Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Tarayyar Turai za ta bunkasa Afirka da dala biliyan 170

Wannan shafi na kawo muku abubuwan da ke faruwa a sassan duniya kai-tsaye, musamman a Najeriya da Nijar maƙotansu.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. 'Yan bindiga sun kashe 'yan sandan Najeriya uku a Enugu

    An shiga rudani da fargaba a cikin garin Enugu bayan da wasu ‘yan bindiga suka kasha ‘yan-sanda uku a wani wurin binciken ababan hawa, Alhamis din nan da rana.

    Lamarin ya faru ne kamar yadda rahotanni suka ce da kusan karfe 1:20 na rana, a kusa da rukunin gidaje na

    Ulumalinda a wajen karamar hukumar Enugu ta kudu.

    An ce ‘yan bindigar sun sace wata mata a yayin farmakin, wanda aka ce sun kai minti talatin suna cin karensu ba babbaka.

    Haka kuma sun ‘yan bindigar sun yi wa wata mata mai sana’ar karba da bayar da kudi (POS) fashi bayan da harsashi ya same ta.

    Kakakin ‘yan-sanda na jihar, Daniel Ndukwe, ya tabbatar wa da maneman labarai lamari, amma bai yi Karin bayani ba.

  2. An dawo da masarauta bayan shekara 117 a Sudan ta Kudu

    An mayar da daya daga cikin masarautun Sudan mafiya dadewa, bayan sama da shekara dari daya da mutuwar sarkinta na karshe.

    Sojojin Birtaniya ne da ke sintiri a lokacin suka kashe Sarki Gbudue a shekarar 1905, to amma bayan wadannan shekaru a jiya Laraba aka nada tattaba kunnensa domin maye gurbinsa a matsayin basaraken al'ummar Azande.

    Daruruwan mutane ne suka yi dafifi domin kallon nadin Wilson Peni Rikito Gbudue, a fadar sarkin da ke garin Yambiyo a jihar Western Equatoria.

    Za a shafe duk tsawon wannan mako ana bikin mayar da sarautar da kuma nadin.

    Wani kanin sarkin ya musanta maganar da wasu ke yi cewa al'ummar Azanden sun nemi a dawo da sarautar ne domin su ci moriyar siyasa a jihar tasu.

    Ya ce sun yi hakan ne kawai domin ciyar da al'adarsu gaba da kuma kare tarihi da gadonsu.

  3. Dole ne wadanda suka shigo da gurbataccen mai su yi bayani - Buhari

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya ce dole ne wadanda suka shigar da gurbataccen man fetur din da aka rinka sayar wa a kasar a kwanakin nan su yi bayani.

    Shugaban ya bayar da umarni ga dukkanin hukumomin da abin ya shafada su dauki duk matakin da ya dace da dokar kasar, domin tabbatar da kare jama’a masu amfani da kayayyaki daga masu algus da zalunci.

    Kakakin shugaban, Mallam Garba Shehu, ne ya bayyana wannan a wata sanarwa da ya fitar Alhamis din nan.

    A sanarwar shugaban ya ce kare muradun jama’a abu ne da gwamnatinsa ta ba fifiko, kuma a shirye yake ya dauki dukkanin matakan da suka wajaba ya kare mutane daga gurbatattun abubuwan da za su cutar da su.

    A kwanakin nan dai bayan da aka shiga matsalar karancin man fetur a sassan Najeriya, masu ababen hawa da dama sun sayi mai a wasu gidajen mai na kasar, wanda kuma ta bayyana daga bisani gurbatacce ne, har ta kai ga ababan hawa sun rika samun matsala, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce a kasar.

  4. Wadanda ake zargi da kisan Hanifa sun samu lauya

    Babban lauyan gwamnati kuma Kwamishinan shari’a na jihar Kano, Barrister Musa Abdullahi Lawan,ya bayyana cewa hukumar bayar da tallafin shari’a ta Najeriya (Legal Aid Council of Nigeria) ta nuna aniyarta ta samar da lauyoyin da za su wakilci mutanen da ake zargi da sacewa da kuma kashe yarinyar nan Hanifa Abubakar.

    Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa, kwamishinan ya fada mata a ranar Alhamis din nan cewa, matakin ya biyo bayan umarnin da mai shari’a Usman Na’abba na babbar kotun Kano ya yi ne a ranar 5 ga watan nan na Fabrairu cewa gwamnatin jihar ta sama wa babban wanda ake zargin da sauran mutum biyu lauya, kamar yadda suka bukaci lauya ya tsaya musu a shari’ar, saboda ba su da shi.

    Babban lauyan na gwamnatin Kano ya ce, a bisa doka duk mutumin da yake fuskantar shari’ar zargin kisan kai, ana bukatar ya samu lauya mai wakiltarsa, idan kuma ba shi da lauyan ba kuma shi da halin dauka, tsarin mulki Najeriya ya sa dole jiha ta sama masa.

    Atoni Janar din ya kara bayani da cewa hukumar bayar da tallafin shari’ar ta Najeriya hukuma ce ta tarayya wadda aka kafa ta domin taimaka wa duk wani dan kasar da ba shi da lauya a shari’ar da ake masa mai hukuncin kisa, kyauta.

    An dakatar da shari’ar Abdulmalik Tanko da mutum biyu da ake zargi da sacewa da kuma kashe Hanifa saboda ba su da lauyan da zai kare su.

    Daman alkalin da ke shari’ar ya dage zama har zuwa ranar 14 ga watan nan na Fabrairu, bayan da ya gabatar da umarnin a sama musu lauya.

  5. An dakatar da malaman da suka shiga yajin aiki a Zimbabwe ba albashi

    Ma'aikatar ilimi ta Zimbabwe ta dakatar ta malaman makarantar da suka yi yajin aiki, suka ki zuwa makaranta a ranar Litinin da aka koma karatu.

    Malamai da yawa na makarantun gwamnati na yajin aiki saboda karancin albashi.

    Ma'aikatar ta ce ta dakatar da malaman ne mai tsaye wata uku ba tare da albashi ba, yayin da kuma za a ci gaba da gudanar da bincike kan zargin rashin da'a da suka nuna.

    An koma makarantu ne a kasar ranar Litinin bayan wata daya da aka yi na hutu saboda kullen yaki da korona.

    Yawancin malaman makaranta a Zimbabbwe ana biyansu kasa da dala 200 a wata a bisa canjin gwamnati, kuma kasa da dala 100 a kasuwar bayan-fage, wadda yawanci da farashinta ake sayar da kaya da biyan ayyuka.

    Kungiyar malaman na neman a rinka biyansu mafi karancin albashi na dala 540.

    A ranar Talata gwamnati ta sanar da arin albashin ma'aikatanta da kashi 20 cikin dari, wanda ya hada da biyansu dala 100 a wata a kudin kasar waje.

  6. Faransa za ta samar da tarin tashoshin makamashin nukiliya

    Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya sanar da shirinsa na zuba dinbin jari a fannin makamashin nukiliya da makamashi maras gurbata muhalli, kamar mai amfani da hasken rana da Iska.

    Mista Macron ya kuduri hakan ne domin mayar da kasar tasa wadda ba ta fitar da hayaki mai haifar da dumamar yanayi nan da shekara ta 2050.

    Shugaban yana son gina tashoshin makamashin nukiliya akalla shida, inda ake sa ran ta farko ta fara aiki zuwa shekara ta 2035.

    Faransa na samun kashi 70 cikin dari na wutar lantarkinta daga makamashin nukiliya.

    Ana daukar makamashin nukiliya a matsayin wanda ba ya fitar da hayaki mai gurbata muhalli sosai, amma kuma kwararru a bangaren muhalli na cewa yana da tsada sosai.

    Sannan yana sa a karkatar da hankali daga zuba kudi wajen samar da makamashi maras gurbata muhalli, kana kuma yana haifar da matsalar sharar nukiliya mai hadarin gaske.

  7. Tarayyar Turai za ta bunkasa Afirka da dala biliyan 170

    Kungiyar Tarayyar Turai ta yi alkawarin yin wani shiri na zuba jari har nadala biliyan 170 domin kasashen Afirka.

    Shugabar hukumar Turan, Ursula von der Leyen ce ta gaya wa hukumomin Senegal a yayin da ta kai ziyara babban birnin kasar Dakar.

    Ta ce wannan shi ne wani shiri na farko na nahiya a karkashin sabon shirin habaka harkokin jin dadin jama’a na gwamnati da na ‘yan kasuwa a kasashe masu tasowa, mai suna Global Gateway.

    Ana yi wa wannan manufa ta kungiyar ta Tarayyar Turai kallo a matsayin wata kishiya ga ayyukan da China ke yi a kasashe masu tasowa, mai suna Belt and Road Initiative.

  8. Pa Sorie: Tunawa da rayuwar sojan Saliyo da ya yaƙi Hitler

    Samuel Sorie Sesay, daya daga cikin sojojin da suka kusa shudewa daga doron kasa na cikin wadanda suka yi Yakin Duniya na Biyu tare da sojojin Birtaniya, ya mutu a watan jiya a Saliyo yana da shekara 101.

    Yayin da ake shirin binne shi ranar Juma'a, Umaru Fofana ya yi waiwaye kan rayuwarsa.

    Yana da iya tunawa da abubuwan da suka faru a shekarun baya, sai dai a ganinsa an manta da shi.

    Yayin da yake bikin cika shekara 100 da haihuwa a shekarar 2020 tare da iyalansa masu tarin yawa, Pa Sorie - kamar yadda aka fi saninsa - na da batutuwan da yake son yin magana akansu masu yawa.

  9. Aƙalla mutum shida suka rasu a harin ƙunar baƙin waken Somalia

    Ma'aikatan agajin gaggawa a Somalia sun ce akalla mutane shida ne suka mutu wasu da dama kuma suka jikkata a wani harin kunar bakin wake da aka kai a Mogadishu babban birnin kasar.

    Kungiyar masu ikirarin jihadi ta Al Shabaab ta ce ta kai hari kan wata karamar motar bas cike da wakilan da ke da ruwa da tsaki wajen zaben 'yan majalisar.

    Akasarin wadanda suka mutu matafiya ne.

    Ana samun yawaitar hare-hare a 'yan makonnin nan yayin da 'yan siyasa ke kokawa kan tsarin da aka jinkirtar na zaben majalisar dokoki da shugaban kasa.

    Masu sharhi kan harkokin tsaro sun ce mafi yawan tashe-tashen hankula na faruwa ne daga bangarorin siyasa masu gaba da juna

  10. Rikicin Ukraine: Firaminista Boris Johnson ya isa Poland don tattaunawa

    Firaminista Boris Johnson na Birtaniya ya isa birnin Warsaw na Poland kuma an ɗauke shi a mota zuwa fadar gwamnatin ƙasar.

    Mista Johnson zai tattauna da ɗan uwansa na Poland Mateusz Morawiecki game da fargabar da ake da ita ta Rasha da ke yunƙurin afka wa maƙociyarta Ukraine.

    Ana tsammanin zai yi taron manema labarai bayan kammala tattaunawar sannan ya wuce zuwa sansanin sojojin ƙungiyar tsaro ta Nato da kuma dakarun Birtaniyar.

    Tun da farko firaministan ya ce idan har Rasha ta afka wa Ukraine "zai zama mummunan bala'i".

  11. Yarima Charles mai jiran gadon Sarautar Birtaniya ya kamu da korona

    Yarima Charles mai jiran gadon Masarautar Birtaniya ya kamu da cutar korona har ma ya killace kan sa, a cewar fadarsa ta Clearance House cikin wata sanarwa a Twitter.

    An sanar da labarin kamuwar tasa ne jim kaɗan kafin ya fita zuwa Winchester don halartar wani biki.

    A ranar Laraba yariman da matarsa Camilla sun gaisa da mutane a wurin wata liyafa a gidan ajiye kayan tarihi na British Museum.

    A ranar Alhamis gwaji ya nuna Camilla ba ta ɗauke da cutar. Wannan ne karo na biyu da Yarima Charles ya kamu da cutar.

    A watan Maris na 2020 ne yariman mai shekara 73 ya fara harbuwa da cutar.

  12. Gurɓataccen fetur: Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi a dakatar da kamfanonin da ke da laifi

    Majalisar Wakilan Najeriya ta nemi gwamnatin ƙasar ta dakatar da kamfanonin mai na 'yan kasuwa da suka shigar da gurɓataccen man fetur ƙasar.

    Ƙudirin da majalisar ta cimma a yau Alhamis wani ɓangare ne na binciken da wakilan ke yi game da asalin man, wanda ya lalata ababen hawan mutane da dama a faɗin Najeriya tun daga ƙarshen watan Janairu.

    Tun farko shugaban kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPC, Mele Kyari, ya bayyana MRS da Oando da Duke Oil da Emadeb a matsayin kamfanonin da suka yi dakon man zuwa ƙasar daga Belgium.

    NNPC ya ce yana ci gaba da bincike da kuma tuntuɓa don ɗaukar matakin da ya dace.

    Ita ma hukumar kula da harkokin mai Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority (NMDPRA) ta ce ta gano matsalar kuma tuni ta dakatar da fitar da gurɓataccen man, wanda hakan ya haddasa dogayen layi a gidajen sayar da shi.

  13. Jirgin Houthi ya raunata mutum huɗu a Saudiyya bayan harbo shi

    Rundunar haɗin gwiwa ƙarƙashin jagorancin Saudiyya da ke yaƙar 'yan tawayen Houthi a Yemen ta ce ɓaraguzan wani jirgi maras matuƙi da aka harba kan filin jirgi a yammacin Saudiyyar sun raunata mutum huɗu.

    Rahoton kafar yaɗa labaran gwamnatin ƙasar ya ce mutanen da aka jikkata ma'aikatan filin jirgin ne da kuma matafiya.

    Ta ce ɓaraguzan jirgin ne suka jikkata mutanen bayan sun gano tare da kakkaɓo shi. Mayaƙan na Houthi sun sha aika jirage marasa matuƙi zuwa Saudiyya a baya.

    A kwanan nan, sun kai wa Daular Larabawa (UAE) hari, wadda ke gaba-gaba a tawagar haɗin gwiwar.

  14. Shugaban Koriya Ta Kudu na fargabar barkewar tashin hankali tsakanin kasarsa da Koriya ta Arewa

    Shugaba Moon Jae-in na Koriya ta Kudu ya yi gargadin tashin hankali zai sake barkewa a yankin kamar wanda aka gani shekaru 5 da suka gabata, sakamakon gwajin makamai masu linzami babu kakkautawa da Koriya ta Arewa ke yi dan tsakanin nan.

    A wata hira da kamfanonin dillancin labarai 8, Mista Moon, ya ce tattaunawar sulhu ce kadai hanyar da za ta dakatar da hakan, ko dai tsakaninsa da shugaban Koriya ta Arewa Kim Jong-un, ko tsakanin Kim da Shugaba Biden na Amurka.

    Mr Moon da k tunkarar zabe a wata mai zuwa, ya dora alhakin abin da ke faruwa kan rashin cimma matsaya a ganawar tsohon shugaban Amirka Donald Trump da Kim a shekarar 2018.

  15. NNPC ya ɗora wa kamfani huɗu alhakin shiga da gurɓataccen mai Najeriya

    Kamfanin mai na gwamnatin Najeriya NNPC ya bayyana sunan kamfanonin mai na 'yan kasuwa da yake zargi da shiga da gurɓataccen mai ƙasar, wanda ya haddasa lalacewar ababen hawa.

    Shugaban NNPC Mele Kyari ya ce kamfanonin MRS da Oando da Duke Oil da Emadeb ne suka yi dakon man zuwa Najeriya yayin da yake yi wa manema labarai jawabi ranar Laraba.

    Ya ce NNPC ya samu rahoton man da ke ɗauke da sinadarin methanol da yawa a cikinsa ranar 20 ga watan Janairun 2022, wanda aka ɗauko daga ƙasar Belgium.

    Ya ƙara da cewa duk da ma'aikatansu na hukumar Nigerian Midstream and Downstream Regulatory Authority (NMDPRA) sun tantance jiragen da suka yo dakon man kuma suka ba su damar wucewa, aikin tantancewar bai tanadi duba yawan sanadarin methanol ba.

    Tun a watan Janairu ne masu ababen hawa suka fara fuskantar dogayen layi a gidajen mai na faɗin ƙasar, abin da NNPC na faruwa sakanakon dakatar da sayar da gurɓataccen man da suka yi.

    Shugaban hukumar ta NMDPRA, Faruk Ahmed, ya faɗa wa BBC Hausa yadda aka yi man ya shiga Najeriya da matakin da suka ɗauka.

    Latsa hoton ƙasa ku kalli bidiyon:

  16. 'Yan Ghana za su fara amfani da fasfo na latironi don zuwa ƙasashen duniya

    'Yan Ghana za su fara amfani da katin shaidar ɗan ƙasa a matsayin fasfon tafiye-tafiye, inda za su iya sauka a filayen jiragin sama 44,000 na fadin duniya.

    Yanzu Ghana ta kasance daga cikin kasashen duniya kalilan da ke amfani da katin shaidar dan kasa a matsayin fasfo.

    Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta duniya ICAO ta amince da katin shaidar, wanda akafi sani da Ghana Card, ya yi aiki a matsayin fasfo na latironi ko kuma E- Passport.

    Latsa hoton ƙasa ku saurari rahoton Muhammad Fahd Adam daga Ghana:

  17. Rabin al'ummar duniya na rayuwa ƙarƙashin mulkin danniya - Rahoto

    Wani rahoton shekara-shekara da ƙwararru a fannin tattalin arziki ke fitarwa ya ce kusan rabin al'ummar duniya ne kadai ke rayuwa karkashin mulkin dimokuradiyya.

    Sai dai sun ɗora alhakin hakan ga annobar korona, wadda ta sanya aka samu mafi kankantar adadi tun da suka fara binciken a shekarar 2006.

    Ɓarkewar annobar ta kara bai wa shugabannin da ke son mulki ci gaba da zama a kan mulki.

    Binciken ya nuna cewa fiye da kashi 1 cikin 3 na al'ummar duniya na karkashin mulkin danniya, yawancinsu a China.

    Kasashen Norway da New Zealand da Finland na sahun gaba a ingantacciyar dimokuradiyya, yayin da Koriya ta Arewa da Myanmar da Afghanistan ke sahun baya.

  18. Hisbah ta fasa kwalabar giya kusan miliyan huɗu a Kano

    Hukumar Hisbah mai tabbatar da dokokin Shari'ar Musulunci a Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta fasa kwalabar barasa ko giya kusan miliyan huɗu.

    Kwamandan Hisba Harun Sani Ibn Sina, shi ne ya jagoranci aikin fasa kwalaben miliyan 3,800,000 a Ƙaramar Hukumar Danbatta ranar Laraba.

    Hukumar ta ce ta shafe tsawon lokaci tana tara su bayan ta ƙwace daga hannun 'yan kasuwar da ke shigar da giya jihar kafin ta fasa su.

    A ƙarƙashin dokokin Kano, sayar da giya da sauran kayan maye haramun ne saboda sun saɓa wa kundin Shari'ar Musulunci da jihar ke aiki da shi.

  19. 'Yan gudun hijirar Borno sun koma gidaje 803 da Gwamna Zulum ya sake gina musu

    Gwamna Babagana Umara Zulum na Jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ya ƙaddamar da sabbin rukunin gidaje da gwamnatinsa ta gina wa 'yan gudun hijira a Ƙaramar Hukumar Konduga ranar Laraba.

    A cewar gwamnatin jihar, an sake gina gida 803 ne bayan shekara bakwai suna gudun hijira sakamakon hare-haren mayaƙan ƙungiyar Boko Haram.

    Wata sanarwa da Isa Gusau, kakakin gwamnatin Borno, ya fitar ta ce Gwamna Zulum ya ba da umarnin a bai wa mutum 500 naira 100,000 kowannensu waɗanda gidajensu ba sa cikin waɗanda aka sake ginawa, inda za a raba musu miliyan 50 jumilla.

    Kazalika, gwamnan ya ba da umarnin raba wa maza 240 'yan gudun hijirar da suka koma garinsu naira N200,000 kowannensu. Sannan kowace mace daga cikin 379 za ta samu N10,000 da kuma atamfa.

    Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya yaba wa hukumar cigaban yankin arewa maso gabas ta North-East Development Commission (NEDC) bisa taimakon kayan abinci da take ba wa 'yan gudun hijirar.

  20. Najeriya: Tarar miliyan 500 ga ma'aikacin da ya saci kuɗi don neman lafiya a ƙasar waje

    Majalisar Wakilan Najeriya ta yi wa wani ƙudirin doka karatu na biyu, wanda zai tanadi hukunci ga duk jami’in gwamnatin da ya kwashi dukiyar al'umma don zuwa ƙasashen waje a duba lafiyarsa.

    Wani ɗan majalisa ne ya gabatar da ƙudurin gyara Dokar Harkokin Kula da Lafiya ta Ƙasa ta 2014, ta yadda za a ci tarar naira miliyan 500 ga duk jami'in gwamnatin da ya saɓa ta.

    Honorabul Abubakar Yunus, ɗan majalisar ne, kuma ya yi wa Zahraddeen Lawan ƙarin bayani: