Majalisar Malaman Indonesia ta haramta kuɗin intanet na crypto
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail
Amurka ta kakabawa rundunar sojin Eritrea takunkumi
Amurka ta kakabawa rundunar sojin kasar Eritrea takunkumi da jam'iyyar kasar mai mulki da kuma wasu jami'ai biyu, inda suke zarginsu da hannu a yakin da ake yi a yankin Tigray na Ethiopia.
Amurkar ta yi Allah wadai da Eritrea saboda yiwa zaman lafiyar kasar Ethiopia makarkashiya, lamarin da ya haddasa wani bala'in da ya shafi bil-adama.
Eritrea dai na goyan bayan gwamnatin Ethiopia akan 'yan tawayen Tigray.
Majalisar Dinkin Duniya ta zargi dukkanin ɓangarorin dake yakin na tsawon shekara guda da aikata manyan laifuka da zasu iya kaiwa laifukan yaƙi.
Wannan rikicin ya raba mutane fiye da miliyan biyu da muhallansu.
Rundunar sojin ruwan Najeriya za ta horar da sojojin Chadi

Asalin hoton, Other
Shugaban rundunar sojin ruwan Najeriya ya ce za su horar da takwarorinsu na Chadi.
Babban hafsan sojin ruwan na Najeriya Vice Admiral Awwal Gambo ya bayyana haka ne lokacin da jekadan Chadi a Najeriya Abakar Chahaimi ya kai ziyara hedikwatar sojin ruwan Najeriya a Abuja, cewar sanarwar da rundunar sojin ta aika wa manema labarai a ranar Juma'a
Vice Admiral Awwal Gambo ya jinjina wa sojojin Chadi kan rawar da suka taka na tabbatar da tsaro a yankin tafkin Chadi da kuma Sahel. Ya kuma ce wannan manufa ɗaya ta ƙasashen na ƙoƙarin tabbatar da tsaro da kare iyakokinsu daga ayyukan ƴan ta’adda.
Majalisar Malaman Indonesia ta haramta kuɗin crypto da tallar kudin a matsayin haja

Asalin hoton, Getty Images
Majalisar malamai ta Indonesia ta yanke hukuncin cewa amfani da kuɗin intanet na crypto a matsayin hanyar ciniki, haramun ne a Musulunci, amma ta ce ana iya kasuwancin ƙadarorin da suka shafi intanet, kamar yadda ɗaya daga cikin shugabanninta ya bayyana.
Indonesia, ƙasa mafi yawan musulmi a duniya, ta haramta amfani da crypto a matsayin kuɗi, amma ta ce ana iya saka hannun jari da kasuwancin kayayyaki na intanet a kasuwar sayar da kayyaki.
A matsayin hanyar biyan kuɗi, an haramta amfani da kuɗin crypto bisa tsarin dokar shari'ar musulunci saboda suna dauke da abubuwa na rashin tabbas da cutarwa, kuma sun saɓa wa dokokin ƙasa, kamar yadda Asrorun Niam Sholeh, shugaban majalisar malaman ta MUI ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Reuters.
Sannan majalisar ta ce tallar kuɗin crypto a matsayin haja haramun ne, inda majalisar malaman ta kamanta kuɗin da caca, saboda bai cika sharuɗɗan shari’ar Musulunci kamar kayayyi da kuma tsabar kuɗi da za a iya gani da sauransu ba.
Amma majalisar ta amince a yi kasuwancin kuɗin ta hanyar da bai saɓa wa shari’a ba.
"Yara miliyan ɗaya na iya mutuwa a Afghanistan kafin ƙarshen 2021"
Hukumar Lafiya ta WHO ta yi gargadin cewa akwai yara miliyan daya da ke fuskantar barazanar mutuwa zuwa karshen shekara a Afghanistan saboda yunwa.
Mai magana da yawun hukumar, Dakta Margaret Harris, ta ce sama da yara miliyan uku aka yi hasashen za su shiga halin yunwa ko tamowa.
Asusun yara na Majalisar Dinkin Duniya, ya ce ya damu matuka da karuwar auren wuri kan yara, yayin da matsanancin talauci da yunwa ke tilastawa iyalai ɗaukar mawuyacin hukunci.
Ya ce ya samu rahotanni da ke tabbatar da cewa iyaye na karbar sadakin yayansu mata jariri da sunan baiko.

Faransa na binciken zargin yi wa wata soja fyade a fadar shugaban ƙasa

Asalin hoton, Getty Images
An ƙaddamar da binciken shari'a kan zargin wani soja da yi wa wata soja mace fyade a fadar shugaban kasa ta Elysee.
An ce lamarin ya faru ne a watan Yuli, bayan wani bikin da shugaba Emmanuel Macron ya halarta.
Wanda ake zargi ya amsa tambayoyi amma zuwa yanzu ba a caje shi ba.
Ofishin Mista Macron ya ce nan take aka ɗauki matakan tallafawa sojan, wadda aka sauya wa wurin aiki.
An kuma ɗauke wanda ake zargi da aikata laifin daga fadar Elysee.
Rwanda ta ɗaure mai sukar gwamnati a shafin YouTube

Asalin hoton, Ishema TV
An yanke hukuncin ɗaurin shekara bakwai kan wani shahararren mai yaɗa bidiyo a shafin YouTube da ke Rwanda kan sukar gwamnati.
Dieudonne Niyonsenga, wanda aka fi sani da Cyuma, an same shi da laifin zamba da basaja da cin mutunci jami’an gwamnati.
Ya musanta zarge-zargen da kuma cewa zai daukaka kara.
Hotunan bidiyonsa na zargin sojoji da aikata munanan cin zarafi a unguwanni masara galihu lokacin kullen korona.
Ko a kwana baya sai da aka yanke hukuncin shekaru 15 kan wani wanda ya yi fice a shafin Youtube da ake zargi da ingiza rikici.
Mahukunta Rwanda na yawaita zargin abokan hamayya da aike su gidan yari kan cacakar gwamnati.
'Yan bindiga sun saci mutane, sun saka wa yankunan Sokoto sabon haraji

Asalin hoton, Daily Trust
Kusan kimanin wata ɗaya bayan 'yan bindiga sun karɓi kudin fansa kimanin Naira miliyan 11 don sako mutum 20 da suka sace a garin Gatawa, 'yan bindiga sun sake komawa garin inda suka saci mutum biyar, a cewar rahoton Premium Times.
Yanzu haka dai yan bindigan na neman kudin fansa kimanin dubu diyar biyar, don sako wanda suka sace din, kamar yadda majiya da yawa daga garin ke fada.
Gatawa da ke Sabon Birni a Ƙaramar Hukumar Sokoto, ya kasance a baya cikin garuruwan da 'yan bindigan ba sa shiga a jahar.
Amma yanzu garin ya zama inda masu kai hare-hare ke addabar mutane.
A harin da aka kai ranar Laraba, wani mazaunin garin wanda ya bukaci a boye sunansa, ya yi faɗa wa jaridar cewa 'yan bindigar ba su kashe ko mutum daya ba, kuɗin fansa kawai suke so su tara.
"'Yan bindigar sun zo ne da safe misalin karfe 8:00 lokacin da mutane ke barin gidajensu kuma suka yi ta harbi a sama kafin su fara kama mutane. Bayan sun gama kama mutanan, sai suka saki baki ɗayan mata amma suka tafi da maza biyar," in ji mutumin.
Bayan tafiyar su ne yan bindigan suka aiko da sakon cewa a haɗa musu kuɗi kimanin 500,000 a matsayin kuɗin fansar wadanda suka sace, kamar yadda majiyar ta ce.
'Yan sandan Najeriya sun tabbatar da mutuwar ɗan jaridar Vanguard

Asalin hoton, Tordue Salem
'Yan sandan Najeriya sun tabbatar da mutuwar ɗan jarida Tordue Henry Salem bayan ya ɓata tun ranar 13 ga watan Oktoba.
Kafin mutuwarsa, Tordue wakilin jaridar Vanguard nr a Majalisar Wakilan Najeriya.
Yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Juma'a, 'yan sanda sun ce mota ce ta bige shi. Kazalika, sun gabatar da wani mutum da ake zargin shi ne direban motar.
Ɓacewar tasa ta jawo koke-koke a ƙasar, abin da ya sa wasu 'yan jarida suka yi zanga-zanga zuwa hedikwatar 'yan sanda da ke Abuja suna neman jami'an tsaro su nemo shi.
An ga gawar tasa ne kwana biyu bayan Majalisar Wakilai ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan ɓatan nasa.
Yanzu haka gawarsa tana mutuware na Babban Asibitin Wuse da ke Abuja.
An gudanar da babban taro kan Libya a Faransa
An gudanar da wani babban taro kan Libya a Faransa, domin tabbatar da cewa na mutunta tsare-tsaren kawo karshen rikicin siyasar kasar.
Daftarin da aka fitar bayan taron ya bukaci dukkanin bangarori su mutunta jadawalin zabukan shugaban kasa da ‘yan majalisa da za a soma gudanarwa a ranar 24 ga watan Disamba.
Daftarin na cewa duk wanda ya yi korafin haifar da cikas ga shirye-shiryen zabuka da mika Mulki na iya fuskantar takunkumin MDD.
Mataimakiyar shugaban kasar Amurka, Kamala Harris na halartar taron a birnin Paris, haka zalika shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi da kuma ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov
Janar Burhan ya sake naɗa kansa shugaban Sudan

Asalin hoton, EPA
Shugaban Sudan wanda ya yi juyin mulki, Abdel Fattah al-Burhan, ya naɗa sabuwar majalisar gudanarwa, inda ya naɗa kansa a matsayin shugabanta, yayin da ya cire fararen hula na tsuhuwar majalisar.
An rantsar da shugaban ne a ranar Alhamis.
Janar Burhan ya ɗora Mohamed Hamdan matsayin mataimakinsa da kuma sauran wasu manyan shugabannin soji a kan mukaman da suka rike kafin juyin mulkin na ranar 25 ga watan Oktoba.
Mambobi 14 na majalisar rikon kwaryar sun haɗa da fararen hula amma babu ko mutum ɗaya daga cikin jama'iyyun siyasa da suka rike mukamai a gwamnatin baya.
Hamɓararren ministan yaɗa labarai na Sudan, Hamza Balloul, ya ce hakan "kara ba da damar cigaba da juyin mulki ne", yana mai cewa mutane "na iya fatali da shi kuma sannan aci gaba da rikon kwarya".
Sabuwar majalisar na zuwa ne daidai lokacin da ake tsaka da korafe-korafen a cikin ƙasar da kuma waje kan haramcin juyin mulkin da kuma toshe layukan intanet.
Bam ya kashe mutane suna Sallar Juma'a a Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images
Wani abin fashewa ya tashi a wani masallaci da ke yankin Spin Ghar a gabashin Afghanistan ana tsaka da Sallar Juma'a, inda ya kashe mutane da dama kuma raunata mutum 12.
Wani jami'in Taliban da ba a bayyana sunansa ba ya faɗa kamfanin labarai na AFP cewa fashewar ta haddasa mutuwa da kuma ji wa mutane rauni.
"Na tabbatar an samu fashewa yayin Sallar Juma'a a cikin masallacin gundumar Spin Ghar," a cewar jami'in.
Mai magana da yawun gwamnati a yankin, Qari Hanif, ya faɗa wa kamfanin labarai na AP cewa da alama a cikin masallacin aka dasa bam ɗin.
Ya zuwa yanzu babu ƙungiyar da ta ɗauki alhakin kai harin amma ƙungiyar ISKP ta sha kai hare-haren bam tun bayan da Taliban ta ƙwace mulkin ƙasar.
Masu fasa ƙwauri ne ke jawo tashin farashin shinkafa - Ministar kuɗi ta Najeriya

Asalin hoton, Getty Images
Ministar Kuɗi ta Najeriya Zainab Ahmed ta ce masu fasa ƙwauri ko kuma sumoga ne ke jawo tashin farashin shinkafa a kasuwannin ƙasar.
Da take magana a shirin Politics Today na Channels TV ranar Alhamis, ministar ta ce 'yan sumoga ne ke cutar da 'yan ƙasa ta hanyar shigo da kayan da ba su da inganci.
"Kwarai da gaske akwai matsaloli kuma suna tasowa ne saboda fasa ƙwaurin kayayyaki zuwa cikin ƙasa," in ji ta.
"Akwai 'yan ƙasa marasa kishi da ke shigo da shinkafa maras inganci, wata ma bai kamata ɗan Adam ya ci ba, amma haka za su kawo ta kasuwa."
Ministar ta jaddada cewa akwai rundunonin haɗin gwiwa da gwamnati ta samar don yaƙi da fasa ƙwauri "da kuma daƙile ayyukan masu kawo wa tattalin arzikin ƙasa cikas".
Gwamnatin Najeriya ta haramta shigar da shinkafa ƙasar daga ƙasashen waje da zummar haɓaka nomanta a ƙasar.
Ƙasashen duniya na taron ceto Libya

Asalin hoton, Reuters
A yau Juma'a Faransa ke gudanar da wani taron ƙasa da ƙasa da nufin tabbatar da Libya ta tsaya kan shirin gudanar da zaɓe a watan Disamba.
Ana kuma sa ran manyan ƙasashen duniya za su amince da yunkurin da ake na kawar da dakarun kasashen waje daga kasar.
Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris za ta halarci tattaunawar da za a yi a birnin Paris, da Shugaban Masar Abdel Fattah al-Sisi, da Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergei Lavrov.
Taron na zuwa ne daidai lokacin da rikicin siyasa ke kara kamari a Libya, wanda masu lura da al'amura ke cewa na yin barazana ga shirin samar da zaman lafiya a kasar.
Kotun soja ta ɗaure ɗan jaridar Amurka a Myanmar

Asalin hoton, Reuters
Wata kotun soja a Myanmar ta ɗaure ɗan jaridar Amurka, Danny Fenster, shekara 11 a gidan yari.
Kotun ta kama Mista Fenster da laifin karya dokar shige da fice da shirya taro ba bisa ƙa'ida ba da kuma haddasa ƙiyayya a kan gwamnatin sojan ƙasar.
A farkon makon nan ne aka sake gabatar da tuhuma biyu a kansa da suka haɗa da ƙoƙarin raba ƙasa da kuma ta'addanci, waɗanda ka iya janyowa a yi wa mutum ɗaurin rai-da-rai.
Za a fara yi masa shari'a ranar 16 ga Nuwamba kan sabbin tuhume-tuhumen.
A watan Mayu aka tsare Fenster mai shekara 37 a filin jirgin sama na Yangon.
Shi ne mamallakin shafin jaridar intanet ta Frontier Myanmar kuma yana cikin gomman 'yan jaridar da aka tsare tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a watan Fabarairu.
Buhari zai gana da sakataren harkokin wajen Amurka kan makamashi

Asalin hoton, State House
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Antony Blinken zai kai ziyara ƙasashen Najeriya da Kenya daga 15 zuwa 20 ga watan Nuwamba.
Ofishin Harkokin Wajen Amurka ya ce Mista Blinken zai gana da Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, inda za su tattauna kan makamashi da harkokin lafiya da dimokuraɗiyya.
Kazalika idan ya je Kenya, Blinken zai tattauna da Shugaba Uhuru Kenyatta game da annobar korona da kuma matsalolin tsaro a maƙotanta kamar Ethiophia da Sumaliya da Sudan.
A Dakar babban birnin Senegal, Shugaba Macky Sall "zai jaddada ƙawancen ƙasashenmu biyu," in ji ofishin cikin wata sanarwa.
EFCC ta kama Lucky Igbinedion tsohon gwamnan Jihar Edo

Asalin hoton, Other
Hukumar yaƙi da rashawa a Najeriya, Economic and Financial Crimes Commission (EFCC), ta tabbatar da kama tsohon Gwamnan Jihar Edo Lucky Igbinedion kan zargin cin hanci.
Mai magana da yawun hukumar, Wilson Uwajuren, ya faɗa wa BBC Pidgin cewa Mista Igbinedion ya je ofishinsu na Abuja domin amsa tambayoyi game da ɓatan kuɗi naira biliyan 1.6.
Rahotanni na cewa gwamnatin Edo ce ta karɓi rancen kuɗin ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan amma sai aka gan su a asusun wani kamfani da yake da hannu a ciki.
A 2008 ma, gwamnan wanda ya yi mulki daga 1999 zuwa 2007 ya fuskanci tuhuma daga EFCC, inda har aka ɗaure shi wata shida a gidan yari bayan ya amsa aikata laifi ɗaya daga cikin 191 kan ɓatan naira biliyan 2.9.
Muna tafe da ƙarin bayani da zarar mun samu...
Yau ce ranar ƙarshe a taron sauyin yanayi

Asalin hoton, Getty Images
Yau Juma'a ce rana ta ƙarshe a taron ƙoli kan sauyin yanayi na duniya da ke gudana a Glasgow babban birnin Scotland, inda manazarta ke ganin babu alamar cimma matsaya ta fuskar taƙaita fitar da hayaki mai gurɓata muhallli.
Shugaban taron na Cop26, Alok Sharma, ya yi gargaɗin cewa har yanzu akwai babban ƙalubale a gaba.
Wakilin BBC ya ce akwai kuma ƙarin wasu batutuwan da ake kai ruwa rana a kansu, kamar dagewar kasashe masu tasowa kan lallai kasashe masu arziki su cika alkawarin ba su dala biliyan 100 da suka yi domin ɗaukar matakan yaki da matsalar ta sauyin yanayi.
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP cewa ba shi da kwarin gwiwar za a cimma kwakkwarar matsaya.
Korona ta kashe ƙarin mutum 11 a Najeriya
Hukumar NCDC da ke yaƙi da cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 53 ɗauke da cutar korona ranar Alhamis.
Kazalika, cutar ta kashe ƙarin mutum 11, abin da ya sa jumillar adadinsu ya zama 2,933.
Mutanen da cutar ta kama sun fito ne daga jiha tara, ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.
Jihohin su ne:
- PLagos-19
- Abuja-7
- Plateau-7
- Rivers-7
- Imo-5
- Kano-4
- Zamfara-2
- Bayelsa-1
- Gombe-1
Ya zuwa yanzu jumillar mutum 212,947 ne aka tabbatar sun harbu da cutar a Najeriya, sannan ta kashe. Sai kuma 205,000 da aka sallama daga asibiti bayan sun warke.
Maraba
Barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye na Juma'atu - babbar rana.
Umar Mikail ke cewa ku biyo mu domin samun rahotanni daga sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.
