Majalisar Dokoki ta mayar wa Buhari kasafin kudin 2022

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Mu kwana lafiya

    A nan za mu rufe wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye. Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu.

    Ku biyo mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni.

    Mu kwana lafiya.

  2. Mutum bakwai sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a Neja

    Abubakar Sani Bello

    Asalin hoton, OTHER

    Mutum uku 'yan gida daya na cikin mutane bakwai da suka mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a kauyen Zhigiri na karamar hukumar Shiroro da ke jihar Neja a arewacin Najeriya.

    Jaridar ThisDay, wadda ta rawaito wannan labari, ta kara da cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi da maraice.

    Cikin wadanda suka mutu har da mata guda biyu na wani mutum mai suna Mallam Muazu Babangida da kuma dansa guda daya.

    Sai dai ba a san sauran mutanen da suka mutu ba.

    Rahotanni sun ce lamarin ya faru ne lokacin da mutanen suke kan hanyarsu ta zuwa kauyen Dnaweto domin halartar bikin radin suna.

    Hukumomi ba su ce komai a kan batun ba kawo lokacin rubuta wannan labarin, sai dai sanarwar da kungiyar Coalition of Shiroro Association ta fitar ranar Talata ta tabbatar da faruwar lamarin.

  3. Majalisar Dokoki ta mayar wa Buhari kasafin kudin 2022

    Ahmad Lawan

    Asalin hoton, NASS

    Majalisar Dokokin Tarayya ta mayar wa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kasafin kudin kasar na shekarar 2022 domin ya sanya masa hannu.

    Akawun Majalisar Dokokin, Amos Ojo, ne ya aike wa shugaban kasar kasafin kudin tare da wasikar da aka rubuta ranar 24 ga watan Disamba, a cewar jaridar Premium Times da ake wallafawa a shafin intanet.

    Ta kara da cewa Akawun Majalisar Dokokin ya shaida wa Shugaba Buhari cewa ya aike masa da kasafin kudin ne kamar yadda dokokin Najeriya suka bukaci ya yi.

    Ya aike da kasafin kudin ne mako guda bayan 'yan majalisar dattawa da na wakilai sun amince da shi.

    'Yan majalisar sun amince da naira tiriliyan 17.1 maimakon naira tiriliyan 16.3 da shugaban ya nemi su amince – abin da ke nuna sun kara naira biliyan 700.

    Dokokin Najeriya sun bai wa 'yan majalisar damar karawa ko rage adadin kasafin kudin.

  4. Kotu ta dakatar da kamfanin Shell daga hakar man fetur

    Masu zanga-zanga

    Asalin hoton, EPA

    Wata kotu a Afirka Ta Kudu ta dakatar da kamfanin Shell daga yin gwajin kasa domin hako fetur a gabar teku da ke gabashin kasar, har sai ta kammala sauraren karar da ke gabanta game da batun.

    Masu rajin kare muhalli sun jinjina wa kotun kan daukar wannan mataki suna masu fargabar cewa kyale kamfanin ya hako mai a yankin zai sa halittun ruwa su mutu.

    Shell ya ce ya "dakatar" da gudanar da ayyuka a yankin a yayin da zai yi nazari kan hukuncin kotun.

    Ministan Makamashin Afirka Ta Kudu Gwede Mantashe ya soki masu adawa da aikin hako mai a yankin yana mai cewa suna so su hana Afirka hako albarkatun kasar da Allah ya huwace mata.

  5. Bikin raya al’adun gargajiya na kabilar Tangale

    Bikin Tangale

    Asalin hoton, Abdul Mohammed

    A ranar Talata ne aka kammala bikin raya al’adun gargajiya na kabilar Tangale a garin Kaltungo da ke jihar Gombe a arewa maso gabashin Najeriya.

    Bikin Tangale

    Asalin hoton, Abdul Mohammed

    Kabilar Tangale na daya daga cikin manyan kabilun jihar Gombe galibin ‘yan kabilar kuma na zaune a kananan hukomomin Kaltungo, Billiri da Shongom.

    Bikin Tangale

    Asalin hoton, Abdul Mohammed

    Bayanan hoto, Abdul Mohammed

    Sarkin Kaltungo, wato Mai Kaltungo, Injiniya Saleh Muhammad Ya jaddada bukatar zaman lafiya tsakanin al’uma yana mai kira ga matasa su rungumi al’adun gargajiya musamman kyawawan dabi’u a maimakon rungumar al’adun kasashen waje marasa kyau.

    Bikin Tangale

    Asalin hoton, Abdul Mohammed

    Ana gudanar da bikin ne a duk karshen shekara kuma shugabar kwamitin shirya bikin, Hajiya Sa’adatu Sa’ad Mustapha, ta bayyana cewa an shirya bikin ne domin nuna kyawawan al’adun gargajiya na kabilar Tangale.

  6. Masarautar Dansadau a Zamfara na murnar cika wata ɗaya ba tare da harin 'yan fashi ba

    'Yan fashin daji

    Asalin hoton, Daily Trust

    Al’ummar Masarautar Dansadau a Jihar Zamfara ta Najeriya na murnar kwashe fiye da wata ɗaya ba tare da fuskantar hare-hare daga ‘yan fashin daji ba bayan wani sulhu da suka yi da su.

    A makonnin bayan ne dai rahotanni suka ce ‘yan fashin ƙarƙashin jagorancin Ali Kachalla suka nemi yin sulhu da masarautar kuma daga ƙarshe ɓangarorin biyu suka amince da sharuɗɗan juna.

    Hare-haren da ‘yan fashin ke kai wa ƙauyuka a shiyyar arewa maso yammacin Najeriya sun soma ne daga yankin fiye da shekara 11 da suka wuce.

    Haruna Shehu – Tangaza ya tattauna da Alhaji Mustafa Umar Wazirin Dansadau, inda ya fara da tambayar sa halin da suke cikin a yanzu.

    Latsa hoton sama ku saurari hirar:

    Bayanan sautiMasarautar Dansadau a Zamfara na murnar cika wata ɗaya ba tare da harin 'yan fashi ba
  7. Za a hukunta masu gine-ginen da suka ƙi kammalawa a Abuja

    Abuja

    Asalin hoton, Rex Feauters

    Hukumar kula da Abuja babban birnin Najeriya Federal Capital Territory Administration (FCTA) ta ce ta shirya tsaf don hukunta masu gidajen da suka ƙi kammala gininsu a ƙwaryar birnin.

    Wata sanarwa da daraktan filaye Alhaji Adamu Hussaini ya fitar wadda kuma jaridar Daily Trust ta ruwaito ta ce sun ɗauki matakin ne domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin mazauna Abuja mai girman murabba'in kilomita 250.

    "Domin tabbatar da tsaron lafiyar rayuka da dukiyoyi a ciki da kewayen murabba'in kilomita 250 na Abuja, akwai yiwuwar hukumar ta kamamala shirye-shirye domin hukunta masu gidajen da suka bar su ba tare da an kammala ba," a cewar sanarwar.

    Ya ƙara da cewa hukuncin za su haɗa da ƙwace shaidar mallaka, sannan ya shawarci masu giajen da su kammala gininsu.

  8. Faransa ta tsaurara dokokin yaƙi da korona

    Faransa

    Asalin hoton, Getty Images

    A wata mai kama da haka Faransa ta zamo kasa ta baya-bayan nan a Turai da ta tsaurara matakan hana bazuwar nau'in Omicron na korona.

    A yanzu Faransa ta sa dokar saka takunkumi a waje amma kuma ba ta kakaba dokar kulle ba.

    Kazalika an umurci ma'aikata da su yi aiki daga gida na akalla kwana uku a sati.

    Yayin sanar da sabbin matakan, Firaminista Jean Castex ya bayyana annobar a matsayin wani wasan kwaikwayo da ba shi da lokacin arewa.

    Faransa na daga cikin kasashen da suka yi nasarar yi wa mutane da dama rigakafin korona, amma kuma Omicron na bazuwa kamar wutar daji.

  9. Mata na zanga-zangar kashe tsoffin sojoji da suka zargi Taliban da yi

    Wani dandazon mata sun yi maci a titunan Kabul babban birnin Afghanistan a yau Talata, suna zargin gwamnatin Taliban da kashe sojojin tsohuwar gwamnati a asirce wadda Amurka ke goyon baya.

    Kamfanin labarai na AFP ya ruwaito mata kusan 30 sun taru a kusa da wani masallaci yayin da dakarun Taliban ke ƙoƙarin hana 'yan jarida ɗaukar rahoton taron.

    Jami'an tsaron Taliban sun tsare wasu 'yan jarida kafin daga baya su sake su bayan sun goge hotuna daga kyamarar wasu daga cikinsu.

    Tun bayan dawowarta kan mulki a watan Agusta, Taliban ta haramta zanga-zangar da gwamnati ba ta amince da ita ba.

    Wani rahoto da ƙungiyoyin Amnesty International da Human Rights Watch da Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) suka fitar a kwanan nan ya zargi ƙungiyar da kashe mutum kusan 100 ba tare da shari'a ba.

  10. Zazzaɓin Lassa ya kashe mutum 92 a Najeriya

    Ɓeraye

    Asalin hoton, MATTHIEU AUBRY

    Yayin da annobar korona ke ci gaba ratsa sassan Najeriya, sabon rahoton hukumar NCDC ya nuna cewa zazzaɓin Lassa ya halaka mutum 92 a shekarar 2021.

    Kazalika, rahoton ya ce ya zuwa lokacin rahoton Mako na 50, jumillar mutum 454 ne suka harbu da zazzaɓin a ƙaramar hukuma 66 da ke jiha 16 na faɗin Najeriya da kuma Abuja babban birnin ƙasar.

    Jiha uku daga ciki da suka haɗa da Edo (197) da Ondo (159) da Taraba (21) ne ke da kashi 83 cikin 100 na dukkan mutanen da aka tabbatar sun kamun.

    Jihohin Bauchi da Ebonyi na da mutum 18 kowaccensu, a cewar NCDC.

  11. Faransa za ta sake rufe masallaci kan zargin tsattsauran ra'ayin Musulunci

    Masallaci  a Faransa

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomin Faransa sun ba da umarnin rufe wani masallaci a arewacin ƙasar saboda tsattsauran ra'ayin limamin masallacin, kamar yadda suka faɗa wa AFP a yau Talata.

    Masallacin da ke garin Beauvais mai al'umma 50,000 mai nisan kilomita 100 daga birnin Paris, za a rufe shi tsawon wata shida, a cewar hukumomin gundumar Oise wanda ya ƙunshi garin Beauvais.

    Sun ce huɗubar da ake yi a wurin tana haddasa "ƙiyayya" da kuma "goyon bayan jihadi".

    Yunƙurin na zuwa ne mako biyu kacal bayan Ministan Harkokin Cikin Gida Gerald Darmanin ya bayyana cewa ya nemi a rufe masallacin saboda limamin "yana haƙon Kiristoci da 'yan luwaɗi da Yahudawa" a huɗubobinsa. Ministan ya ce hakan "ba za ta saɓu ba".

    Bisa doka hukumomi za su gudanar da ayyukan leƙen asiri da tattara bayanai na kwana 10 kafin a ɗauki mataki amma sun faɗa wa AFP a yau Talata cewa nan da kwana biyu za a rufe masallacin.

    A farkon shekarar nan ne gwamnatin Faransa ta ce za ta tsaurara sa ido kan masallatai da wuraren ibada da zimmar kakkaɓe tsattsauran ra'ayin Musulunci, matakin da ya jawo zazzafar muhawara a faɗin duniya.

    Ma'aikatar cikin gida ta ce ya zuwa watan da ya gabata, an binciki masallatai kusan 100 cikin fiye da 2,600 da ake da su a Faransa game da zargin "yaɗa aƙidar tawaye".

  12. Ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita yankuna a Brazil

    Brazil

    Gwamnan Bahia a Brazil ya ce jihar na fuskantar mummunan bala'in da ba su taba ganin irinsa ba a tarihi, bayan da ambaliya ta kashe sama da mutun 20 kawo yanzu.

    Rui Costa ya kai ziyara cibiyoyin ba da agaji a jihar da ke arewa maso gabashin kasar, inda aka jibge sama da mutun 60,000 da aka kwashe daga gidajensu.

    Wakilin BBC ya ce an shafe makonni ana tafka ruwan sama a arewa maso gabashin Indiya bayan an ɗauki lokaci mai tsawo ana fuskantar fari.

  13. Motar fasinja ta afka cikin kogi a Jihar Legas

    Legas

    Asalin hoton, Pius Utomi Ekpei

    Ana fargabar mutum ɗaya ya rasu a Jihar Legas yayin da wata motar bas ta fasinja ta afka cikin kogi ranar Litinin.

    Waɗanda lamarin ya faru a kan idonsu sun ce ana tunanin direban ya kasa sarrafa motar ce lokacin da ta faɗa kogin da ke yankin Iyana-Oworo ɗauke da wasu mutane da ke halartar biki a yankin.

    An ga yadda kayayyakin mutane suke iyo a saman ruwa tare da sauran abubuwan da ke cikin motar. Sai dai rahotanni sun ce mutanen da ke wucewa sun ceto dukkan fasinjojin.

    Daga baya ne kuma wasu daga fasinjojin suka ankara cewa ba su ga mutum ɗaya ba.

    Daga bisani aka ga wata mace kwance ba a cikin hayyacinta ba kuma nan take aka kai ta asibiti, inda ta rasu a can.

    Hukumomi a jihar ba su yi ƙarin bayani ba ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoton.

  14. An ƙaƙaba wa Indiyawa mazauna Delhi dokar kulle

    Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    An ƙaƙaba wa mazauna babban birnin IndiyaDelhi dokar hana fita bayan an fara samun bazuwar nau'in korona na Omicron.

    Ba a Delhi kaɗai ba, jihohi da dama sun tsaurara dokoki don tunkarar Omicron.

    Indiya ta ji jiki sosai lokacin da nau'in Delta ya shiga kasar a farkon wannan shekara.

    Ana fargabar Omicron ya bazu cikin sauri a kasar mai yawan al'umma da kuma rashin wadatattun kayan aiki a asibiti.

  15. Korona ta sake kashe mutum biyu a Najeriya, 859 sun kamu

    Hukumar yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta NCDC a Najeriya ta ce ƙarin mutum 859 sun kamu da cutar korona ranar Litinin.

    Haka nan cutar ta yi ajalin wasu mutum biyu a Litinin ɗin.

    Jiha 14 ne suka fuskanci ƙaruwar a wannan karon, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar. Su ne:

    • Lagos (555)
    • Abuja (57)
    • Rivers (44)
    • Plateau (43)
    • Edo (41)
    • Ondo (34)
    • Kwara (23)
    • Kano (18)
    • Ogun (16)
    • Enugu (11)
    • Oyo (6)
    • Delta (5)
    • Bauchi (3)
    • Bayelsa (3)

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 238,420 ne suka harbu da cutar a Najeriya, sannan ta kashe mutum 3,024. Sai dai mutum 212,770 sun warke kuma an sallame su.

  16. Maraba

    Umar Mikail ne ke muku barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye.

    Za mu kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya tun daga wannan hantsi na Talata har zuwa darenta.

    Ku biyo mu!