Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Hatsarin jirgin ruwa ya kashe 'yan mata bakwai a Jigawa

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Jabir Mustapha Sambo

  1. Sojojin Najeriya 'sun fatattaki' 'yan Boko Haram daga Damboa

    Mazauna garin Damboa na Jihar Borno sun wayi gari cikin murna sakamakon nasarar da sojoji suka yi ta daƙile harin mayaƙa masu iƙirarin jihadi a safiyar yau Juma'a, a cewar rahoton Daily Trust.

    Jaridar ta ruwaito cewa maharan sun afka wa garin da misalin ƙarfe 6:35, inda suka dinga harbi kan mai tsautsayi.

    Fafatawar ta sanya mayaƙan suka fice daga garin bayan minti 30, kamar yadda wata majiyar tsaro ta shaida wa jaridar.

    "Ina tabbatar muku Boko Haram sun kawo hari da safiyar nan amma ba su yi nasara ba a Damboa saboda sojoji sun fatattake su nan take," in ji majiyar.

    A ranar Asabar da ta gabata rundunar sojan Najeriya ta ce ta kashe gwamman mayaƙan ISWAP da suka kai wa sansaninta hari a Askira, sai dai lamarin ya yi sanadiyyar kashe Birgediya Janar Dzarma Zurkushu.

    Wani ɗan banga ya bayyana cewa mayaƙan sa-kai 10 sun ji raunukan harbin bindiga a Kala da ke kusa da Damboa.

  2. Ƙarin mutum 61 sun harbu da korona a Najeriya

    Hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 61 da suka kamu da cutar korona ranar Alhamis.

    Cikin rahoton da ta wallafa, NCDC ta ce mutanen sun fito ne daga a jiha 10, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar .Jihohin su ne:

    • Gombe-16
    • Taraba-15
    • Zamfara-14
    • Abuja-7
    • Kano-2
    • Lagos-2
    • Rivers-2
    • Bauchi-1
    • Delta-1
    • Katsina-1

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 213,464 ne suka harbu da cutar, sannan ta kashe mutum 2,973. Sai dai an sallami 206,292 daga asibitoci bayan sun warke.

  3. Barka

    Maraba da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye.

    Umar Mikail ke cewa mu kasance tare domin samun rahotanni daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.