Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An rage wa ma’aikata kwanakin aiki a Kaduna

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau, Nasidi Adamu Yahaya and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Wa zai lashe kyautar Ballon d'Or ta bana

    Ana dab da sanin gwarzon ɗan ƙwallon kafar duniya na bana inda za a sanar da kyautar Ballon d'Or a yau Litinin 29 ga watan Nuwamba.

  2. Isra'ila za ta karɓi Yahudawan Habasha 3,000

    Gwamnatin Isra'ila ta amince ta karɓi ƴan gudun hijirar dubban Yahudawa daga Habasha da ke fama da yaƙi waɗanda suka daɗe suna jira domin haɗuwa da ƴan uwansa a Isra'ila.

    Yahudawan Habasha kimanin 140,000 ke zaune a Isra'ila. Kuma an ƙiyasta cewa kusan Yahudawa 6,000 suka rage a Habasha.

    Ko da yake asalinsu Yahudawa ne, amma Isra'ila ba ta ɗaukar su a matsayin Yahudawa ƙarƙashin dokokin addini, amma maimakon haka suna ta ƙoƙarin shiga ƙasar ƙarƙashin shirin amincewar gwamnati na sake haɗuwa da ƴan uwansu.

    Wasu masu fafutika sun zargi gwamnati na jan ƙafa wajen aiwatar da shirin 2015 na ƙoƙarin dawo da Yahudawan Habasha zuwa Isra'ila cikin shekaru biyar.

  3. Taliban za ta fara tattaunawa da Amurka

    A yau ne ake sa ran Amurka da Taliban za su fara zama na biyu domin tattaunawa tun bayan da kungiyar ta yi juyin mulki a Afghanistan.

    Kafafen watsa labaran cikin gida na Afghanistan sun ce za a yi ganawar kasashen biyu ne a Qatar, abin da ke nuni da irin zakuwar da al'ummar kasar ke yi na ganin an yi wannan tattaunawa.

    Amurka ta ce taron da aka shirya yi mai tsawon mako biyu zai kare muradanta ne da suka hada da yaki da ta'adanci da kuma batun tattalin arzikin Afghanistan wanda ya gurgunce.

  4. Ƴan fashin teku sun kashe mutum huɗu da sace mutum bakwai a Bayelsa

    Rahotanni a Najeriya sun ce wasu ƴan bindiga masu fashin teku sun kai wa ma’aikatan kamfanin haƙo mai hari inda suka kashe mutum huɗu tare da garkuwa da mutum bakwai.

    Jaridar The Nation da ta ruwaito labarin ta ce ƴan fashin sun kai wa ma’aikatan kamfanin Agip hari new a yankunan Okoroma da Ogbokiri-Akassa da ke cikin ƙananan hukumomin Nembe da Brass a jihar Bayelsa.

    Jaridar ta ce ƴan bindigar sun kashe ma’aikatan kamfanin Agip uku da kuma jami’in tsaro da direban jirgin ruwan da suke ciki.

  5. Korona ta kama mutum 23 a Katsina

    Hukumar ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 110 da suka kamu da cutar korona a Najeriya.

    Alƙalumman sun nuna mutum 27 suka kamu da cutar a jihar Imo sai a jihar Katsina da aka samu mutum 23 a ranar Lahadi.

    A jihar Rivers an samu mutum 20, sai jihar Ondo mai mutum 11. A Kaduna ƙarin mutum tara suka kamu da cutar.

    Yanzu jimillar mutum 214,092 cutar ta shafa a Najeriya amma 207,254 sun warke yayin da cutar ta kashe mutum 2,976 a Najeriya.

    Ga jihohin da aka samu ƙarin cutar a Najeriya a ranar Lahadi.

    Imo-27

    Katsina-23

    Rivers-20

    Ondo-11

    Kaduna-9

    FCT-6

    Oyo-6

    Plateau-3

    Osun-2

    Ekiti-1

    Gombe-1

    Zamfara-1

  6. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da za mu kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.