Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Rikicin Ukraine: Putin ya amince da 'yancin kai na yankunan Ukraine biyu

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi na kai-tsaye.

    Mu haɗu da ku gobe Talata don samun labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Umar Mikail ke muku fatan alheri.

  2. Za mu mayar wa Rasha martani cikin haɗin kai da jajircewa - Tarayyar Turai

    Ana ta ci gaba da Allah wadai da matakin Rasha na amincewa da 'yancin kai na wasu yankunan Ukraine.

    Ƙungiyar Tarayyar Turai ta European Union (EU) na daga cikin waɗanda suka mayar da martani zuwa yanzu.

    "Amincewa da 'yancin kai na wasu yankunan Ukraine da suka ɓalle karya dokokin ƙasa da ƙasa ne ƙarara da kuma keta 'yancin Ukraine da yarjejeniyar Minsk," a cewar Shugabar EU Ursula von der Leyen.

    "EU da ƙawayenta za su mayar da martani cikin haɗin kai da jajircewa da kuma mara wa Ukraine baya."

  3. Labarai da dumi-dumi, Ayyana yankunan Ukraine matsayin masu zaman kansu ya saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa - Birtaniya

    An tambayi Firaministan Birtaniya Boris Johnson game da jawabin da Shugaban Rasha Vladmir Putin ya yi.

    Ya ce ayyana yankunan da suka ɓalle daga Ukraine a matsayin masu cin gashin kansu "ya yi matuƙar saɓa wa dokokin ƙasa da ƙasa".

    "Wannan yi wa 'yancin Ukraine karan-tsaye ne," in ji shi. "Wannan saɓa yarjejeniyar Minsk ne kuma ina tunanin wannan mummunar alama ce."

    Shugaba Putin ya ayyana yankunan Donetsk da Luhansk da ke gabashin Ukraine a matsayin masu cin gashin kansu bayan sun ayyana ɓallewa daga ƙasar.

  4. Wasu ne ke iko da Ukraine daga waje - Putin

    Shugaba Putin ya koma kan gwamnatin Ukraine, inda ya soki mahukuntan ƙasar.

    Ya siffanta abubuwan da suka faru a 2014 - waɗanda suka jawo saukar shugaban Ukraine da ke goyon bayan Rasha - a matsayin "juyin mulki".

    Putin ya ce wasu ne ke iko da Ukraine daga waje, ba tare da ya ba da wata hujja ba.

  5. Rushewar Tarayyar Soviet fashi da makami ne ga Rasha - Putin

    Da yake ci gaba da jawabin da ake yaɗawa kai-tsaye yanzu haka, Shugaba Putin na Rasha ya ce an yi wa Rasha "fashi" sakamakon rushewar Tarayyar Soviet a 1991.

    Ba wannan ne karon farko da ya fara faɗin haka ba - ya taɓa siffanta rushewar tarayyar a matsayin "bala'in siyasa na yanki".

  6. Labarai da dumi-dumi, Rasha za ta ayyana yankunan Ukraine a matsayin masu zaman kansu

    Fadar Shugaban Ƙasar Rasha ta Kremlin ta ce Shugaba Vladmir Putin zai ayyana wasu yankuna biyu na Ukraine da suka ɓalle a matsayin masu zaman kansu.

    Sanarwar da fadar ta fitar ta ce Putin ya faɗa wa shugaban Faransa da na Jamus cewa zai saka hannu kan wani umarrni da zai ayyana Donetsk da Luhansk a matsayin masu cin gashin kan su - ba ƙarƙashin Ukraine ba.

  7. APC ta saka 26 ga Maris ranar babban taro na ƙasa

    Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta saka ranar 26 ga watan Maris don gudanar da babban taronta na ƙasa.

    Mai magana da yawun jam'iyyar na ƙasa, Salisu Na’inna Dambatta, ya faɗa BBC Hausa cewa za a gudanar da taron ne a Abuja.

    Jam'iyyar ta cimma matsayar ne jim kaɗan bayan ta sanar da fasa gudanar da shi ranar 26 ga Fabarairu.

    BBC Hausa ta fahimci cewa yanzu haka mambobin kwamatin riƙo na shugabancin APC ƙarƙashin Gwamna Mai Mala Buni suna ganawar sirri.

    Tun farko APC ta sanar da hukumar zaɓe ta INEC cewa za ta gudanar da tarukan shiyya kafin na ƙasa baki ɗaya.

  8. 'Yan majalisa a Mali sun amince wa sojoji su ci gaba da mulki shekara 5 nan gaba

    'Yan majalisa a Mali sun amince baki ɗayansu da wani shirin gwamnatin sojan ƙasar da ke son ci gaba da zama a mulki har tsawon shekara biyar nan gaba.

    Har yanzu ba a bayyana ranar da za a gudanar da zaɓe ba a ƙasar.

    A shekarar da ta gabata ya kamata a gudanar da zaɓen amma sai ba a yi ba, abin da ya sa ƙungiyar Ecowas ta sanya mata takunkumai.

    Yanzu Mali na bin hanyoyin shari'a don a ɗage mata takunkumin da ƙungiyar harkokin kuɗi ta Afirka ta Yamma, Uemoa, ta sanya mata yayin da take fama da bashi.

  9. Goodluck Jonathan zai koma Mali

    Wakilin Ecowas na musamman - ƙungiyar haɓaka tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma - tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan zai sake komawa Mali don ci gaba da warware rikicin siyasar ƙasar.

    Wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar a yau Litinin ta ce Jonathan zai jagoranci tawagar wakilai zuwa ƙasar ranar Alhamis kuma hakan ya biyo bayan zaman da aka yi ne game da jadawalin gudanar da zaɓe a ƙasar.

    Majalisar mulkin soja ta Mali ta ƙi ta ba da tabbacin gudanar da zaɓe kamar yadda ta yi alƙawari tun farko, inda ta yi tayin ci gaba da zama a mulki tsawon shekara biyar masu zuwa.

    Jonathan zai samu rakiyar shugaban ƙungiyar da kuma shugaban sashen siyasa.

  10. Sabuwar doka kan kafafen sada zumunta a Pakistan ta tanadi ɗaurin shekara 5 a gidan yari

    'Yan hamayya da masu raji na kafafaen watsa labarai a Pakistan sun yi kakkausar suka kan wata sabuwar doka da gwamnati ta sanar a karshen mako ba tare da wata tattaunawa ba a majalisar dokokin kasar.

    Dokar ta tanadi cewa za a iya ɗaure mai amfani da shafukan sada zumunta har shekara biyar bisa laifin ɓata suna.

    Kazalika dokar ta ba wa kowa dama - ba lallai sai mutumin da aka bata wa sunan ba - shigar da kara a kotu.

    Shugaban Pakistan ya sanya hannu kan dokar kwana daya bayan da majalisar zartarwar kasar ta amince da ita.

    Masu sukar sun ce an bullo da dokar ne da nufin tauye 'yancin fadin albarkacin baki, zargin da gwamnati ta musanta.

  11. Jahilci ne ya sa ake ganin Buhari na jan-ƙafa wajen amincewa da dokar zaɓe - Fadar shugaban ƙasa

    Fadar gwamnatin Najeriya ta ce "jahilci ne" ya sa wasu ke ganin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari yana jan-ƙafa wajen saka wa sabon ƙudirin dokar zaɓe hannu, wanda Majalisar Tarayya ta miƙa masa tun a watan Janairu.

    A kwanan nan ne wasu ƙungiyoyin farar hula suka dinga sukar shugaban saboda bai saka wa sabon ƙudirin dokar hannu ba a karo na biyu bayan Majalisar Tarayyar ta yi mata kwaskwarima tare da sake aika wa Buhari.

    Wata sanarwa da fadar ta wallafa a shafinta na Twitter ta ce shugaban ƙasa na da kwana 30 don yin nazari kan ƙudirin, kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya ba shi dama.

    "Sai dai a tausaya musu saboda jahiltar Kundin Tsarin Mulki da suka yi saboda shugaban ƙasa na da kwana 30 da zai iya saka mata hannu ko kuma akasin hakan bayan Majalisa ta miƙa masa dokar," in ji sanarwar.

    "A bayyane take cewa an miƙa wa shugaban ƙasa ƙudirin ranar 31 ga watan Janairun 2022, abin da ke nufin gwamnati za ta iya nazari cikin tsanaki har zuwa 1 ga watan Maris kamar yadda Kundin Tsarin Mulki ya tanada."

    Tun farko Buhari ya ƙi amincewa da sabuwar dokar yana mai cewa 'yan majalisar ba su ba wa jam'iyyu zaɓi ba wajen maganar zaɓen fitar da 'yan takara, inda suka ce zaɓen 'yar tinƙe kaɗai za a bi. Daga baya sun gyara sannan suka sake miƙa wa shugaban.

  12. Kotun duniya na sauraren bahasi kan cin zalin Musulmin Rohingya

    Kotun duniya za ta koma sauraren bahasin jama'a a kan zargin cewa gwamnatin Myanmar ta aikata laifin kisan kiyashi a kan tsirarun Musulmi 'yan Rohingya

    Sojojin da ke mulkia kasar sun kafe cewa Gambia, wadda ta shigar da karar ba ta da hurumin yin hakan.

    Sama da ƴan Rohingya 1,730, ne suka tsere daga Myanmar bayan kamen da sojoji suka shiga yi musu a 2017, inda hakan ya tilasta musu tsallaka iyaka, zaman gudun hijira a sansanonin da ke warwatse a Bangladesh.

    Haka kuma sojojin da suka kwace mulkia shekarar da ta wuce sun maye gurbin, tsohuwar jagorar gwamnatin kasar, Aung San Suu Kyi, mai lambar yabo ta zaman lafiya ta Nobel, a matsayin wakiliyarsu a zaman sauraren.

    Yanzu dai tana karkashin daurin talala a gidanta.

    Kungiyoyin kare hakkin dan-Adam na fatan, shari'ar za ta kawo sauki tare da yi wa Musulman 'yan Rohingya adalci.

  13. APC ta sake ɗage babban taronta na ƙasa

    Jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya ta sake ɗage ranar babban taronta na kasa bayan tsayar da ranar 26 ga watan Fabrairu tun da farko.

    Wannan na ƙunshe a cikin wata takarda da jam’iyyar ta aika wa hukumar INEC ɗauke da sa hannun shugabanta na riƙo gwamnan Yobe Mai Mala Buni.

    "Muna sanar da hukumar zaɓe cewa jam’iyyarmu ta yanke shawarar gudanar da zaben shiyoyi a ranar 26 ga watan Maris."

    Hakan na nufin an ɗage taron tsawon wata ɗaya

    Ba a san ranar gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa ba.

  14. Kungiyar ɗaliban Najeriya ta ba gwamnati da ASUU wa’adin maƙo ɗaya su janye yajin aiki

    Kungiyar ɗalibai ta NANS a Najeriya ta ba gwamnatin tarayya da ƙungiyar malaman jami’a ASUU wa’adin mako ɗaya su sasanta ko kuma su fuskanci bore ɗalibai a sassan ƙasar.

    Shugaban ƙungiyar ɗaliban na ƙasa Sunday Adedayo ne ya yi wannan gargadin a ranar Litinin a Sokoto, kamar yadda kafar talabijin ta Channels ta ruwaito.

    Ya ce ƙungiyarsu ta yanke shawarar cewa idan har gwamnatin tarayya da ASUU suka kasa sasatawa zuwa Juma’a, “ɗaliban za su haɗa gangami da ba gwamnati yaren da za ta fahimta.”

    “Mun tsayar da ranar 28 ga watan Fabrairu, dukkanin ɗaliban Najeriya da aka kora gida za su fito su rufe hanyoyin gwamnati da ofisoshin ma’aikatar limi da ta ƙwadago,” in ji shugaban ɗaliban

  15. An gano karyar da ta ɓace tsawon shekara 12

    An gano wata karya da ta yi batan dabo shekara 12 da suka gabataa Carlifonia da ke Amurka.

    An mika Zoey da aka yi wa gani na karshe kilomita 100 daga gidan da ta bace ga masu ita, wadanda suka cika da murna an sake tozali da ita.

    Likitocin dabbobi sun yi wa karyar wani gwajida ya tabbatar da cewa ta rabu da iyayen gijin nata, tun shekaru 10 da suka gabata, har ma daga bisani aka sanya sunanta cikin rijistar dabbobin da suka mutu, saboda tsawon lokacin da ka kwashe ba tare da jin duriyarta ba.

    A lokacin da aka samu Zoe dai ba ta da lafiya, a don haka tuni an kwantar da ita a asibiti, inda ta ke samun kulawa ta musamman.

  16. Kotu ta yi watsi da karar neman hana wa Atiku tsayawa takara

    Wata babbar kotun tarayya a Abuja ta yi watsi da ƙarar da wata ƙungiya mai da’awar kare haƙƙin ɗan Adam ta shigar tana ƙalubalantar cancantar takarar tsohon shugaban Najeriya Atiku Abubakar.

    Kungiyar mai suna Egalitarian Mission for Africa ce ta shigar da ƙarar tana ƙalubalantar cewa ba a Najeriya aka haifi Atiku ba, don haka ta ke neman kotu ta hana shi tsayawa takarar shugaban ƙasa.

    Sai dai alƙalin kotun mai shari’a Inyang Ekwo ya yi watsi da ƙarar inda ya ce ba hurumin ƙungiyar ba ne, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Najeriya NAN ya ruwaito.

    Watsi da ƙarar na zuwa bayan gwamnantin Adamawa ta shaida wa Kotun cewa Atiku cikakken ɗan jihar ne wanda aka zaɓa gwamna a 1999, kuma ya zama mataimakin shugaban ƙasa daga 1999 zuwa 2007.

  17. Tinubu ya faɗa wa matasa sai ya riga su zama shugaban ƙasa

    Tsohon gwamnan Legas kuma jagoran jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya faɗawa matasan ƙasar cewa za su yi shugabancin ƙasa amma sai bayan ya yi.

    Fitaccen ɗan siyasar na Najeriya ya faɗi haka ne a ziyarar da ya kai wa Alaafin na Oyo Lamidi Adeyemi, a ranar Lahadi.

    Tinubu ya buƙaci matasa su ba magabatansu dama.

    “Kun toshe wa magabatanku dama tun kafin ku zama shugaban ƙasa, idan kun zama shugaban ƙasa fa, za ku kore mu ne a gari?”

    “Sai kun tsufa za ku zama shugaban ƙasa, kuma sai na riga zama shugaban ƙasa,” in ji Tinubu.

    Matasa a Najeriya sun daɗe suna fafutikar ganin sun kai ga madafan iko, da samun muƙaman siyasa.

  18. An fara sauke sabuwar manhajar sada zumunta ta Donald Trump

    Kamfanin fasaha na Apple ya fara ba wasu kwastomominsa damar sauke manhajar sada zumunta da aka kera saboda Donald Trump da magoya bayansa.

    Manhajar da ake kira Truth Social tana tallata kanta a matsayin dandali ga waɗanda suke jin ana danne ra'ayoyinsua wasu shafukan na sada zumunta.

    An dakatar da tsohon shugaban daga amfani da Facebook da Twitter bayan mummunan harin da aka kai kan ginin Majalisar Dokokin Amurka a bara.

  19. Jirgin yaƙin Iran ya yi hatsari

    Wani jirgin yaƙin Iran ya yi hatsari inda ya kashe mutum uku a yankin arewa maso yammacin Tabriz.

    Rahotanni sun ce jirgin ya faɗi ne a wata makaranta, inda ya kashe matuka jirgin biyu da wani mutum guda da ke cikin mota a kusa da inda jirgin ya faɗi.

    Wani bidiyo da aka ɗaukak inda hatsarin ya faru ya nuna yadda jami’an kashe gobara ke ƙoƙarin kashe wuta a tarkacen jirgin.

  20. 'Mun daina yi wa maza kayan ɗaki - Matan Mayo Belwa

    Kungiyar 'yan mata da zawarawa ta Mayo Belwa a jihar Adamawa da ke Najeriya ta gindaya sharudda ga duk maza da ke son aure daga karamar hukumar.