Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mutum uku ne suka mutu a ruftawar gini hawa 25 a Legas - 'Yan sanda

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Jabir Mustapha Sambo

  1. Buhari ya isa birnin Glasgow lafiya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya isa birnin Glasgow na Scotland lafiya domin taron sauyin yanayi.

    Shugaban zai hadu da shugabanni sama da 120 da za su halarci taron

    Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya aike wa manema, ta ce sai a ranar Talata Buhari zai gabatar da nasa jawabin a wurin taron sannan kuma zai bayyana irin matakan da ƙasarsa ke ɗauka wajen rage ɗumamar yanayi.

    Ana sa ran shugaban zai gana da shugaban Amurka Joe Biden da kuma na Faransa Emmanuel Macron.

    Taron sauyin yanayin da aka yi wa lakabi da COP 26, taro ne da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya domin duba inda aka kwana bayan taron Paris da aka gudanar a shekarar 2015.

  2. An buɗe wasu kasuwannin mako a Zamfara

    Gwamnatin Zamfara ta sanar da buɗe wasu kasuwannin mako a jihar bayan rufe kasuwannin fiye da wata biyu a wani mataki da aka ɗauka na magance matsalar ƴan bindiga da suka addabi jihar.

    Cikin wata sanarwa, kwamishinan watsa labaran jihar Ibrahim Dosara ya ce gwamnati ta yanke shawarar buɗe kasuwannin ne saboda sauƙin da aka samu na matsalolin tsaro da kuma ƙorafe-ƙorafen jama’a.

    Kasuwannin da aka buɗe sun haɗa da kasuwar Nasarawar Burkullu da kasuwar Gusau da Shinkafi da Kasuwar Daji da ta Dan Jibga.

    Sai dai matakin buɗe kasuwannin bai shafi kasuwar dabbobi ba.

    Gwamnatin Zamfara ta bayyana wasu dokoki na cin kasuwar da ta ce duk aka saɓa za ta rufe kasuwannin.

    Dokokin sun haɗa da haramta wa mutane shiga kasuwa da bindiga da kuma yin barazana ga wani da sunan wata ƙungiya ko hukuma.

  3. Algeria ta dakatar da ba Morocco gas

    Fadar shugaban Algeria ta ce ƙasar ta dakatar da ba makwabbiyarta Morocco gas saboda tsamin dangantaka tsakanin ƙasashen biyu.

    Sanarwar da fadar shugaban kasar ta fitar ta ce, "Saboda wasu halayen Morocco da ke cin karo da muradun Algeria da hadin kai, ƙasar ya umarci kamfanin mai na Sonatrach da ya yanke huldar kasuwanci da kamfanin samar da wutar lantarki na Morroco ONEE".

    Algeriya na shigar da gas ne Morocco ta hanyar bututun da ya ratsa Spain, inda gwamnatin Rabat ke biyan wasu kuɗaɗe.

    Morocco kuma na amfani da wani kaso na gas ɗin domin samun makamashin lantarki.

    Algeriya kuma yanzu ta ƙi sabunta yarjejeniyar wacce ta kawo ƙarshe a ranar Lahadi.

    Amma za ta ci gaba da ba Spain gas ta hanyar bututun Medgaz.

    Dangantaka ta yi tsami tsakanin ƙasashen biyu kan batututwa da dama inda Algeriya ta katse duk wata hulɗar diflomasiya tare da haramtawa jiragen Morocco ratsawa ta sararin samaniyarta.

    Algeria na zargin Morocco ne da goyon bayan ƴan a ware da kuma leƙen asiri ta hanyar yin amfani da fasahar Isra’ila.

  4. Sauyin yanayi: A biya mu ko kuma mu mutu tare - Chakwera

    Shugaban ƙasar Malawi, Lazarus Chakwera ya aika wani saƙo mai ƙarfi ga ƙasashe masu ci gaban tattalin arziƙi game da buƙatar su riƙa biyan ƙasashe matalauta fam biliyan 100 duk shekara don yaƙi da tasirin sauyin yanayi.

    Ya shaida wa BBC cewa ba zai ji tsoron faɗa wa shugabannin duniya a taron sauyin yanayi da ake kira COP26 cewa "Ba aikin agaji ba ne. Don haka ku biya ko kuma duk mu halaka tare."

    Tun a 2009, manyan ƙasashen duniya suka yi alƙawalin tara kuɗaɗen zuwa 2020 domin biyan ƙananan ƙasashe a matsayin diyyar tasirin sauyin yanayi.

    Amma har yanzu ba cimma buƙatar ba, kuma gwamnatin Birtaniya da ke ɗaukar nauyin taron ta ce da wahala ta cimma buƙatar zuwa 2023.

    Ga ƙasashe da dama, wannan babban batu da ke kan tebur – kuma ƙananan ƙasashe sun tafi Glascow ne da fatan biyan wannan buƙatar.

    Chakwara ya ce: “idan muka ce ku cika alƙawali, ba wai muna nufin agaji ba ne, batu ne na biyan ɓarnar da aka yi.

  5. Shugabannin duniya na taro kan yadda za su tunkari bala’in dumamar yanayi

    Shugabannin kasashen duniya za su fuskanci matsin lambar daukar matakin gaggawa, domin magance bala'in sauyin yanayi.

    Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da birnin Glasgow na Scotland ya dauki harami, domin bude taron koli kan sauyin yanayi da Majalisar Dinkin Duniya za tajagoranta.

    Shugaban Amurka Joe Biden da takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari na cikin shugabannin kasashe 120 da za su halarci taron da zai dauki makwanni biyu ana yi.

    Shugaba Joe Biden na Amurkaya ce ga Amurka ya zama wajibi a ga sauyi

    Ya ce batun komawa amfani da makamashin da baya gurbata muhalli ta hanyar daina amfani da mai ko iskar gas ko sinadari zai taimaka wajen rage dumamar yanayin.

    Ana sa ran shugaban China Xi Jinping zai yi jawabi ne kawai ta hanyar karanta sanarwa a wajen taron.

  6. Korona ta kama mutum biyar a Kano

    Hukumar NCDC da ke ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 74 da suka kamu da korona a ranar Lahadi.

    Benue ne inda cutar ta fi kama mutane a ranar Lahadi inda alƙalumman suka bayyana ƙarin mutum 49 da suka kamu da cutar.

    Cutar ta kuma kama ƙarin mutum 6 a Enugu da Osun.

    Mutum 5 suka kamu a Kano

    Alƙalumman sun ce ba a samu wanda ya kamu da korona ba a Legas inda cutar ta fi bazuwa a Najeriya a ranar Lahadi

    Amma an samu ƙarin mutum biyu da cutar ta kama a jihar Abuja birnin tarayyar Najeriya.

  7. Maraba

    Muna maku maraba da kasancewa da mu a wannan shafin da muke kawo labarai da rahotanni kai tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.