'Zinedine Zidane ya nuna cewa ba ya da sha'awar horar da Man Utd'
Yunƙurin Manchester United na ɗauko Zinedine Zidane ya gamu da cikas, inda wasu majiyoyi na kusa da tsohon kocin Real Madrid ya ce ba ya sha'awar zuwa Old Trafford.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.
Awwal Ahmad Janyau and Nasidi Adamu Yahaya
Yunƙurin Manchester United na ɗauko Zinedine Zidane ya gamu da cikas, inda wasu majiyoyi na kusa da tsohon kocin Real Madrid ya ce ba ya sha'awar zuwa Old Trafford.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 57 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar ranar Lahadi.
Mutanen sun haɗar da 30 a jihar Legas, da 9 a Enugu, da 7 a jihar Rivers da ke kudu masu gabashin ƙasar.
Ragowar jihohin sun haɗar da Kaduna mai mutum 3, da Osun mai mutum 3, sai kuma jihohin Abia, da Bauchi, da Kano da Ogun da Plateau da a can kuma aka samu mutane ɗaƴa-ɗaya.
Yanzu dai jumullar waɗanda suka kamu da cutar a Najeriya tun bayan ɓullarta sun kai 213,589, ko da yake an sallami 206,518.
Adadin waɗanda suka rasa rayukansu sanadin cutar kuwa ya kai 2,974.
Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.