Rufewa
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.
Awwal Ahmad Janyau
Masu bibiyarmu a wannan shafin a nan muka zo ƙarshen kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye, sai kuma gobe Lahadi idan Allah Ya kai mu za mu ci gaba da kawo muku wasu labaran.
Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Zamfara ta ceto mutum 24 waɗanda ƴan bindiga suka yi garkuwa da su.
A wata sanarwa da mai magana da yawun ƴan sandan jihar SP Mohammed Shehu ya fitar, tun da farko sun samu labarin harin da ƴan bindigan suka kai kan hanyar Gurgurawa a Ƙaramar Hukumar Bungudu ta Jihar Zamfara inda ƴan bindigar suka kwashi jama'a da dama.
Daga nan ne jam'ian ƴan sanda da ƴan bijilanti suka bazama cikin daji nemo waɗanda aka sace.
A cewar SP Mohammed, ko da ƴan bindigan suka hangi jami'an tsaro, sai suka soma harbi kan mai uwa da wabi wanda hakan ya ja aka ci gaba da musayar wuta tsakanin jami'an tsaron da ƴan bindigar.
Ya bayyana cewa bayan wutar da ƴan bindigar suka sha, sai suka gudu suka bar waɗanda suka yi garkuwa da su.
Mutum 14 waɗanda akasarinsu mata ne aka ceto a wurin da lamarin ya faru, sauran mutum goma kuma a yayin da suke gudu neman ɗauki suka samu suka koma ƙauye ba tare da wani rauni ba.
Haka kuma rundunar ta ce ta ƙwato babura bakwai waɗanda ƴan bindigan ke amfani da su yayin samamen da suka kai.
A Najeriya mahukunta sun ce mutum biyar ne suka rasa rayukansu lokacin da ƴan bindiga suka kai hari wasu yankuna na jihar Kebbi a arewa maso yammacin kasar da safiyar yau.
Bayanai sun ce yan bindigar sun kuma tare hanyar Koko zuwa Yawuri na tsawon sa'o'i.
Hon Yusuf Tanko Sununu wanda shi ne dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar yankin kuma ya yi man karin bayani.
Jami'an gwamnatin Taliban da ke kudancin birnin Kandahar na Afghanistan sun bayyana cewa mayaƙansu sun kashe wata mata bayan babur mai ƙafa ukun da take ciki ya ƙi tsayawa a wani shingen bincike.
An raunata wasu fasinjoji biyu a lokacin da dakarun ƙasar suka buɗe wuta. Wannan ne karo na uku da irin wannan lamarin yana faruwa a ƴan makonnin nan.
Ko a ranar Juma'a sai da dakarun Taliban ɗin suka kashe wani likitan haƙori kan zargin motarsa ta ƙi tsawaya a wani shingen bincike a Kabul babban birnin ƙasar.
Hakazalika ko a watan da ya gabata, sai da dakarun suka harbe wata matashiya da ke hanyar zuwa wurin biki ita da iyalanta cikin mota guda
Sama da kashi 50 cikin dari na mata da ke amfani da maniyyin da ake bayarwa kyauta wanda ake sa musu a mahaifa su haihu, mata ne da ba su da maza, wadanda suka kuduri aniyar renon 'ya'yansu har su girma su kadai ba tare da wani namiji ba, kamar yadda bayanai na baya-bayan nan daga daya daga cikin manya-manyan cibiyoyi na duniya masu adana maniyyi, Cryos International suka nuna.
Bayanan daga Cryos wadda ke samar da daskararren maniyyi da aka adana da kuma kwai (maniyyin mata) ga kasashe sama da 100 a duniya sun nuna karuwar yawan mata marassa maza da ke karbar maniyyin a cikin shekara bakwai da ta wuce, inda yawan ya tashi sama sosai zuwa kashi 54 cikin dari a 2020.
Shugaba Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa Ukraine a shirye take ta kare kanta daga Rasha ko da taimakon ƙawayenta ko babu.
Ya bayyana haka ne a wani taro kan tsaro a Munich. A yayin tarn, an fi tattauna batun Rasha n shirin mamaye Ukraine.
Mista Zelensky ya bayyana cewa Ukraine ta katange Turai daga sojojin Rasha tsawon shekara takwas sai dai ya ce ƙasarsa ba za ta kasance shinge ba har abada.
Ya buƙaci ƙasashen yamma da su tashi tsaye domin dakatar da abin da ya kira mamaya.
Ƴan sanda a Somalia sun bayyana cewa aƙalla mutum goma suka rasu a wani harin ƙunar baƙin wake a garin Beledweyne da ke yankin tsakiyar ƙasar.
Ƙungiyar da ke iƙirarin jihadi ta Al Shabaab ta ɗauki nauyin kai harin inda ta ce ta hari wani gidan abinci wanda ya yi suna sakamakon jami'ai da yan siyasar ƙasar na yawan zuwa wurin.
Mazauna kusa da wurin da lamarin ya faru sun bayyana cewa wurin ya lalace kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka rasu akwai ɗan takara da ke neman kujera a majalisa a zaɓen ƙasar da ke gudana.
A daidai lokacin da ake zabe a ƙasar, Al Shabaab na ci gaba da zafafa hare-hare inda suka tayar da bam sau biyu cikin makonni biyu da suka gabata.
Matsalar tsaro na ci gaba da addabar Najeriya musamman jihohin arewacin kasar inda masu garkuwa da mutane domin karbar kudin fansa da sauran kungiyoyi masu dauke da makamai ke ci gaba da kai hare-hare.
Hukumomin na cewa sun dukufa domin murkushe ‘yan bindigar inda ko a cikin wannan makon rundunar sojin sama ta ce ta kashe fiye da 40 daga cikinsu a Jihar Katsina, har da wani jagoransu Dogo Umaru.
Sai dai matsalar wadda aka dade ana fuskanta a jihohin arewa maso yammacin Najeriya ta fara watsuwa zuwa wasu jihohi kamar Filato da Bauchi inda akan samu rahotannin sace-sacen mutane domin karbar kudin fansa.
A filinmu na Gane Mani Hanya na wannan mako, Ishaq Khalid ya tattauna da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad Abdulkadir, Kauran Bauchi kan wannan batu da ma wasu batutuwan ciki harda aniyarsa ta tsayawa takarar shugabancin Najeriya.
Gwamnan ya fara ne da bayanin halin da jiharsa ke ciki ta fuskar tsaro.
Gamayyar ƴan adawa da ƙungiyoyin fararen hula a Chadi sun yi gargaɗi gwa gwamnatin sojin ƙasar game da dakarun Faransa da ke ficewa daga Mali.
A cikin wata sanarwa da suka fitar a rana Juma’a sun ce suna fatan gwamnatin ba za ta mayar da Chadi ba a matsayin madaddalar dakarun Barkhane ba, kamar yadda jaridar Alwihda ta ruwaito.
Wannan na zuwa bayan dakarun ƙasashen waje da ke yaƙi da masu ikirarin jihadi sun fara ficewa a Mali.
Dakarun Barkhane na da babban sansani a N'Djamena babbar birnin Chadi.
Ƴan bindiga sun tare hanyar Koko zuwa Yauri, kamar yadda ɗan majalisar tarayya da ke wakiltar yankin Hon Tanko Yusuf Sununu ya tabbatar wa BBC.
Rundunar sojin Mali ta ce an kashe sojojinta takwas sannan biyar sun ɓata bayan wani hari da 'yan tawaye suka kai a arewa maso gabashin kasar.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce, sojojin saman Mali sun kashe mayakakusan 60.
Rundunar ta ce sojojin na neman maboyar 'yan tawaye ne a lokacin da suka yi ta luguden wuta a yankin Arham.
Wannan na zuwa ne kwanaki biyu bayan da Faransa da ƙawayenta suka ce za su janye dakarunsu daga Mali, inda suka kwashe kusan shekara goma suna yakar masu da'awar jihadi.
Faransa ta ce gwamnatin sojan Mali na kawo mata cikas ga aikinta; gwamnatin mulkin sojan ta mayar da martani ta hanyar umurtar sojojin Faransa da su fice cikin gaggawa.
Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya sanar da yin marhabin da dakarun kasashen turai da ke ficewa daga kasar Mali.
Shugaban ya sanar da hakan ne a shafin sa na Twittera ranar juma’a, tare da cewa ya yanke wannan shawarar ne tun kafin daukar matakin ficewar dakarun Faransa daga Mali.
Shugaban ya ce manufar hakan shi ne tabbatar da tsaron iyakokin Nijar musamaman da Mali.
“Muna ganin idan dakarun Barkhane da Takuba suka fice, wannan yanki zai ƙara fuskantar barazanar ƴan ta’adda,” in ji Bazoum.
Sai dai matakin shugaban ya haifar da ce-ce-ku-ce tsakanin ƴan Nijar, kamar yadda za ku ji a rahoton Abdou Halilou.
Mutane tara suka mutu yayin da guguwar Eunice ta yiɓarna a arewacin Turai.
An ba da rahoton mutuwar mutane a ƙasashen Netherlands da Belgium da Birtaniya da kuma Ireland, yawancinsu sun mutu ne ta hanyar faɗowar bishiyu.
Guguwar da ke gudun kusan kilomita 200 a cikin sa'a da iska mai ƙarfi ta shafi Birtaniya zuwa Faransa da Denmark.
Masu inshora sun yi hasashen cewa guguwar ta haifar da hasarar kusan rabin dala biliyan a Biritaniya kaɗai.
Jami’an rundunar ‘yan sandan jihar Ogun sun kama wata mata mai suna Bola Agbedimu, mai shekaru 30, a ranar masoya, da ake zargin ta yi bushasha da kudaden jabu na naira.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa ya ce an kama matar ne da takardun naira 1,000 na jabu a kasuwar Kila da ke ƙaramar hukumar Odeda a jihar Ogun.
Jami’in ya ce sun kama ta ne bayan samun rahoton cewa tana kashe kuɗin jabu a kasuwar, kuma nan take jami’an ƴan sanda suka yi mata dirar mikiya.
Ƴan sandan sun ce sun samu kudi na jabu naira 24,000a cikin jakar matar.
Sanarwar ta ce, bayan kammala bincike za a hukunta matar.
Shekara hudu ne kenan ba labarin Leah Sharibu dalibar makarantar sakandaren Dapchi da ‘yan Boko Haram suka sace a watan Fabrairu.
Leah Sharibu na cikin dalibai mata sama da 100 da Boko Haram ta sace a ranar 19 ga watan Fabrairun 2018, bayan abkawa makarantarsu ta kwana.
Sai dai duk da an saki wasu daga cikinsu amma har yanzu babu labarin Leah wadda aka sace a lokacin tana ‘yar shekara 14.
Iyayenta har yanzu ba su cire ransu ba ga ƴarsu inda suke ci gaba da yin kira ga gwamnatin Najeriya ta kuɓutar da ita, kamar yadda suka bayyana a cikin wata sanarwa da suka fitar.
Satar ɗalibai da mutane domin kuɗin fansa ta zama ruwan dare a Najeriya, tun bayan satar daliban makarantar Chibok a jihar Borno da na Dapchi a jihar Yobe a arewa maso gabashi da kuma sace-sacen ɗalibai a makarantun jihohin arewa maso yammaci.
Kungiyar manoman masara ta Najeriya ta ce an samu gagarumin sauyi a yadda ake noman masara a kasar a karkashin shirin gwamnatin kasar na ba da rance don noman na masara.
Kungiyar ta ce sabanin yadda a baya manoma kan karbi rancen kayan noman amma su ki biya, a yanzu manoman da kansu suke kiran jami’an da za su karbi bashin da ake binsu bayan sun yi girbi.
Ku saurari rahoton Yusuf Ibrahim Yakasai kan yadda lamarin yake a jihar Gombe.
Shugaba Biden na Amurka ya ce tabbas shugaba Vladimir Putin ne ya ba da umarnin Rasha ta mamaye Ukraine, yana mai cewa gwamnatinsa ta samu bayanan sirrin da suka tabbatar da ahakan.
A wani jawabi da ya yi daga FadarWhite House, Biden ya ce har yanzu za a iya magance wannan matsala ta fuskar diflomasiyya.
Ana ganin wannan a matsayin kakkausan gargadin da Joe Biden ya yi kan aniyar Rasha a Ukraine.
Biden ya kuma ce baya haufin tabbas shugaba Putin ya gama yanke shawarar abin da zai yi.
Sai dai Rasha ta musanta zargin na kokarin mamaye Ukraine.