Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

An rage wa ma’aikata kwanakin aiki a Kaduna

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau, Nasidi Adamu Yahaya and Badariyya Tijjani Kalarawi

  1. Rufewa

    A nan za mu rufe wannan shafi da ke kawo muku labarai da rahotanni kai-tsaye.

    Ku kasance da mu gobe domin samun sabbin bayanai.

    Kada ku manta za ku iya karanta wadannan labarai a shafinmu na intanet a bbchausa.com.

    Kuna iya tafka muhawara da bayyana raayoyinku a shafukanmu na sada zumunta a ko da yaushe kuke so.

  2. Mutum 15 sun mutu a mummunan hatsarin mota a Jigawa

    Rundunar 'yan sandan jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya ta sanar da mutuwar mutum 15 a wani hatsarin mota da ya rutsa da su a kan titin Achilafiya zuwa Karnaya.

    Jami'in hulda da jama'a na rundunar ASP Lawan Shiisu, ya tabbatar da hakan ga manema labarai.

    ASP Shiisu, ya ce motoci biyu ne sukai taho mu gama da misalin karfe 5 na yammacin ranar Litinin a karamar hukumar Yan Kwashi da ke jihar a lokacin da daya daga cikin direbobin motar ke kokarin kauce wa ramukan da ke titin.

    Duka motocin biyu samfurin Goldf Wagon ne, kuma nan take suka kama da wuta, daya daga cikin direbobin da fasinja daya sun kone ta yadda ba ma za a iya gane su ba.

  3. An hana alkalai shiga kotu kan dan Gaddafi

    Mazauna kudu maso gabashin birnbin Sebha, sun cika tituna domin yin zanga-zanga kan mamaye kotun yankin da gungun masu dauke da makamai suka yi wa wata kotu tare da hana alkalai da ma'aikata shiga.

    Ana sa ran kotun za ta yi zaman daukaka karar da Saif al-Islam Gaddafi, da ga tsohon shugaban kasar Mu'amnmar Gaddafi, kan hana shi tsayawa takarar shugaban kasa da hukumar zaben kasar ta yi a zabe mai zuwa a watan Disamba mai zuwa.

    Ana kyautata zaton gungun mayakan magoya bayan Khalifa Heftar ne, wanda shi ma batun tsayawarshi takarar ya fuskanci cikas, da kuma shi ma batun na shi ke gaban kotun.

    Masu zanga-zangar na rera wakokin kin amincewa da yi wa fannin shari'a hawan kawara. Sun kuma yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya ta shiga batun domin tabbatar da zaman lafiya a daidai lokacin da ake shirye-shiryen zaben da ake fatan zai kawo sauyi a kasar, wandfa shi ne irin sa cikin shekaru goma.

  4. Uwa ta rasu a kokarin kare danta aTurkiyya

    Wata uwa rasa ranta a kokarin kare danta daga wani rufin kwano da ya rufta, sakamakon guguwar da ta fada wa wasu yankunan birnin Santambul na Turkiyya.

    Kafar yada labaran kasar TRT, ya rawaito cewa baraguzan ginin sun binne uwa da dan nata, nan take ta rasu yayin da dan kuma yake gadon asibiti.

    Kafar yada labaran TRT ta ce wadanda suka shaida lamarin, sun bayyana yadda uwar ta yi saurin bai wa dan nata kariya, lokacin da rufin kwanon ke kokarin fadowa, lamarin da ya sanya ya fado a gadon bayanta.

  5. An daure wani uba saboda raba 'ya'ya da mahaifiyarsu

    An yanke wa wani uba daurin shekara guda a gidan kaso, saboda kwace 'ya'yansa daga hannun mahaifiyarsu, tare da barinsu karkashin kulawar wasu 'yan uwa a Libya.

    Mohammed El Zubaidy, mazaunin Birtaniya, ya take dokar kotu da ke kunshe a takardun kotu da suka bai wa 'ya'yansa mata biyu damar komawa hannun mahaiyarsu Tanya Borg da ke Birtaniya.

    Alkalin kotun ya bayyana Mista Mohammed da wanda ba zai iya kula da 'ya'yansa ba, musamman la'akari da abin da ya faru a shekarar 2015, lokacin da ya dauki 'ya'yan daga hannun mahaifiyarsu, tare da janyo musu shan bakar wuya.

    Kin rattaba hannu kan takardun kotu na amincewa da Mis Tanya kula da yaran, na daga cikin dalilan da suka janyo aka daure shi shekara guda.

  6. Canada da Hong Kong sun gano masu nau'in korona na Omicron

    Kasar Kanada ta sanar da gano mutanen farko da suka kamu da cutar korona nau'in Omicron su biyu, da suka dawo daga balaguro a Najeriya.

    Gwamnatin Ontario, ta tabbatar da cewa mutanen biyu su na babban birnin kasar Ottawa.

    Kawo yanzu an killace dukkan mutanen biyu a cibiyar killace masu fama da cutar korona da ke kasar, da kuma kokarin gano wadanda sukai mu'amala da su. kamar yadda jami'an kasar suka bayyana.

    Ministan lafiyar Canada Jean-Yves Duclos, ya shaidawa manema labarai cewa an yi nasarar gano mau cutar ne a daidai lokacin da suka sauka filin jirgin sama.

    A wani labarin irin wannan da gidan talbijin din CTV na Hong kong ya rawaito, ya tabbatar da samun wasu mutane biyu da nau'in koronar na Omicron, wadanda suka dawo daga kasar Kanada.

    Ma'aikatar lafiya da cibiyar dakilke cutuka masu yaduwa na kasar suka bayyana, sun ce babu tabbacin ko matafiyan 'yan asalin Kanada ne, amma dai sun shiga kasar ne daga can.

    Tun da fari jami'an lafiya sun ce matafiyan sun dauki cutar ne daga wani matafiyi, da ya dawo daga kasar Afirka ta Kudu, su na kuma zama a Otal guda. An dai killace bakin da suke Otal din, za kuma ayi musu gwaji domin tabbatar da ba sa dauke da sabon nau'in koronar mai saurin yaduwa.

  7. Mutum 7 sun mutu a Zanzibar bayan cin naman kunkuru mai guba

    Mutum 7 ciki har da yaro dan shekara uku ne suka mutu, wasu uku na kwance a asibiti a yankin Pemba na Zanzibar, bayan cin naman kunkuru mai dauke da guba.

    Cin naman kunkuru dai ba wani bakon abu ba ne a Zanzibar musamman ga mazauna tsuburai da wadanda ke zaune a yankunan gabar teku.

    Sai dai a yanzu, hukumomi sun haramta cin naman. A kan samu kunkurun da namansa kan gurbata sakamon cin wani abu mai dauke da guba.

    Kawo yanzu dai, babu tabbacin wacce irin guba ce a naman knkurun da ta janyo mutuwar mutanen, kamare yadda kungiyar Turtle Foundation charity ta Zanzibar ta bayyana.

    Akalla iyalai biyar ne suka ci naman kunkurun a yankin Pemba da ke fitaccen tsuburin Zanzibar a ranar Alhamis, kamar yadda shugaban 'yan sandan yankin Juma Said Hamis ya shaidawa BBC.

  8. Bazoum ya yi sauyin ministocin gwamnatinsa

    Shugaban Jamhuriyar, Mohamed Bazoum, ya yi gyaran fuska ga majalisar ministocin gwamnatinsa.

    Ministan Cikin Gida, Alkashe Alhada na daga cikin minstocin da aka sauya wa kujera, inda aka maye shi da Ministan hanyoyi Hamma Souley wanda dan asalin Jahar Tillabery ne, yankin da ke fama da matsalolin tsaro.

    Wannan garanbawl ya zo ne kwana biyu bayan hare-haren a yankin Tera ta jihar Tillabery.

    Latsa alamar lasifika, domin sauraron rahoton da Tchima Illa Issoufou ta aiko mana daga Yamai:

  9. Abin da ya sa gwamnatin Borno za ta saya wa dalibai kekuna 4,000

    Gwamnatin jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya ta yi karin haske kan dalilan da suka sa za ta samar da kekunan hawa 4,000 kyauta, ga daliban jeka-ka-dawo a makarantun dake yankunan karkara.

    Hare-haren Boko Haram cikin sama da shekaru goma sun yi mummunan tasiri kan kokarin samar da ingantaccen ilimi a jihar ta Borno da ma wasu jihohin arewa maso gabashin kasar.

    Lata alamar lasifika don sauraron hirar da Bilkisu Babangida ta yi, da kwamishinan Ilimi na jihar Bornon Alhaji Lawan Abba Wakilbe.

  10. Shugaban kamfanin Tiwita Jack Dorsey ya yi murabus

    Shugaban lkamfanin Tiwita Jack Dorsey ya sanar da yin murabus daga mukaminsa, inda wani babban jami'in kamfanin Parag Agrawal ne zai maye gurbin Mista Jack.

    Mista Dorsey, wanda ya kirkiri shafin na sada zumunta a shekarar 2006, shi ke jan ragamar Tiwita tun daga wancan lokacin.

    A wata sanarwa da ya fitar, Jack ya ce "lokaci ya yi da ya kamata na kauce," tare da cewa kamfanin zai ci gaba da gudana.

    Ya kara da cewa ya amince da kwarewar wanda zai maye gurbinsa a matsayin shugaba, tare da mika sakon godiya gare shi, ya kumna karkare da cewa ''Lokaci ya yi da zai jagoranci kamfanin.''

    A shekarar 2011 ne Mista Agrawal ya fara aiki da Tiwita, kuma tun shekarar 2017 ya ke jagoranbtar fannin fasahar kamfanin.

    Mista Dorsey dai ya dade ya na fuskantar matsin lamba, daga masu zuba jari kan ya sauka daga mukaminsa.

  11. Za a koma tattaunawa kan shirin makamin Nukiliyar Iran

    A karon farko cikin watanni biyar, za a koma teburin shawara domin farfado da yarjejeniyar nukiliyar kasar iran.

    Ministan harkokin kasashen wajen Iran Saeed Khatibzadeh ya shaida cewa kasar a shiriye take domin cimma matsaya game da farfado da yarjejeniyar, amma tawagar kasar ba za su amincewa Amirka ta shiga tattaunawar ba.

    Gwamnatin Iran ta shaida cewa babban fatanta a yayin wannan zama, shi ne cire mata dukkan jerin takunkuman tattalin arzikin da aka kakaba mata.

    Ana sa bangaren Firaministan Israila Naftali Bennett ya gargadi shuwagabannin manyan kasashen da zasu halarci zaman tattaunawar da su yi taka tsantsana da abunda ya kira kutunguilar Iran.

  12. An rage wa ma’aikata kwanakin aiki a Kaduna

    Gwamnatin jihar Kaduna da ke Najeriya ta ce daga ranar 1 ga watan Disamba ma’aikatan jihar za su dinga yin aiki kwana huɗu a mako.

    Matakin zai bai wa ma’aikatan damar yin aikin kwana ɗaya daga gida, domin inganta aiki da ba su damar samun lokaci ga iyalinsu da kuma samun lokacin noma, kamar yadda sanarwar da gwamnatin Kaduna ta fitar a ranar Litinin ta bayyana.

    Sanarwar ta ce matakin na daga cikin darussan da aka koya lokacin annobar korona da ke buƙatar samun lokacin samun annashawa saɓanin tsohon tsarin da aka saba da shi na aiki.

    Sanarwar ta kuma ce lokacin aiki zai koma daga ƙarfe 8 na safe zuwa 5 na yamma daga Litinin zuwa Juma’a.

    Dukkanin ma’aikatan jihar baya ga makarantu da ma’aikatan lafiya za su yi aiki ne daga gida a ranar Juma’a.

  13. An hana cinikin soyayyiyar fara a cikin jirgin Uganda

    Hukumomin sufurin jiragen sama na Uganda sun haramta sayar da soyayyiyar fara a cikin jirgin ƙasar bayan wani abu da ya faru a ƙarshen mako.

    Farar da ake kira Nsenene ana sayar da ita nega fasinjan jirgin Uganda.

    Wani bidiyo ya nuna wani mutum yana tallar farar a cikin jirgi, kuma hukumomin jirgin sun ce lamarin bai yi wa wasu fasinja daɗi ba.

    Kafofin yada labaran cikin gida sun ce an dakatar da wasu ma’aikatan jirgin saboda abin da ya faru.

  14. An kama matar da ke shirin zuwa Saudiyya aikin Umrah da hodar Iblis a Abuja

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce ta kama wata mata da ke kan hanyar zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Umrah da jikar hodar iblis 80 a filin jirgin sama na Abuja.

    An kama matar da ake zargi mai suna Adisa Afusat Olayinka ƴar asalin jihar Kwara da ke zama a yankin Ibafo na jihar Ogun a ranar Laraba 24 ga watan Nuwamba lokacin da take shirin hawa jirgin Qatar Airways, kamar yadda hukumar NDLEA ta bayyana a sanarwar da ta fitar a ranar Litinin.

    Matar ta ce ta shiga harakar fataucin miyagun ƙwayoyi ne bayan haɗuwa da wata mata a aikin Umrah a shekarar 2019.

    Sai dai a cewar sanarwar matar ta ce ta shiga harakar ne domin haɗa kuɗi naira miliyan bakwai don magance wata matsalar rashin haihuwa duk da ta yi aure tsawon shekara 28 ba haihuwa.

  15. Man Utd ta naɗa Rangnick matsayin sabon koci

    Manchester United ta sanar da naɗa Ralf Rangnick a matsayin kocinta na riƙon ƙwarya zuwa ƙarshen kaka, kafin ya samu biza.

  16. An fara taron jaddada aminci tsakanin China da Afrika a Senegal

    An buɗe taron kwana uku na haɗin kan ƙasashen Afrika da China a Dakar babban birnin Senegal.

    Wakilai daga sassan Afrika da na China ne suka halarci taron tare da ɗaruruwan baƙi.

    Taron na zuwa a daidai lokacin da tattalin arzikin Afrika ke fuskantar koma-baya saboda tasirin annobar korona da sauyin yanayi.

    Ana sa ran taron zai mayar da hankali kan yadda za a yi maganin tasirin annobar korona da kuma wasu sabbin dubaru da za su zama jagora ga inganta hulɗar ɓangarorin biyu cikin shekaru uku masu zuwa.

    A ranar Talata ake sa ran fitar da abin da taron ya cimma.

    Shugaban China Xi Jinping zai jawabi ta bidiyo, a taron wanda ministan harakokin wajen China Wang Yi ke jagoranta a Dakar.

  17. Kotun Botswana ta halatta ƴancin ƴan maɗigo da Luwaɗi

    Kotun ɗaukaka ƙara a Botswana ta tabbatar da hukuncin shekarar 2019 da ya halatta maɗigo da luwaɗi a kasar.

    Alƙalai biyar na kotun sun yanke hukunci baki ɗaya cewa haramta auren jinsi ɗaya ya saɓa wa kundin tsarin mulki na ƴancin ƴan maɗigo da luwaɗi,

    A shekarar 2019,babbar kotun ƙasar ta yi watsi da dokar da ta ce ta saɓawa kundin tsarin mulki wacce ta shafi ɗaurin shekara bakwai ga waɗanda aka kama masu alakar jinsi ɗaya.

    Kotun ta ce ana cutar da ɗan Adam ne idan aka mayar da wasu tsiraru saniyar ware.

    Amma gwamnatin ƙasar ta ɗaukaka ƙara inda ta ce ƴan ƙasar da dama ba su amince da hukuncin ba na shekarar 2019.

    Ƙasashen Afrika da dama sun kyamaci auren jinsi ɗaya.

  18. Gwamnatin Nijar za ta yi bincike kan zanga-zangar ƙin jinin Faransa

    Mahukunta a Jamhuriyar Nijar sun ce za su gudanar da bincike don tantance haƙiƙanin abin da ya faru cikin ƙarshen mako a garin Tera na jihar Tillabery bayan wata zanga-zangar ƙin jinin Faransa ta yi sanadin kashe wasu matasa.

    Masharhanta a ƙasar dai sun ce abin da ke faruwa yana da ban takaici don kuwa zai karkatar da hankulan jami'an tsaro daga yaƙin da suke yi da masu iƙirarin jihadi, waɗanda su ne manyan abokan gaban Nijar.

    Ƙungiyoyin fararen hula dai na ci gaba da kiraye-kirayen a gudanar da zanga-zangar ƙin jinin Faransa, yayin da rahotanni ke ambato Shugaba Mohamed Bazoum na cewa raba tsakanin Nijar da Faransa a wannan mawuyacin lokaci, ba shi ba ne mafita.

    Ku saurari rahoton wakiliyar BBC daga Nijar

  19. NDLEA ta kama buhunhuna maƙare da wiwi a Kano da Legas

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya, NDLEA ta ce ta kama buhunhuna maƙare da tabar wiwi da yawanta ya kai 12,385kg wacce aka shigo da ita ta ruwa a Legas daga maƙwabciyar Najeriya da ba a bayyana ba.

    Sanarwar da kakakin hukumar Femi Babafemi ya fitar ya ce an kama wiwi a gaɓar teku wurin shaƙatawa na Eko Atlantic da ke Victoria Island.

    Sanarwar ta kuma ce an kama wasu da ake zargi manyan masu fataucin ƙwaya Alhaji Bukar Malam Abdu da aka kama da buhunhunan wiwi da nauyinsu ya kai kilo 143 da kuma Bashir Shu’aibu da aka samu da wiwi kilo 466 ɗan asalin Edo mazauni Kano.

    An kuma kama wasu masu fataucin ƙwaya a jihohin Delta da Edo da Borno da Yobe, kamar yadda hukumar ta bayyana.

  20. Sabon nau’in korona na Omicron mai hatsari ya dami duniya

    Ministocin lafiya na kasashe bakwai masu karfin tattalin arziki a duniya da ake kira G7 za su yi wani taro domin samar da matsaya kan sabon nau'in cutar korona na Omicron.

    An fara gano wannan nau'in cutar ne a Afirka ta Kudu ranar Laraba da ta gabata kuma ana ci gaba da samun masu kamuwa da cutar.

    Kasashen France da Switzerland da Canada duk sun tabbatar da bullar cutar a kasashen nasu a ci gaba da gudanar da binciken kimiyya kan wannan nau'i na annoba na Omicron.

    Gwamnatin Najeriya ta ce nau’in cutar bai ɓulla a ƙasar ba kawo yanzu, kamar yadda hukumar da ke ɗakile cutuka masu yaɗuwa ta ce ta ɗauki matakai na ɗakile cutar a ƙasar