Sai da safe
A nan za mu rufe wannan shafi. Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu.
Ku biyo mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni.
Sai da safenku.
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Umar Mikail and Nasidi Adamu Yahaya
A nan za mu rufe wannan shafi. Da fatan kun ji dadin kasancewa tare da mu.
Ku biyo mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni.
Sai da safenku.

Asalin hoton, Borno state government
Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, Babagana Umara Zulum, ya roki masu kwatanta ayyukansa da na sauran gwamnoni su daina.
Ya yi rokon ne a wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Isa Gasau ya fitar ranar Litinin.
Gwamnan ya yaba wa mutanen da ke tallata ayyukansa a shafukan sada zumunta, sai dai ya ce bai kamata a rika kwatanta “ayyukanna da na sauran gwamnoni ba, tun da dukkan jihohin suna da bambanci”.
“Duk da yake Ina matukar godiya bisa dukkan goyon baya da tallata ayyukana, a kwanakin nan, na samu sakonni, inda ake kwatanta ayyukan da muke yi a Borno da na wasu jihohi, a wasu lokutan ma ana zagi.
Gaskiya ba na jin dadi a duk lokacin da aka kwatanta ni da wani gwamna ta hanyar muzanta shi, musamman idan wadanda suke yin hakan suna cikin masu amfani da shafukan sada zumuntar da ke da alaka da mu”, in ji Gwamna Zulum.
Kotu a Rasha ta yanke wa wani sanannen masanin tarihi dauri na shekara 15 a gidan maza, a wata shari'a da aka kwashe tsawon lokaci ana tafkawa.
Yuri Dmitriyev dai ya yi suna ne kan aikinsa na fallasa laifukan da aka tafka lokacin da Joseph Stallin ke jagorancin Tarayyar Soviet, kuma shi ne shugaban wata kungiyar kare hakkin bil'adama a yankinsa.
Wakilin BBC ya ce an dade ana tafka wannan shari'a. A bara kotu ta yanke masa hukuncin dauri na shekara 13, yau kuma kotu ta tsawaita hukuncin zuwa shekara 15.
Kotu ta same shi ne da laifin lalata da wata yarinya da ya rena a matsayin diya, da daukan hotunan tsiraicin yarinyar da kuma mallakar makami. Ya dai musa zarge-zargen.
Magoya bayansa na zargin cewa ana kokarin cin zarafinsa ne saboda aikinsa.

Asalin hoton, Getty Images
Gwamnatin sojin Mali ta soma gudanar da taron kwanaki hudu kan yadda za ta mika mulki ga farar hula bayan juyin mulkin da aka yi a watan Agustan 2020.
Hukumomin sojin sun bayyana cewa taron wata dama ce ga al'ummar kasar wajen bayar da shawarwari kan sauye-sauyen da suke so a yi, sai dai manyan kungiyoyin farar hula sun yi watsi da shi suna masu cewa ba za su halarce shi ba don ba shi da amfani.
Taron “zai yi nazari kan halin da kasa take ciki sannan ya fitar da darusan da aka koya game da shi”, a cewar shugaban sojojin da suka yi juyin mulkin, Kanar Assimi Goia, yayin da yake bude taron ranar Litinin.
“Alhakinku ne ku bayar da kwararan shawarwari, a samar da mafita ga matsalolin da muke fama da su,” a cewarsa.

Asalin hoton, Getty Images
Wasu sabbin alkaluma sun nuna cewa 'yan wasa da ma'aikatan Gasar Firimiya 103 ne suka kamu da cutar korona a cikin kwana bakwai zuwa ranar 26 ga watan Disamba.
A makon da ya gaba ce shi, alkaluma sun nuna mutum 90 ne suka kamu da cutar.
An yi wa mutum 15,186 gwajin cutar daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Disamba, a yayin da hukumomin Gasar Firimiya suka sake kaddamar da matakin yin gwaji a kullum kan 'yan wasa da ma'aikata.
An soke gudanar da manyan wasannin Gasar Firimiya a watan Disamba saboda annobar korona.

Asalin hoton, Channels TV
Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu 'yan daba sun kai hari filin da jam'iyyar PDP take gudanar da zabukan shugabanninta a Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Gidan talbijin na Channels ya rawaito cewa tun da fari an so a gudanar da taron a Zaitun Oil mill, da ke bayan hukumar alhazai amma aka sauya zuwa Command Guest House da ke Gusau.
Rahotanni sun ce 'yan dabar siyasa sun yi wa wurin dirar-mikiya da sanyin safiyar Litinin inda suka lalata kayan zabe da fom-fom da motocin 'yan jam'iyyar PDP da kuma kujeru sannan suka cinna wuta kan rumfunan da aka kafa.

Asalin hoton, Channels TV
Hotunan da aka rika watsa a shafukan intanet sun nuna yadda wurin ya kama da wuta bayan an yi kaca-kaca da shi.
Rahotanni sun ambato Umar Aminu, wani hadimin mataimakin gwamnan Zamfara, Mahdi Aliyu Gusau, yana cewa babu wanda ya isa ya yi musu barazanar da za ta kai su fasa gudanar da taron.
An soma zaman doya-da-manja tsakanin Gwamna Mohammed Matawalle da mataimakinsa tun bayan gwamnan, wanda aka zaba a karkashin jam'iyyar PDP, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.
Ministan Yada Labarai na Pakistan Fawad Chaundhry ya soki Taliban kan dokar da ta fito da ita ta takaita zirga-zirgar mata, inda ya bayyana ta a matsayin "ci-baya", kuma "haɗari ga kasar Pakistan".
Mista Chaundhry ya ce babban abin da Pakistan ke kokarin fada da shi shi ne ra'ayin rikau a Afghanistan, amma kasarsa na matukar son tallafa wa mutanen Afghanistan.
A jiya Lahadi ne gwamnatin Taliban ta ce mata ba za su iya yin tafiya mai nisa ba ba tare da samun rakiyar wani muharraminsu ba.
Kazalika gwamnatin Taliban ta umarci masu ababen hawa da kar su sake su ɗauki duk wata mace da ba ta sanya hijabi ba.

Asalin hoton, Reuters
Shugaban Somalia Mohamed Abdullahi Farmajo ya dakatar da firaministansa, yana mai zargin sa da hannu a satar fili.
Ofishin Mohamed Hussein Roble ya ce sanarwar da ofishin shugaban ƙasar ya fitar "abin takaici ne" kuma zai ci gaba da aikinsa a matsayin firaminista.
Masu goyon bayansa sun ce shugaban ƙasar yana yunƙurin yin "juyin mulki ne a fakaice".
Jami'an tsaro sun yi yunƙurin hana Mista Roble shiga ofis a yau Litinin amma ba su yi nasara ba.
Shugabannin biyu sun daɗe suna rigima kan shugabanci, abin da ya sa ake fargabar hakan zai ƙara tsaurara rashin zaman lafiya a Somalia.
Somalia ta daɗe ba ta da tsayayyar gwamnatin ƙasa tun bayan da aka hamɓarar da gwamnatin Siad Barre a 1991.

Asalin hoton, Other
Sirikin Rochas Okorocha da 'yan sanda suka kama a Jihar Imo, Uche Nwosu, ya ce 'yan sandan ba su sanar da shi ba kafin su kama shi.
A ranar Lahadi ne 'yan sandan Imo suka kama tsohon ɗan takarar gwamnan lokacin da yake gudanar da adddu'o'i a coci. Sun isa wurin ɗauke da makamai sannan suka yi harbi a sama kafin su tafi da shi.
Mista Nwosu ya bayyana hakan ne bayan jami'an taron sun sake shi a yau Litinin.
Mai taimaka masa kan kafafen yaɗa labarai, Nwadike Chikezie, ya faɗa cikin wata sanarwa cewa mai gidan nasa bai kwana a hannun 'yan sandan ba.

Asalin hoton, TRUCKEE MEADOWS FIRE DEPARTMENT/ TWITTER
Ƙanƙara ta lulluɓe yankin yammacin Amurka, inda ta jefa dubbai cikin duhun rashin lantarki.
Ƙanƙara mai tudun inci 30 ta yi ta faɗowa a arewacin California cikin awa 24, hakan ya jawo ɗaukewar lantarki da kuma rufe tituna.
Ana ta yaɗa bayanan gargaɗi a jihohi shida na yankin.
A ranakun ƙarshen mako, guguwa haɗe da ambaliyar ruwa ta afka wa kudancin Carlifornia, wadda ta lalata lantarki da kuma cika tituna da ruwa.
Hukumar yanayi ta ƙasa ta ce ruwan sama mai tudun inci 1.8 zai ci gaba da zubowa a Reno, Navada daga Lahadi da dare zuwa Ltinin.

Asalin hoton, Reuters
An ci gaba da samun jiragen da ake soke tashinsu yayin da aka shiga sabon mako a faɗin duniya, abin da ke ƙara jefa matafiya cikin ƙunci.
Jirgi fiye da 1,400 aka soke a ranar Litinin, kuma sokewar ta fi shafar zirga-zirga zuwa ko fitowa daga China a Amurka, a cewar shafin FlightwAware.com mai bin sawun tafiye-tafiye.
Kamfanonin jirage a Amurka sun ce sokewar ta fi alaƙa da rashin lafiyar ma'aikatansu da kuma killace kansu a suke yi.
Jumilla, an soke jirgi fiye da 8,000 tun daga ranar Juma'a yayin da ake bikin Kirsimeti.
Gwamnatin Israila ta amince da kashe dala miliyan300 don gina wani rukunin gidaje a tuddan Golan.
Firaminista Naftali Bennett ya ce burinsu shi ne su ninka yawan Yahudawa da ke zaune a yankin na Golan Heights.
Masana na ganin wannan wani yunkuri ne gwamnati a Tel Aviv ke yi na kara tabbatar da iko da Tuddan Golan, wanda ta ƙwace daga hannun Syria sama da shekara 50 da suka wuce.

Asalin hoton, Other
'Yan sanda ne suka kama Uche Nwosu, sirikin tsohon Gwamnan Imo Rochas Okorocha, a cewar wata sanarwa daga 'yan sandan jihar.
'Yan sandan ɗauke da makamai sun yi awon gaba da tsohon ɗan takarar gwamnan Imo ɗin ne a Cocin St. Peter’s Anglican da ke Ƙaramar Hukumar Nkwerre ranar Lahadi.
Sai da suka yi harbe-harbe a sama don tarwatsa mutane kafin su tafi da shi.
"Muna sanar da jama'a cewa ba sace Uche Nwosu aka yi ba, 'yan sanda ne suka kama shi kuma rundunar 'yan sandan Imo na sane da kamen nasa," in ji wata sanarwa da kakakin rundunar Michael Abattam ya fitar.

Asalin hoton, Getty Images
A na ci gaba da shirye-shirye da za a shafe mako ɗaya ana yi a Afrika ta Kudu don nuna alhinin mutuwar Archbishop Desmond Tutu.
Mai fafutukar kare haƙƙin bakaken fatar ya rasu da safiyar Asabar yana da shekaru 90.
Wakiliyar BBC ta ce da ma 'The Arch' kamar yadda ake masa laƙabi, ya shafe sama da shekara 20 yana fama da kansar marena.
Gwamnatin Afrika ta Kudu ta bayyana cewa za a yi jana'izar marigayi Tutu a ranar 1 ga watan Janairu.
Shugaba Cyril Ramaphosa ya ce za a yi ƙasa-ƙasa da tutar ƙasar don girmamawa ga marigayin.
Shugabanni a fadin duniya na ci gaba da ta'aziyyar mutuwar Mista Tutu, ciki har da Fafaroma Francis da Shugaba Biden na Amurka da Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya da ma Sarauniya Elizabeth ta Birtaniya.

Asalin hoton, State House
Fadar Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta ce shugaban ƙasar lafiyarsa ƙalau bayan an samu rahoton cewa makusantansa sun kamu da cutar korona a ƙarshen mako.
Mai magana da yawun fadar Femi Adesina ne ya bayyana hakan lokacin da ya bayyana ta cikin shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels ranar Lahadi.
Da aka tambaye shi ko Buhari ya killace kansa sai ya ce: "Ina ganin shugaban ƙasa lafiyarsa ƙalau, yana ci gaba da ayyukansa kamar yadda ya saba. Amma idan wani na kusa da shi ya kamu (da korona), zai killace kansa har sai ya warke. Saboda haka shugaban ƙasa yana ci gaba da ayyukansa kamar kullum."
Game da mutanen da suka kamu da cutar a fadar ta Aso Rock Villa, Adesina ya ce ba zai faɗi sunansu ba saboda bai sani ba.
"Abin da zan ce shi ne ma'aikatan shugaban ƙasa su ma mutane ne...don muna ma'aikatan fadar shugaban ƙasa hakan ba ya nufin ba za mu kamu da cutuka ba...ba ni da ikon faɗar waɗanda suka kamu saboda ban sani ba.
"Garba Shehu ya tabbatar cewa ya kamu amma ya ce ba ta yi tsanani ba. Kuma na yi imanin cewa zuwa yanzu ya kamata ya warke tun da abin ya faru tun Laraba. Saboda haka babu wani abin tashin hankali."

Asalin hoton, NCDC
Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce mutum takwas ne suka rasu ranar Lahadi - washegarin Ranar Kirsimeti - sakamakon cutar korona.
Haka nan, wasu 1,547 sun kamu da cutar a Lahadin, abin da ya sa jumillar adadinsu ya kai 237,561, yayin da waɗanda cutar ta kashe kuma suka zama 3022.
Alƙaluman da NCDC ta fitar ranar Asabar sun nuna cewa mutum 20 ne suka mutu a ranar ta Kirsimeti.
Waɗanda suka kamun sun fito ne daga jiha 10, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar. Su ne:

Asalin hoton, Nigerian Army
Dakarun runduna ta 82 ta sojojin Najeriya a Jihar Inugu sun kama Godwin Nnamdi, wani jagoran haramtacciyar ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) ta 'yan aware a kudancin ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar Birgediya Janar Onyema Nwachukwu ya ce dakarun rundunar Operation Golden Dawn ne suka kama wanda ake zargin a ranar Kirsimeti.
Janar Nwachukwu ya ce an kama "gawurtaccen" shugaban ƙungiyar yayin wani sintiri a Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas.
Sojojin sun ƙwace bindigar AK-47 da harsasai da kuma wayar salula daga hannun Godwin Nnamdi, a cewar janar ɗin.
"An kama jagoran IPOB/ESN yayin wani samame a wani sansani da ake zargin shi ne matsugunin ƙungiyar a Dajin Akpowfu da ke Ƙaramar Hukumar Nkanu ta Gabas," in ji shi.
Maraba da sake haɗuwa a wannan shafi na labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan hantsi.