Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'Yan sanda sun kama mutum 40 kan yajin aikin 'yan A-Daidaita-Sahu a Kano

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Imam Saleh

  1. Korona ta kashe ƙarin mutum shida a Najeriya

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce cutar korona ta kashe ƙarin mutum shida ranar Lahadi a ƙasar.

    Haka nan, hukumar ta ce an samu ƙarin mutum 537 da suka kamu da cutar.

    Sabbin kamuwar sun fito ne daga jiha takwas, ciki har da Abuja babban birnin Najeriyar. Jihohin su ne:

    • Rivers (313)
    • Lagos (178)
    • Abuja (19)
    • Kaduna (11)
    • Gombe (6)
    • Ogun (6)
    • Ekiti (3)
    • Abia (1)

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 248,312 ne aka tabbatar sun harbu da cutar a Najeriya, yayin da 3,077 suka rasa rayukansu.

  2. Assalamu Alaikum

    Barkanmu da sake haɗuwa a shafin rahotanni kai-tsaye, inda za mu kawo abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi na Litinin - mande tushen aiki.