'Yan sanda sun kama mutum 40 kan yajin aikin 'yan A-Daidaita-Sahu a Kano

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Imam Saleh

  1. Rufewa

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist

    To jama'a a nan za mu dasa aya, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu za mu dawo don ci gaba.

    Za ku iya komawa ƙasa don samun labaran da muka wallafa a wannan rana.

    A madadin abokin aikina Umar Mika'il, Imam Saleh ke cewa mu kwana lafiya daga nan sashen Hausa na BBC.

  2. Yawan hayaƙi mai gurɓata muhallin da ake fitarwa a duniya ya ƙaru

    Hayaƙi

    Asalin hoton, AFP

    Masu nazari a Amurka sun ce alkaluma sun nuna hayaki mai gurbata muhallin da ake fitarwa ya karu da fiye da kashi shida a shekarar da ta gabata idan aka kwatanta da 2020.

    Rahoton na wata kungiya mai zaman kanta, Rhodium Group ya alakanta karuwar ga yawan amfani da lantarkin da ake samarwa daga makamashin kwal da kuma karuwar motoci kan tituna bayan shekara guda da annobar korona.

    Karuwar ta kuma nuna cewa Amurka ta kara nisanta daga burin rage gurbataccen hayakin da gwamnatin Biden ta yi alkawarin cimma.

  3. 'Yan sanda sun kama mutum 40 kan yajin aikin 'yan A-Daidaita-Sahu a Kano

    Bayanan sauti'Yan sanda sun kama mutum 40 kan yajin aikin 'yan A-Daidaita-Sahu a Kano

    Latsa hoton da ke sama don sauraren karin bayanin da SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya yi wa Khalifa Shehu Dokaji:

    Rundunar ‘yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta ce ta kama kimanin mutum 40 bisa zargin afka wa wasu masu sana'ar babur mai kafa uku, saboda kin shiga yajin aikin da suke yi, tare da yi wa masu tafiya a kafa kwace.

    Tun dai da safiyar yau Litinin aka girke jami’an tsaro na ‘yan sanda da na rundunar tsaro ta civil Defense wasu daga cikin manyan titunan Kano, don jiran ko ta kwana na yiwuwar samun rikici a lokacin da masu babur mai kafa uku a jihar suka fara yajin aiki.

    A cewar SP Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Kano, mutanen da suka kama suna dauke da makamai inda suke tare hanya suna yi wa mutane kwace da tilasta wa masu kananan motoci daukar kaya sauke mutanen da suka dauko don rage musu hanya.

  4. Mali ta fusata ta yi wa jakadunta na kasashen ECOWAS kiranye bayan ƙaƙaba mata takunkumin ƙahon zuƙa

    Asibiti Goita

    Asalin hoton, AFP

    Gwamnatin Mali ta ce ta yi wa jakadunta da ke kasashen Afirka ta Yamma kiranye bayan da kungiyar ECOWAS ta kakaba mata takunkumin karya tattalin arzikinta.

    Wakilin BBC ya ce wani mai magana da yawun gwamnatin Malin ya bayyana takunkuman a matsayin wadanda suka saba doka kuma ba a yi su bisa ka'ida ba.

    Ya kuma zargi ECOWAS da kasancewa a aljihun wasu kasashe da ke wajen yankin. ECOWAS ta dauki matakan ne bayan da sojojin da ke mulki a Mali suka ki martaba matsayar da suka dauka da farko ta gudanar da zabe a watan gobe tare da bayyana kudirinsu na ci gaba da rike shugabanci na tsawon wasu shekaru.

    Tuni ECOWAS ta dakatar da Mali tare da kakaba wa wasu jami'anta takunkumai.

  5. Mayaƙan Tigray sun zargi dakarun Eritiriya da kai musu farmaki

    Mayaƙan TPLF

    Asalin hoton, afp

    Mayakan Tigray sun zargi sojoji daga Eritrea mai makwabtaka da Ethiopia da kaddamar da hare-hare a yankin da ke arewacin kasar.

    Mai magana da yawun kungiyar TPLF ya ce an kai hare-haren a wurare biyu kusa da Sheraro, wani gari da ke kan iyaka.

    Zai yi wahala a iya tantance sahihancin ikirarin na mayakan saboda an katse layukan sadarwa.

    Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta dakatar da ayyukan agaji a wani yanki da ke arewa maso yammacin Tigray inda aka ba da rahoton fiye da mutum 50 da suka rasa matsugunansu sun mutu sanadin wani hari ta sama da gwamnatin ta kai.

  6. Bidiyon yadda yajin aikin 'yan A-Daidaita-Sahu ya tilasta wa Kanawa taka sayyada

    Bayanan bidiyo, Bidiyon yadda yajin aikin 'yan A-Daidaita-Sahu ya tilasta wa Kanawa taka sayyada

    Latsa hoton da ke sama domin kallon yadda mazauna birnin Kano da ke arewacin Najeriya suka rika taka sayyada sakamakon yajin aikin matuka A-Daidaita-Sahu.

  7. China ta umarci mutum miliyan biyu su zauna a gida lokacin bikin sabuwar shekara

    China

    Asalin hoton, Getty Images

    Mahukunta a Beijing sun buƙaci jama'a fiye da miliyan biyu da su zauna a gidajensu yayin hutun sabuwar shekarar China ta Lunar domin takaita bazuwar annobar korona.

    Matakin na zuwa ne a rana ta biyu ta gwaji a Tianjin da ke makwabtaka da birnin inda a nan aka gano masu dauke da sabon nau'in korona na Omicron.

    An sanar da al'ummar Tianjin cewa a yanzu suna bukatar izini kafin su fita daga birnin.

    A cewar wakilin BBC, wannan ne karon farko da a hukumance China take fuskantar kalubalen yaki da ɓarkewar nau'in Omicron na korona.

    Da alama mahukunta a China sun damu matuka cewa tafiye-tafiye a sabuwar shekarar na iya haifar da yaduwar cutar tare da zama barazana ga gasar Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijng zai karbi bakunci cikin watan Fabarairu.

  8. An ɗage haramcin amfani da babura masu ƙafa biyu a arewaci da yammacin Yobe

    Masu babura masu ƙafa biyu a jihar Yobe

    Asalin hoton, OTHERS

    Gwamnatin jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya ta sanar da ɗage haramcin amfani da babura masu ƙafa biyu a arewaci da yammacin Yobe.

    Wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun mai ba wa gwamnan jihar shawara kan harkokin tsaro Janar Ɗahiru Abdussalam, ta ce ƙananan hukumomin da aka ɗage haramcin sun haɗar da Fika, da Fune, da Nangere, da Potiskum, da Bade, da Machina, da Nguru, da Jakusko, da Karasuwa da kuma Yusufari.

    Sai dai duk da wannan mataki gwamnatin jihar ta sanya wasu sharuɗa ga masu amfani da baburan da suka haɗar da amfani da su kawai daga ƙarfe 6 na safe zuwa 6 na yamma, sannan ban da goyo.

    An kuma ba su umarnin yin rijistar baburan na su kana za su yi zirga-zirga ne a iya ƙananan hukumomin da suke ban da tsallakawa wata ƙaramar hukumar.

  9. Jami'an Rasha da Amurka sun tattauna gaba da gaba a kan Ukraine

    Amurka da Rasha

    Asalin hoton, Getty Images

    Jami'an Diflomasiyya daga Amurka da Rasha na ganawa a birnin Geneva domin fara tattaunawar farko don warware taƙaddamar da ake yi a Ukraine.

    Ofishin jakadancin Rasha cikin wani sako a shafin Twitter ya ce tattaunawar za ta zama "mai ma'ana".

    Wakilin BBC ya ce wannan ne karon farko da jami'an diflomasiyyar Rasha da Amurka suka gana gaba da gaba domin tattauna takaddamar da ake a Ukraine da kuma bukatar Rasha ta ganin ƙungiyar tsaro ta NATO ta janye daga gabashin Turai.

    Mataimakiyar Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Wendy Sherman, ta ce Amurka za ta saurari bukatun Rasha sannan ita ma ta bayyana nata.

    Rasha ta sha kiran a kawo karshen fadada aikin kungiyar tsaro ta NATO amma da take magana a Brussels, mataimakiyar firaministan Ukraine ta yi fatali da bukatar, inda ta yi kira ga Rashar da ta janye dubban sojojin da ta girke kusa da iyakarta.

  10. Jami'ar Yusuf Maitama Sule ta soke jarrabawa saboda yajin aikin 'yan A-Daidaita-Sahu

    Kano

    Asalin hoton, YMSU

    Jami'ar Yusuf Maitama Sule da ke birnin Kano ta soke jarrabawar da ta shirya farawa a yau Litinin sakamakon yajin aikin direbobin babur mai ƙafa uku a jihar.

    Jami'ar ta sanar da matakin ne cikin wata sanarwa da Dr. Yau Datti ya sanya wa hannu a ranar Lahadi, inda ta ce an soke wadda za a yi daga ƙarfe 8 zuwa 11 na safe.

    "Kwamatin jarrabawar zai tattauna da shugaban jami'ar don tsayar da lokacin da za a yi sauran jarrabawar," in ji sanarwar.

    'Yan ƙungiyar masu baburan da aka sani da A-Daidaita-Sahu a Kano sun fara yajin aikin na sati ɗaya daga Litinin sakamakon abin da suka kira "cin mutuncin da suke fuskanta wajen karɓar haraji daga gwamnatin Kano".

  11. Afcon 2021: Senegal 0-0 Zimbabwe

    AFCON

    Asalin hoton, CAF

    An tafi hutun rabin lokaci a wasa tsakanin Senegal da Zimbabwe babu ci a gasar Kofin Ƙasashen Afirka da ke gudana a Kamaru.

    Tagawar Senegal ta fi matsawa, sai dai ba a kai hare-hare masu yawa ba a wasan da ake bugawa a filin wasa na Omnisports da ke birnin Bafoussam.

    Duk wadda ta yi nasara a wasan za ta ɗare saman teburin Rukunin B kafin wasa tsakanin Guinea da Malawi da ƙarfe 5:00 agogon Najeriya.

  12. 'Yan bindiga sun harbe mutum ɗaya a Jihar Enugu

    Enugu

    Asalin hoton, Other

    Wasu 'yan bindiga sun harbe mutum ɗaya a Enugu babban birnin Jihar Enugu da ke kudancin Najeriya a safiyar yau Litinin.

    Mutanen ɗauke da makamai sun fara harbe-harbe tare da cinna wa wasu gidaje wuta, har suka kashe wani jami'n tsaro na sa-kai.

    Ya zuwa yanzu jami'an tsaro sun isa yankin Greece yayin da aka tura su yankuna daban-daban na birnin.

    Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan zumunta ya nuna yadda mutane ke gudun tsira da rayukansu.

    An zargi ƙungiyar 'yan aware ta Ipob da kai harin yayin da suke ƙoƙarin tabbatar da dokar hana fita ta duk Litiin da suka saka, sai dai ƙungiyar ta musanta zargin tana mai cewa ta soke dokar da ta kafa.

    Lamarin ya tilasta wa mazauna Enugu rufe shaguna da wuraren harkokinsu don tsira da rayukansu.

  13. Za a rantsar da Shugaba Ortega na Nicaragua a karo na huɗu

    A yau Litinin Shugaba Daniel Ortega na Nicaragua zai sha rantsuwar kama aiki a wa'adin mulki na hudu a jere bayan zaben da Amurka da Tarayyar Turai suka kira da "abin kunya".

    A watan Nuwamba ne Mista Ortega ya lashe zaɓen da kashi 75 cikin 100 na ƙuri'un da aka kaɗa bayan fafatawa da abokan hamayya kusan bakwai.

    Wakilin BBC ya ce cikin ƙasashen da za su aika wakilai domin halartar bikin rantsuwar Mista Ortega akawai Rasha da China da Koriya ta Arewa da Iran da kuma manyan aminan Nicaragua wato Venezuela da Cuba.

  14. Matan Saudiyya 10 sun yi nasara a gasar tseren doki ta Sarki Abdulaziz

    Saudiyya

    Asalin hoton, Getty Images

    Matan Saudiyya mahaya dawaki 10 ne suka yi nasara cikin 38 da suka fafata a gasar tsere karo na shida yayin Bikin Raƙumi na Sarki Abdulaziz ranar Asabar.

    Ɗaruruwan 'yan kallo sun taru don shaida tseren da mata suka fafata a karon farko a tarihin bikin, kamar yadda jaridar Saudi Gazette ta ruwaito.

    Wannan ne karon farko da aka ƙaddamar da zagayen 'yan ɗai-ɗai a tseren wanda ake gudanarwa a filin da ya kai faɗin murabba'in kilomita 32 a yankin Sayahadah.

    Waɗanda suka yi nasara a tseren za su samu kyautar kuɗi riyal miliyan 88, mafi girma a duniya a tsren dabbobi.

    An shigar da mata gasar ce da zimmar ƙarfafa musu gwiwar shiga al'amura sanye da tufafinsu na gargajiya da kuma faɗaɗa azuzwan masu shiga gasar.

  15. Miliyoyin ɗalibai sun koma makarantu a Uganda bayan kusan shekara biyu

    Uganda

    Miliyoyin ɗalibai sun koma makarantu a Uganda a safiyar yau Litinin bayan kusan shekara biyu sakamakon annobar korona.

    Makarantun na Uganda sun fi kusan dukkan sauran makarantu a duniya daɗewa a kulle bayan an rufe su a watan Maris na 2020.

    Za a ciyar da ɗalibai zuwa ajin gaba sannan za a gudanar da ayyuka na musamman don ba su damar iya karatun da aka wuce su.

    Hukumar tsare-tsare ta ƙasar ta yi hasashen cewa aƙalla kashi 30 cikin 100 na ɗaliban da suke makaranta kafin zuwan annobar ba za su koma ba.

    Wakilin BBC Patience Atuhaire ya ziyarci wata makaranta a Kampala babban birnin ƙasar:

    Uganda
    Uganda
  16. Ba a kashe dakarunmu ba a rikicin haƙar gwal a Katsina - Sojojin Najeriya

    Sojojin Najeriya

    Asalin hoton, Nigerian Army

    Rundunar sojin Najeriya ta ce babu sojanta ko ɗaya da aka kashe yayin fafatawar da wasu masu haƙar gwal suka yi a Ƙaramar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina da ke arewacin ƙasar.

    Cikin wata sanarwa ranar Lahadi, mai magana da yawun rundunar Janar Onyema Nwachukwu ya nemi 'yan Najeriya su yi watsi da rahotannin da ke cewa an kashe soja biyu da kuma masu haƙar ma'adanai bakwai sakamakon rikicin da ya ɓarke a garin Magama kan gwal.

    Janar Nwachukwu ya ce rahoton "ba shi da tushe" kuma "an ƙirƙire shi ne da zimmar ɓata wa sojin Najeriya suna".

    Ya ƙara da cewa babu soja ko ɗaya da lamarin ya ritsa da shi a haƙar ma'adanai ba bisa ƙa'ida ba ranar 5 ga watan Janairu kamar yadda rahoton ya nuna.

    Rahotanni sun ce rikicin ya ɓarke ne bayan sojojin sun ce sai an ƙara musu kuɗin da suka amince tun farko na 500,000 kan kowace mahaƙa bayan sun ga yawan gwal ɗin da aka haƙo.

  17. Novak Djokovic ya yi nasara a kotun Australia

    Novak Djokovic

    Asalin hoton, Getty Images

    Kotu ta umarci jami'an tsaron Australia su saki ɗan wasan tennis Novak Djokovic sakamakon "rashin ƙwaƙƙwaran dalili" na tsare shi da kuma soke bizarsa.

    Mai Shari'a Anthony Kelly ya ba da umarnin a janye matakin ƙwace wa Djokovic biza nan take.

    Hakan na nufin bizarsa sahihiya ce kuma zai iya shiga Australia don fafatawa a gasar Australian Open, inda yake riƙe da kambin gasar da ya lashe a 2021.

    Tun farko an tsare Djokovic mai shekara 34 bayan ya shiga ƙasar sakamakon bai yi allurar rigakafin korona ba, wadda ya ce likitoci sun amince cewa yana da lalurar da ta sa ba sai ya yi ba.

  18. Yajin aikin 'yan Adaidaita-Sahu ya jefa mazauna Kano cikin tasku

    Kano

    Titunan birnin Kano a arewacin Najeriya sun kasance fayau sakamakon yajin aikin da direbobin babur mai ƙafa uku - ko kuma Adaidaita-Sahu - suka fara a safiyar Litinin.

    An ga ma'aikata da ɗalibai da masu zuwa wuraren sana'o'i na takawa da ƙafarsu a gefen tituna.

    Wakilin BBC a Kano ya ce an girke jami'an tsaro a wasu muhimman wurare na birnin.

    Kano

    Ƙungiyar direbobin ta faɗa cikin wata sanarwa cewa sun yanke shawarar fara yajin aikin ne na mako ɗaya daga Litinin 10 ga watan Janairu sakamakon "cin mutuncin da ake mana kan karɓar haraji".

    Kazalika, sun gargaɗi abokan aikinsu da cewa: "Duk ɗan Adaidaita-Sahu na Kano, idan ka sake ka fito aiki a ranar to duk abin da ya faru da mashin ɗinka to kai ka jawo wa kanka."

    Kano
    Kano
  19. Ɗaliban Kaduna za su fara zuwa makaranta sau huɗu a sati

    Gwamna Nasir El-Rufai

    Asalin hoton, KDSG

    Bayanan hoto, A ranar 1 ga watan Disamba gwamnatin Kaduna ta fara aiki da kwanakin aiki huɗu a mako

    Gwamnatin Kaduna ta umarci makarantun gwamnati a jihar da su fara aiki kwana huɗu a sati - maimakon biyar - yayin da ake komawa makarantun a yau Litinin don ci gaba da zango na biyu na shekarar karatu ta 2021/2022.

    Kwamashiniyar Ilimi Halima Lawal ce ta bayar da umarnin a Kaduna ranar Lahadi cikin wata sanarwa da kamfanin Labarai na NAN ya ruwaito.

    A ranar 1 ga watan Disamban 2021 ne gwamnatin Kaduna ta fara aiki da kwanakin aiki huɗu a mako.

    Mai magana da yawun Gwamna Nasir El-Rufai ya ce nan gaba su ma makarantu masu zaman kansu za su fara aiki da sabon tsarin.

    Kwamashiniyar ta ce za su tabbata cewa an kammala sabon zangon karatun cikin tsari ba tare da sabon tsarin ya lalata kalanda ko jadawali ba.

  20. Ecowas ta ƙaƙaba wa Mali sabbin takunkumai

    Buhari da wakilin Mali

    Asalin hoton, State House

    Bayanan hoto, Ranar Juma'a ne Shugaba Buahri ya tarɓi wakilin gwamnatin soja ta Mali a Abuja

    Shugabannin ƙasashen Afirka ta Yamma sun amince da kakaba wa Mali tsauraran takunkumin tattalin arziki bayan kin cika alkawarin da sojin mulki juyin mulki suka ɗauka na miƙa mulki ga farar hula.

    Takunkuman sun haɗa da rufe dukkan iyakokinsu da Mali da na tattalin arziki, sun kuma cimma hakan ne a taron koli da suka yi karkashin jagorancin shugaban kungiyar ECOWAS kuma shugaban Ghana Nana Akuffo Addo a birnin Accra.

    Shugaban Burkina Faso Roche Kabore ya ce zabe ne kadai zai bai wa Mali damar sake ginuwa. "Idan har za mu duba halin da ake ciki a kasar, ya kamata mu yi tunanin Mali na bukatar garanbawul ta fuskar siyasa da tattalin arziki da harkokin rayuwa," in ji shi.

    Ya ƙara da cewa "za a cimma hakan ne kadai idan aka gudanar da sahihin zabe karkashin mulkin Dimukradiyya".

    Goïta

    Asalin hoton, Getty Images

    Bayanan hoto, Kanar Asimi Goïta ya naɗa kan sa shugaban gwamnatin Mali bayan juyin mulki a watan Oktoba