga watan Fabrairu aka ƙaddamar da fafutikar neman sauyi da adawa da rashawa a 2011 da ake zanga-zangar ƙasashen Larabawa.
Daruruwan mutane ne suka fito zanga-zanga a ranar Lahadi a birnin Casablanca, suna neman a saki fursunonin siyasa da ake tsare da su.
Masu zanga-zangar sun ce babu ɗaya daga cikin buƙatunsu da aka cimma a tsawon shekaru 11.
An kuma gudanar da zanga-zanga a biranen Rabat da Tangiers.
Fari da annobar korona sun yi tasiri ga taɓarɓarewar tattalin arzikin Morocco.