Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Hatsarin jirgin ruwa ya kashe 'yan mata bakwai a Jigawa

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Jabir Mustapha Sambo

  1. Rufewa

    Masu karatu da haka muka zo karshen shafinmu na kai-tsaye.

    Sai kuma gobe da safe da yardar Allah za mu cigaba da kawo muku labarai da dumi-dumi.

    Sai da safe.

  2. Kotu ta wanke matashin da ya harbe mutum biyu a Amurka

    Kotu ta wanke ba'amurikennan da ya harbe mutum biyu, ya kuma jikkata guda daya a jihar Wisconsin bara.

    Kotu ta ce ta gamsu cewa Kyle Rittenhouse ya yi harbin ne da sunan kare kansa, saboda shima hari aka kai masa.

    Lamarin ya faru ne yayin gudanar da zanga-zangar nuna wariya ta 'racial justice', da aka gudanar a Kenosha a watan Agustan 2020.

    Da farko masu shigar da kara sun ce Kyle mai shekaru 18 ya yi shiga irinta yan banga dauke da makami, kuma yana shirin tada hankalin al'umma, wanda hakan ya sa wasu suka farmasa.

    Sai dai hukuncin kotun ya fusata da dama da suka yi dandazo a bakin kotun don jin yadda za ta kaya.

    A ranar 25 ga watan Agustan 2020 Mr Rittenhouse ya harbe Joseph Rosenbaum da Anthony Huber, ya kuma jikkata Gaige Grosskreutz,wadanda dukansu farar fata ne da ke zaune a Kenosha .

    An baza jami'an tsaro a kan titunan Kenosha don gudun tada tarzomar da ka iya barkewa bayan bayyana hukuncin.

  3. Kevin de Bruyne na Manchester City ya kamu da korona

    Gwaji ya tabbatar da cewa dan wasan tsakiyar Manchester City Kevin de Bruyne ya kamu da cutar korona, bayan ya dawo daga buga wa ƙasarsa Belgium wasa.

    Ɗan wasan mai shekara 30 ya killace kansa na tsawon kwana 10, wanda hakan ke nufin ba zai buga wasan da Manchester City za ta kara da Everton ba a ranar Lahadi, da kuma karawar gasar zakarun Turai da Paris St-Germain.

    De Bruyne wanda aka yi allurar rigakafin korona a baya, ya ci wa Belgium ƙwallo a wasan neman gurbin gasar cin kofin duniya da ƙasarsa ta fafata da Wales a ranar Talata.

    "Muna fatan alamomin ba su yi muni ba," in ji kocinsa Pep Guardiola.

    "Ba za a daɗe ba zai dawo, ba za mu damu da irin girman giɓin da muka samu ba. Yana da muhimmanci sosai. Dole mu taimaka masa kuma muna fatan zai samu sauƙi yayin da ya killace kansa." Inji Guardiola.

  4. Ba zan kori bakin haure daga Belarus ba- Lukashenko

    Daɗɗaɗen shugaban Belarus, Alexander Lukashenko ya shaida wa BBC cewa akwai yiwuwar cewa jami'an tsaron Belarus sun taimaka wa baƙin haure wajen tsallaka iyaka zuwa Poland.

    A wata hira ta musamman da BBC, ya musanta gayyato baƙin hauren zuwa Belarus, a matsayin martani kan takunkumin da Tarrayar Turai ta ƙaƙaba wa ƙasarsa.

    To amma Mista Lukashenko ya ce ba zai kori da bakin hauren da suka shiga ƙasarsa ba.

    Kan batun jerin zanga-zanga da aka gudanar bara gabanin zaben shugaban ƙasa a Belarus, Mista Lukashenko ya yadda cewa an yi wa masu zanga-zanga duka, a wata cibiyar tsare masu laifi da ke Minsk.

    A wata mai kama da haka hukumar da ke sa ido kan haƙƙin bin Adama a Turai ta yi kira ga Poland da ta bai wa ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama da ƴan jarida damar shiga yankinta da ke kan iyakar da Belarus.

    Ta ce halin da baƙin haure ke ciki a iyakar sanadiyyar ayyukan ashha ne da Belarus ta aikata.

  5. Zulum ya kashe wa 'yan gudun hijira naira miliyan 500

    Sama da yan gudun hijira 5,000 ne suka ci gajiyar tallafin gwamnan jihar Borno na naira miliyan 500.

    Sun samu tallafin ne bayan da suka aminta su koma gidajensu a karkashin wani shiri na sake gina rayuwarsu.

    Rikicin Boko Haram ya daidaita rayuwar miliyoyi a yankin Arewa maso Gabas.

    Sanarwar da mai magana da yawun gwamna Babagana Umara Zulum ya fitar, ta ce gwamnan ya isa sansanin 'Bakassi' da sanyin safiyar Juma'a ba zato ba tsammani, inda ya shafe awa bakwai yana raba kayan abinci da kudade.

    Sansanin Bakassi da gwamnatin jihar Borno ta samar na kan titin Maiduguri zuwa Damboa, kuma ya shafe shekara bakwai yana karbar yan gudun hijira mafi yawa daga kananan hukumomin Monguno da Gwoza da Guzmala da Marte.

    Zulum ya kuma jaddada wa yan gudun hijirar cewa " babu wanda za a tilastawa komawa gida matsawar bai natsu da yin hakan ba."

  6. An yi wa Biden allurar bacci, Kamala Harris ta zama shugabar kasa

    Kamala Harris ta zama mace ta farko a tarihin Amurka da ta zama mukaddashiyar shugaban kasar.

    Ta rike mukamin ne na wani an lokaci, yayin da aka yi wa Shugaba Biden allurar bacci don yi masa tiyata.

    Mai taimaka wa shugaban kan harkokin watsa labarai Jen Psaki ta ce Ms Harris na cikin fadar White House a lokacin da da aka yi wa Mista Biden tiyatar, wadda aka saba yi masa duk shekara don duba lafiyarsa.

    Mista Biden wanda zai cika shekara 79 ranar Asabar, shi ne mutum mafi tsufa da ya rike mukamin shugaban Amurka.

  7. Gwamnonin Najeriya na bukatar 'yan sandan jihohi don yakar ta'addanci- Ishaku

    Gwamnan jihar Taraba Darius Ishaku ya ce duka gwamnonin jihohin Najeriya babu wanda ke samun taimakon da ya ke bukata wurin yakar ta'addanci a jiharsa.

    Gwamnan ya fadi haka a shirin gidan talabijin na Channels mai suna 'Politics Today'.

    A cewar gwamnan an gina tsaron kasar ta yadda rawar da gwamnoni ke takawa wurin yakar ta'addanci a jihohinsu ba ta da wani tasirin azo a gani.

    " Ba ni kadai bane ban samun taimako, duka gwamnonin Najeriya na wannan kukan. Hakan yasa mu ke cewa a samar mana da yan sandan jihohi. Inji gwamnan.

    Mista Ishaku na wadannan kalamai ne bayan harin baya bayannan da ake zargin sojojin yankin Ambazoniya na Kamaru sun kai jihar Taraba.

    Rahotanni sun ce sojojin sun dirar wa kauyen Manga da ke karamar hukumar Takum a ranar Laraba, inda suka kashe mutum 11 da suka hada da hakimin kauyen.

  8. An sasanta tsakanin manoman Indiya da gwamnati

    Ƙungiyoyin manoma a Indiya sun yi maraba da matakin gwamnati na soke wasu dokoki uku masu cike da ruɗani, da suka haifar da zanga-zanga tsawon shekara guda.

    Manoman dake cike da murna sun yi sansani a wajen birnin Delhi, suna raba alawa don nuna murna tare da rera wata waƙa mai taken "Allah Ya ja zamanin manoma".

    Sai dai sun ce za su ci gaba da zanga-zanga har sai majalisar dokoki ta soke dokokin a hukumance.

    Matakin soke dokokin da Firanminista Narendra Modi ya ɗauka na zuwa ne gabanin zabukan da za a yi a jihohin Punjab da Uttar Pradesh, da ke da manoma sosai a arewacin ƙasar.

  9. Dole China ta bayyana inda Peng Shuai take- MDD

    Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi kira ga China da ta bayyana inda ƴar wasan Tennis, Peng Shuai take.

    Hukumar Kare Hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya ta buƙaci hukumomi a China su ƙaddamar da sahihin bincike, kan zargin cin zarafi da Mis Peng ta yi kan tsohon mataimakin firimiya Zhang Gaoli.

    An ambato wata jami'ar ƙungiyar Human Rights Watch na cewa "Wannan ba abin da aka saba gani ba ne, saboda ƙungiyoyin ƙasashen waje, ciki har da kwamitin gasar Olympics sun ƙi cewa uffan kan cin zarafin bil Adama da ake yi a China, saboda suna samun kuɗi daga kasar."

    Sai dai Human Rights Watch ta jinjina wa kungiyar yan kwallon tennis mata, bisa jajircewa don sanin inda yar uwarsu take.

    Peng Shuai ta yi kasa ko sama, tun bayan da ta rubuta a shafukan sada zumunta cewa an ci zarafin ta.

    Hukumar mata masu buga Tennis ta yi barazanar janye wasannin ta daga China,ar sai ta samu shaidar cewa Mis Peng na cikin ƙoshin lafiya.

    Kazalika ta bukaci ayi mata alkawarin za a gudanar da bincike kan zarge-zargen da Mis Peng ta yi.

  10. Austria za ta saka dokar kulle don tilasta yin rigakafin korona

    Austria za ta sake sa dokar kulle sannan za ta tilasta ƴan ƙasar yin riga kafin cutar korona, yayin da take ƙoƙarin rage yaduwar cutar da ke ƙara hauhawa.

    Shugaban gwamnatin Austria, Alexander Schallenberg ya ce dokar kullen za ta fara aiki ne ranar Litinin kuma tana iya kai wa kwanaki ashirin.

    Ya ce ba da son ransa za a sake sa dokar ba amma akwai buƙatar yin haka saboda mutane da dama ba su nuna goyon bayansu ba, kuma sun ƙi yin allurar riga kafin.

    Mista Schallenberg ya ce Austria za ta sa dokar tilasatawa ƴan ƙasar yin allurar daga watan Fabrairun shekara mai zuwa.

  11. Zan yi nazari kan buƙatar sakin Nnamdi Kanu - Buhari

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce zai yi nazarin buƙatar da ya kira "mai girman gaske" ta neman ya saki Nnamdi Kanu wadda ƙungiyar dattawan al'ummar Ibo suka gabatar masa.

    Mista Kanu wanda ake zargi da aikata ta'addanci a gaban kotu, na hannun 'yan sandan farin kaya na DSS sakamakon gwagwarmayar da yake yi ta neman kafa ƙasar Biafra a kudancin Najeriya ƙarƙashin ƙungiyar Indigenous People of Biafra (IPOB) da aka haramta.

    Buhari ya bayyana hakan ne yayin da yake karɓar baƙuncin dattawan a fadarsa da ke Abuja ranar Juma'a ƙarƙashin jagorancin tsohon Ministan Sufurin Jirgin Sama Mbazulike Amaechi.

    "Kun nemi abu mai matuƙar girma a wajena a matsayina na shugaban wannan ƙasa. Tasirin buƙatar taku na da girma sosai," a cewar Buhari cikin wata sanarwa da Femi Adesina ya fitar.

    Ya ƙara da cewa buƙatar da dattijan suka nema "ta saɓa wa tanadin tsarin mulki da ya fayyace tsarin shugabanci tsakanin gwamnati da ɓangaren shari'a".

    "Sai dai buƙatar da kuka gabatar mai girma ce sosai amma zan yi nazari a kanta," in ji shi.

  12. Afirka ta Kudu ta gawurta wajen aikata manyan laifuka - Rahoto

    Alƙaluman aikata laifuka na baya-bayan nan da aka fitar na Afirka ta Kudu "abu ne mai muni kamar na baya", a cewar Ministan Harkokin 'Yan Sanda Bheki Cele.

    Kamar yadda shafin Twitter na gwamnati ya bayyana, ministan ya ce bayanan na watan Yuli zuwa Satumba sun nuna cewa Afirka ta Kudu "gawurtacciyar ƙasa ce wajen aikata laifuka".

    A cewarsa, aikata kisan kai ya ƙaru da kashi 21 cikin 100 idan aka kwatanta da irin wannan lokacin na shekarar da ta gabata.

    Game da cin zarafi ta hanyar lalata kuwa, ya ce an yi wa mutum 9,500 fyaɗe cikin wata uku - abin da ke nufin duk awa ɗaya ana aikata fyaɗe sau huɗu. Lamarin ya ƙaru da kashi 7 kenan cikin 100.

    "Wajibi ne a ƙara ƙoƙari wajen tabbatar da cewa an kare rayukan 'yan Afirka ta Kudu," in ji Mista Cele.

  13. 'Yan mata bakwai sun rasu a hatsarin jirgin ruwa a Jigawa

    Rahotanni daga Jihar Jigawa a arewacin Najeriya na cewa wasu ‘yan mata bakwai sun rasa rayukansu bayan da kwale-kwalen da suke tafiya a ciki ya kife ranar Alhamis da dare.

    Lamarin ya faru ne lokacin da suke kokarin tsallaka wani kogi a kan hanyarsu ta dawowa daga taron Maulidi a garin Gasanya.

    Bayanai sun ce jirgin na dauke da mutum 12 ne lokacin da ya kife a cikin kogin wanda ke tsakanin kananan hukumomin Auyo da Kafin Hausa, inda bakwai suka rasu, biyar suka tsallake rijiya da baya.

    Mutanen dai na kan hanyarsu ne ta komawa garinsu na Gafasa da ke aramar Hukumar Kafin Hausa daga Gasanya na karamar hukumar Auyo.

    Malam Mikail Jibril daya ne daga cikin iyayen waanda suka rasu, kuma ya shaida wa BBC Hausa cewa shekarun 'yan matan bai wuce 11 ba zuwa 12.

    Mai garin na Gafasa Alhaji Adamu Abdullahi ya ce tuni aka yi jana'izarsu.

    A watan Mayun wannan shekarar, mutum fiye da 100 sun rasa rayukansu sakamakon irin wannan hatsarin na jirgin ruwa da ya afku kusa da garin Warah na Jihar Kebbi duk a yankin na arewa maso yammacin Najeriya.

  14. Kamfanin Emirates ya sake soke zirga-zirga zuwa Najeriya

    Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Emirates mallakar Daular Larabwa ya sake soke jigilar shiga da fita daga Najeriya har zuwa 30 ga watan Nuwamba.

    Cikin wata sanarwa da ya wallafa, kamfanin ya ce kwastomomin da suka je ko suka bi ta Najeriya cikin kwana 14 da suka wuce ba za a bari su shiga jirginsa ba da zai je Dubai.

    "An soke dukkan tikitin da aka saya," a cewar sanarwar da ya wallafa a shafinsa. An sake dakatar da sufurin ne kwana biyu kacal bayan kamfanin ya sanar da ci gaba da jigilar bayan shafe makonni da dakatarwar.

    A watan Maris Emirates ya sanar da dakatar da zirga-zirga zuwa ƙasar yayin da ake ci gaba da sa--in-sa tsakanin gwamnatin Najeriya da Daular Larabawa game da gwajin cutar korona.

  15. Ghana ta karrama 'yan wasan da suka wakilce ta a wasannin Olympics

    Gwamnatin Ghana ta bai wa 'yan wasan da suka wakilci ƙasar a gasar Olympics ta Tokyo 2020 tukwicin dala 150,000.

    Ministan Matasa da Wasanni Mustapha Ussif ne ya jagoranci bikin ba su kyautukan, inda aka bai wa ɗan wasa ɗaya tilo da ya lashe tagulla, Samuel Takyi, sabuwar mota da kuma dala 10,000.

    Kazalika an ba shi wata dala 20,000 a matsayin gidauniyar cigaban wasanni. Sauran 'yan wasa da kociyoyinsu sun samu dala 5,000 kowannensu.

    Ministan ya gode wa 'yan wasan bisa kishin da suka nuna ta hanyar kafa tarihi a matakin ƙasa da kuma na ƙashin kansu.

  16. An buɗe layukan intanet a Sudan bayan kwana 25

    Hukumomi a Sudan sun buɗe layukan intanet kusan wata ɗaya da rufe su biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya hamɓarar da gwamnatin riƙon ƙwarya.

    An dawo wa da dukkan kamfanonin sadarwa sabis ɗinsu na intanet a ranar Alhamis.

    A ranar 9 ga watan Nuwamba ne kotu ta umarci kamfanonin da su buɗe layukan amma toshewar ba su yi hakan ba.

    Shafin Netblocks mai lura da ayyukan intanet ya tabbatar da dawo da sabis ɗin.

    "An dawo da layukan intanet a Sudan a kwana na 25 bayan toshe su; bayanai sun nuna cewa an samu ƙaruwa a sabis ɗin waya daga ƙarfe 4:30 na yammacin ƙasar; babu tabbas ko sabis ɗin zai ci gaba da zama ko kuma har zuwa yaushe," a cewar Netblocks.

  17. Labaran duniya cikin minti ɗaya

  18. Buhari ya amince a bai wa kowace jiha tallafin naira biliyan 18

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya amince da bai wa jihohin ƙasar 36 tallafin naira biliyan 656.112.

    Bayanan tallafin sun fito ne yayin taron Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa wanda Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo ya jagoranta ranar Alhamis.

    Wata sanarwa daga ofishin Mista Osinbajo ta ce kowace jiha za ta samu naira biliyan 18.225, wanda za ta biya cikin shekara 30 kan kuɗin ruwa kashi 9 cikin 100.

    A cewar fadar shugaban ƙasa, an ɗauki matakin ne saboda a tallafa wa jihohi cimma muradansu na harkokin kuɗi musamman kasafin kuɗaɗensu na shekara.

    Za a raba kuɗin ne a mataki shida cikin wata shida kuma ta hannun Babban Bankin Najeriya (CBN) za a rarraba wa jihohin.

    Tun a watan Yuli ne Ministar Kuɗi Zainab Ahmad ta faɗa wa majalisar cewa za a fara zarar kuɗi daga asusun jihohin domin fara biyan bashin tallafin farko da aka ba su, amma sai jihohin suka nuna turjiya tare da neman wani agajin, abin da ya sa aka ɓullo da agajin kasafin kuɗin kenan.

  19. Nan gaba kaɗan Blinken zai bayyana manufar Amurka a Afirka

    Nan gaba kaɗan Sakataren Harkokin Waje na Amurka Anthony Blinken zai bayyana ƙudirin ƙasarsa kan nahiyar Afirka ƙarƙashin jagorancin gwamnatin Joe Biden.

    Sakataren zai bayyana hakan ne cikin jawabin da zai yi a Abuja yayin da yake kammala ziyarar da yake yi a Najeriya.

    Gwamnatin Donald Trump da ta gabata ta ce babbar manufarta a Afirka ita ce daƙile tasirin China a nahiyar.

    Sai dai masana na ganin gwamnatin Biden za ta fi mayar da hankali kan aiki tare da gwamnatocin nahiyar da kuma yawaita ayyukanta.

    Ana sa ran Mista Blinken zai wuce Senegal bayan kammala jawabin domin kammala ziyarar tasa a Afirka.

  20. Femi Gbajabiamila ya sasanta ASUU da gwamnatin Najeriya

    Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Femi Gbajabiamila ya shiga tsakani a tattaunawa tsakanin gwamnati da ƙungiyar ASUU ta malaman jami'o'i, inda ya sasanta su.

    Zaman sasantawar ya biyo bayan barazanar da ASUU ta yi na sake shiga yajin aiki idan gwamnatin ba ta cika alƙawarin da aka yi a yarjejeniyoyi tsakaninsu ba.

    Yayin zaman wanda ministocin ilimi da na kuɗi suka halarta, ɓangarorin biyu sun amince da abu huɗu kamar haka:

    • Gwamnati za ta biya malaman jami'a naira biliyan 30 cikin mako ɗaya a matsayin kuɗin farfaɗo da jami'o'in
    • Gwamnati za ta fitar da biliyan 22 a matsayin alawus na malaman daga kasafin kuɗin ma'aikatar ilimi
    • Gwamnati ba za ta ƙi yin amfani da tsarin biyan albashi ba na UTAS wanda ASUU ta samar maimakon IPPIS na gwamnati
    • An amince a ganawar cewa yarjejeniyar naira tiriliyan 1,3 da aka cimma a 2009 za ta fara aiki cikin mako ɗaya mai zuwa

    Ministar Kuɗi Zainab Ahmed ta bayyana cewa gwamnati na jiran rahoton kwamatin hukumar cigaban kimiyya da sadarwa ta NITDA kafin aiwatar da matakan da aka cimma.

    "Abin kunya ne a matsayinmu na shugabanni mu zuba ido yayin da abubuwa ke lalacewa," in ji Mista Gbajabiamila.