APGA ta lashe ƙaramar hukumar Anambra ta gabas
APC – 2,034
APGA – 9,746
PDP – 1,380
YPP – 559
Yanzu ƙananan hukumomi shida APGA ta lashe cikin 21 da aka sanar kawo yanzu.
Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya
Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail
APC – 2,034
APGA – 9,746
PDP – 1,380
YPP – 559
Yanzu ƙananan hukumomi shida APGA ta lashe cikin 21 da aka sanar kawo yanzu.
APC – 2,085
APGA – 6,911
PDP – 5,108
YPP – 868
Yanzu ƙananan hukumomi biyar APGA ta lashe cikin 21 da aka sanar kawo yanzu.
Sakamakon da hukumar zaɓe ta Inec ta sanar kawo yanzu ya nuna ɗan takarar jam’iyyar APGA Charles Soludo ne ke kan gaba inda ya lashe ƙananan hukumomi huɗu
Sakamakon ƙaramar hukumar Ayamelum
APC – 2,409
APGA – 3,424
PDP – 2,804
YPP – 407
Sakamakon ƙaramar hukumar Oyi
APC – 2,830
APGA – 6,133
PDP – 2,484
YPP – 900
Sakamakon ƙaramar hukumar Awka ta kudu
APC – 2,595
APGA – 12,891
PDP – 5,498
YPP – 919
Sakamakon ƙaramar hukumar Dunukofia
APC – 1,991
APGA – 4,124
PDP – 1,680
YPP – 1,360
Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta sake shigar da ƙara inda ta nemi kotu ta hana wa shugaba Buharikashe naira biliyan 26 da aka ware masa na tafiye tafiye da abinci da kula da harakokin ofishinsa.
SERAP ta ce ta shigar da ƙarar ne a babbar kotun Abuja a ranar Juma’a, tana mai cewa “bai dace da buƙatun al’umma ba a fifita tafiye tafiye da abinci yayin da kuma aka ware naira biliyan 19.17 kawai don ayyukan asibitocin koyarwa guda 14.”
“Kuɗirin kashe naira biliyan 26 rashin adalci ne ga talakawan Najeriya kuma wani nauyi ne ga masu tasowa,” in ji SERAP.
SERAP ta sha kai gwamnatin Najeriya ƙara kan batutuwa da dama amma har yanzu babu shari’a ɗaya da aka yanke.
Wasu fitattun ƴan jihar Gombe da ke arewa maso gabashin Najeriya sun yi kira ga gwamna Inuwa Yahaya da Sanata Danjuma Goje da su sasanta rikicin da ke tsakaninsu.
Sun yi kiran ne kwanaki kaɗan bayan an yi hatsaniya a jihar ta Gombe tsakanin ɓangaren gwamnan da na Sanatan yayin da Goje ke kai ziyara jihar.
Hatsaniyar — wadda kowane ɓangare ya zargi ɗaya bangaren da haddasawa— ta yi sanadin mutuwar akalla mutum biyar.
Sai dai a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, fitaccen ɗan jihar ta Gombe Alhaji Muhammad Jibrin Barde, ya yi kira ga ɓangarorin da ma mazauna jihar su guji tayar da hankali yana mai cewa hakan zai sa jihar ta fuskanci koma-baya.
A cewarsa, kodayake hatsaniyar ba ta zo da mamaki ba ganin yadda aka daɗe ana takun-saka tsakanin ɓangarorin biyu, akwai buƙatar dukkansu su mayar da wuƙa kube domin ci gaban jihar.
Alhaji Barde ya ƙara da cewa bai kamata mulkin dimokuradiyya ya zama abin ko a mutu ko a yi rai ba yana mai cewa ya kamata shugabanni su ba da muhimmanci wajen bauta wa jama’a ba rikici a tsakaninsu ba.
Shugaban Nijar Mohamed Bazoum ya kai ziyara garin Banibangou yankin Tillaberi domin jajantawa al’ummar yankin.
A ranar Alhamis gwamnatin Nijar ta ayyana zaman makoki na kwana biyu domin jimamin kashe mutum 69 a harin da mayaƙa masu iƙirarin jihadi suka kai a Banibangou da ke kusa da kan iyaka da Mali.
Bazoum ya ce ziyara ce da ta zama dole gare shi bisa abin da ya faru.
"Aiki na ne a lokaci irin wannan na zo da kaina na taya ku jaje,” kamar yadda shugaban ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
Shugaban ya ce ya kai ziyarar ne a madadin al’ummar Nijar tare da yi wa al’ummar yankin alƙawalin cewa gwamnati za ta yi ƙoƙarin gano bakin zaren magance matsalolin tsaro a yankunan da ke kan iyaka.
Yankin da ke kan iyaka da Nijar da Mali da Burkina Faso ya sha fuskantar hare-hare daga mayaƙan da ke da alaƙa da ƙungiyoyin IS da kumna Al Qaeda.
Ƴan takara daga manyan jam’iyyun siyasa a zaɓen gwamnan Anambra sun yi nasara a mazaɓunsu.
Manyan ƴan takarar sun haɗa da ɗan takarar jam’iyyar APGA da ke mulki a jihar Chukuma Soludo da Andy Uba na jam’iyyar APC da kuma Valentine Ozigbo na jam’iyyar PDP.
Duk da samun tsaiku kafin ya kaɗa ƙuri’arsa saboda matsalar na’ura, amma Soludo ya kawo rumfarsa mai lamba 13 a gundumar Isuafia inda ya ba sauran abokan takararsa rata da ƙuri’u 126.
Ɗan takarar PDP ma ya rumfarsa mai lamba 005 a ƙaramar hukumar Aguata inda ya samu yawan ƙuria 75.
Ɗan takarar APC ya samu yawan ƙuri’u 80 a mazaɓarsa ta makarantar cocin Saint Peter mai lamba 16, inda ya ba sauran abokan takararsa tazara.
Hukumar zaɓe mai zaman kanta a Najeriya Inec ta ce an samu matsaloli da suka kawo cikas ga harkokin zaɓen gwamnan jihar Anambra.
Hukumar ta kuma amince da cewa wasu na’urorin tantance masu zaɓe sun samu matsala yayin da ta kasa tura jami’anta a wasu wuraren, kamar yadda shugaban hukumar a Anambra Nkwachukwu Orji ya shaida wa manema labarai.
Ya ce hukumar za ta yi amfani da dokoki da tsarinta na karɓar sakamakon zaɓe.
Shugaban hukumar ya ce inda aka samu matsala za a iya tattara sakamakon a cibiyoyin tattara sakamako na ƙananan hukumomi.
Saudiyya ta yi Allah wadai da harin da aka kai wa Firaministan Iraƙi da safiyar Lahadi, inda ta bayyana harin da na ta’addanci, kamar yadda ma’aikatar harakokin wajen Saudiyya ta bayyana.
An kai wa Mustafa Al-Kadhimi hari ne a gidansa a Baghdad ta hanyar amfani da ƙaramin jirgi mara matuƙi da aka ɗora wa ababen fashewa. Amma ya tsallake rijiya da baya.
Rundunar sojin Iraki ta ce an yi yunƙurin halaka Firaministan ne.
Babu dai wata ƙungiya da ta fito ta yi iƙirarin ɗaukar alhakin kai harin.
Ana sa ran hukumar zaɓe mai zaman kanta Inec za ta fara bayyana sakamakon zaɓen gwamnan Anambra da aka gudanar a ranar Asabar.
Misalin ƙarfe 10:00 na safiyar Lahadi ne hukumar ta ce za ta fara bayyana sakamakon.
Rahotanni sun ce Chukwuma Soludo ɗan takarar jam’iyyar APGA da ke mulki a jihar ne kan gaba a ƙaramar hukumar Awka ta kudu. Sai dai Inec ba ta bayyana sakamakon ba a hukumance.
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 116 sun kamu da korona a ƙasar a ranar Asabar.
Cutar ta kashe ƙarin mutum uku a ranar Asabar
Alƙalumman sun nuna jihar Imo ce ta fi yawan waɗanda suka kamu a ranar Asabar da mutum 53.
Sai jihar Filato inda aka samu ƙarin mutum 30. A Abuja an samu mutum 10.
Ga jerin jihohin da aka samu ƙarin masu korona a Najeriya
Imo-53
Plateau-30
FCT-10
Kano-9
Kaduna-8
Lagos-3
Rivers-3
Jimillar mutum 212,627 yanzu korona ta shafa a Najeriya amma 204,249 sun warke.
Cutar kuma ta kashe jimillar mutum 2,905 a Najeriya
Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.