Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mutum uku ne suka mutu a ruftawar gini hawa 25 a Legas - 'Yan sanda

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Jabir Mustapha Sambo

  1. Rufewa

    Masu karatu anan muka kawo karshen labaran da muke kawo muku na daren yau.

    Sai kuma gobe idan Allah Ya kaimu.

    Mu kwana lafiya.

  2. Ana rububin yin rajistar zabe a jihar Kano

    A Najeriya gwamnatin jihar Kano da ke arewacin kasar ta ce ana samun karuwar masu rajistar zabe a jihar sakamakon fahimtar da al`umma ke yi game da muhimmancin zabe.

    Gwamnatin jihar Kanon ta kafa wani kwamiti na musamman wanda ya shiga shelar wayar da kan al`umma, bayan ta gano cewa mutane da dama na dari-dari da yin rajistar zabe.

    An kafa kwamitin wayar da kan masu zabe ne a jihar bayan rahotanni sun nuna cewa a jihohi da dama a Najeriya ciki har da Kanon, akwai tarin katunan zabe jibge a ofisoshin hukumar zabe, wadanda ke neman yin kwantai saboda masu katunan basu je sun karba ba.

    Hakama akwai wadanda katunan su suka bata, ko suka lalace, da kuma wadanda suka cancanci kada kuri`a masu yawan gaske da basu je an yi musu rajistar ba.

    A cewar mataimakin shugaban kwamitin kuma kwamishinan raya karkara Alhaji Musa Iliyasu Kwankwaso, babban burin gwamnati dai shi ne kare matsayin jihar Kanon na rumbun kuri`a.

    Ya kara da cewa " abunda suke gani a zahiri na nuna cewa kwalliya na biyan kudin sabulu ".

    A babban zaben 2019 jihar Kano ce tazo ta biyu wajen yawan masu kada kuri`a a fadin Najeriya da mutum sama da miliyan biyar, inda ta zo bayan jihar Legas mai mutum fiye da miliyan shida.

  3. Adadin wadanda Korona ta kashe a duniya ya zarta mutum miliyan biyar

    Masu bincike a Amurka sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon annobar korona a duniya sun zarta miliyan biyar.

    Alkaluman da jami’ar Johns Hopkins ta wallafa a shafinta ya tattaro bayanai daga sassan duniya na adadin mutanen da suka kamu, da ma wadanda suka mutu sanadin kamuwa da cutar.

    A cewar rahoton Amurka ke kan gaba da yawan mutanen da annobar ta kashe da kusan mutum 750,000.

    Sai Brazili mai mutum 600,000, sai kuma Indiya da ke ta uku da 450,000.

  4. Kawar da dumamar yanayi zai bunkasa tattalin arzikin duniya- Biden

    Shugaba Joe Biden na Amurka ya shaidawa taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Scotland cewa yaƙi da matsalolin dumamar yanayi abu ne mai matukar muhimmanci, da zai bada damar bunkasar tattalin arziki.

    Ya kara da cewa kirkirar fasahar rage gurbatacciyar iskar da ake fitarwa zai samar da miliyoyin ayyuka a Amurka da sauran sassan duniya.

    Daga nan kuma Mista Biden ya bukaci sauran kasashe su shiga tsarin da Amurka ta kaddamar da Tarayyar Turai, domin rage amfani da makamashi da ke gurbata muhalli da kashi 30 cikin 100.

    " Mu yi alkawarin rage makamashin Methane a duniya, a dunkule mu rage gurbataccen sinadarin Methane da ake fitarwa da kashi 30 cikin 100 nan da shekara 10." Inji Biden

    A lokacin bude taron a Glasgow, Firaminista Boris Johnson na Burtaniya ya gargadi shugabannin duniya cewa masu tasowa nan gaba ba za su taba yafe musu ba, idan har suka gaza wajen shawo kan matsalolin dumamar yanayi.

  5. Mutum uku ne suka mutu a ruftawar gini hawa 25 a Legas - 'Yan sanda

    Ƴan sanda sun tabbatar da mutuwar mutum uku da kuma ceto mutum shida sakamakon rushewar wani gini a jihar Legas da ke kudu maso yammacin Najeriya.

    A yau Litinin da rana ne ginin mai hawa 25 wanda ake kan aikin gininsa ya rushe inda lamarin ya rutsa da mutane da dama.

    Wasu da lamarin ya faru a kan idonsu sun shaida wa BBC cewa mutane da dama ne ke cikin ginin da suka haɗa da ma'aikata da ƴan kwangila a lokacin da abin ya faru.

    Zuwa yanzu an yi amannar kusan mutum 100 ne lamarin ya rutsa da su.

    Tuni aka kai kayayyakin aikin ceto wajen da na gano ko akwai masu rai a ƙarƙashin ɓaraguzan.

  6. Shugaban Turkiyya, Recep Tayyib Erdogan ya fasa halartar taron sauyn yanayi na duniya da ake gudanarwa a Glasgow, saboda rashin jituwa kan wasu tsare-tsare tsaro.

    Mista Erdogan ya ce ya yanke hukuncin fasa halartar taron, bayan masu shirya taro a Scotland sun ƙi aminta da sharuɗɗansa – da ke da alaƙa da yawan tawagarsa.

    Ya ce, batun ya wuce na tsaron tawagarsa, batu ne da ya shafi mutuncin Turkiyya, wanda ba zai aminta a ƙasƙantar ko nuna rashin darajawa ga kasar a idon duniya ba.

  7. An yanke hukuncin kisa ga mutumin da ya kashe 'yan jarida biyua Iraki

    Wata kotu a Iraki ta yanke wa wani mutum hukuncin kisa, bayan kama shi da laifin kashe wasu yan jarida biyu da ke aiki a wata kafar yada labaran cikin gida mai sukar gwamnati.

    Kotun da ke Basra ta kama mutumin da laifin kisan Ahmed Abdul-Samad da Safaa Ghali, a lokacin da suke daukar zanga-zangar kin jinin gwamnati a Kudancin Basra.

    Kotun ta ce ta yanke ma mutumin hukuncin kisa bisa tsarin doka ta sha uku a kundin tsarin mulki na 2015, da ya yi magana kan aikata ta'addanci.

    'Yan jarida da masu fafutuka a kafafen sada zumunta na fuskantar hare hare irin wadannan a Iraki, da ake dora alhakin su akan masu goyon bayan gwamnati.

  8. Gwamnatin mulkin soja mafi lalacewa ta fi gwamnatin Buhari ta APC- Ortom

    Gwamnan jihar Binuwai a yankin tsakiyar Najeriya Samuel Ortom, a ranar Litinin ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari.

    Gwamna Ortom ya ce gwamnatin mulkin soja mafi muni da aka taɓa yi a ƙasar nan ta fi gwamnatin APC mai mulkin ƙasar yanzu.

    Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya faɗi hakan ne a wani taron manema labarai jim kaɗan bayan komawarsa Binuwai ɗin daga taron jam'iyyar PDP da aka yi a Abuja.

    Ya ce sakamakon taron jam'iyyar tasa ya nuna ƙarara cewa PDP ta shirya don karɓar mulkin ƙasar nan a 2023, yana mai zargin cewa wannan gwamnatin ta gaza a duk al'amuranta.

    "Sun yi nasara wajen lalata tattalin arzikinmu da tsaronmu da harkokin rayuwarmu da ma duk wani abu da ya shafi ƙsar nan.

    "Na karanta tarihin Najeriya da na waɗanda suka lalata mu ciki har da mulkin soji. Yawanci mukan ce gwamnatin farar hula mafi taɓarɓarewa ta fi gwamnatin mulkin soji.

    "Amma a gaskiya gwamnatin mulkin soji mafi lalacewa ta fi gwamnatin APC da ke mulki a yanzu," in ji Gwamna Ortom.

  9. Yan sanda sun kama shugaban majalisar dokokin Filato da aka tsige

    Rahotanni daga jihar Filaton Najeriya na cewa jami'an tsaro sun kama shugaban majalisar dokoki da aka tsige Alhamsi din da ta gabata, da kuma wasu yan majalisa 10 da ke goyon bayansa.

    Jaridun cikin gida sun ruwaito cewa yan sanda sun isa zauren majalisar da misalin karfe 3:15 na rana, kuma ba tare da wata-wata ba suka yi awon gaba da honorabul Abok Ayuba da yan koren nasa su 10.

    Wasu rahotannin sun ce jami'an tsaro sun bade masu bore a harabar majalisar dokokin da hayaki mai sa hawaye.

    An ambato dan majalisa mai wakiltar Langtang ta Kudu Honorabul Zinghtin Sohchang yana fada wa yan jarida cewa "gamu nan jami'an tsaro sun tura mu cikin mota kirar Hilux kuma bamu san ina za a je damu ba."

    A makon da ya gabata ne yan majalisar dokokin jihar Filato suka tsige shugaban majalisar Abok Ayuba, wanda aka dade ana hasashen cewa basa ga maciji da gwamna Simon Lalong.

  10. Labarai da dumi-dumi, Gini mai hawa 25 ya rufta kan mutane a Lagos

    Wani gini mai hawa 25 da ake aikin gininsa a birnin Ikkon jihar Legas a Najeriya ya rushe tare da binne mutane.

    Lamarin ya faru ne a yau Litinin a unguwar Ikoyi kamar yadda jami'an hukumar aikin ceto suka sanar.

    Har yanzu babu tabbas kan yawan mutanen da ginin ya ruftawa, amma ma'aikata da maƙwabtan da ke yankin suna ta ƙoƙarin tono mutane daga cikin ɓaraguzan.

  11. An kama gungun masu safarar ƙwaya a kan iyakar Nijar da Najeriya

    Hukumar yaƙi da fatauci da shan miyagun ƙwayoyi ta Jamhuriyar Nijar OCRITIS, ta ce ta kama mugayen ƙwayoyi a wani yanki na jihar Damagaram da ke kan iyaka da Najeriya.

    OCRITIS ta bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da ta yi a yau Litinin a Yamai.

    Hukumar ta gabatar wa manema labarai wasu mutum uku ne dukkan su ƴan Nijar a matsayin wadanda aka kama da sama da kilo 100 na tabar wiwi, da kuɗi da wayoyin hannu damota da sauransu.

    Hukumar Ocritis ta ce ta yi nasarar bankaɗo wannan gungun na ƙasa da ƙasada ya shahara wajen fataucin miyagun ƙwayoyin bisa ƙwarewa da kuma jajircewar jami’anta.

    Mataimakiyar babban mai shigar da ƙara na ƙasa Mme Maidamma Hadizatou ta cewannan gungun yana aiki ne tsakanin kasashen Najeriya da Togo da Benin da Ghana da kuma Nijar.

    Gungun kan yada zango a Nijar ne kasancewar akwai masu sha da dama inda sauran kuma ake zarcewa da ita ƙasashen ketare.

    Sannan ta kokawa kan yaddajihar Damagaram ke neman zama sabon yankin fataucin ƙwaya daga Najeriya zuwa cikin Nijar domin ƙetarawa da ita ƙasashen waje.

    Hukumar ta kuma yi kira ga al’umma da ta ba su goyon baya wajen daƙile irin wannan yunƙuri na neman ɓatawa ko lalata tarbiyyar matasa ta hanyar sa ido da kula.

    Ta ce hakan zai tabbatar wa matasan makomar kirki a gobe da kuma neman taimako wajen bankado ire-iren waɗannan gungu na masu fatauci da sai da ƙwayoyin.

  12. Wani mai shago ya kori yarinya saboda ba ta saka niƙabi ba

    Ƴan sanda a jihar Assam da ke Indiya sun yi wa wani mai shago tambayoyi, wanda da ake zargin ya kori wata yarinya daga shagonsa saboda ba ta saka nikabi ba.

    Yarinyar ta tafi shagon ne domin sayen abin sauraren sauti kuma ta ce ta yi shigar da ta dace kuma tana sanye wando jeans.

    Amma an ce mai shagon ya ƙi amincewa da ita inda ya ce dole ta fita shagonsa.

    An kuma bayar da rahoton cewa an yi wa yaron mai shagon tambayoyi kan zargin ya tunkari mahaifin yarinyar lokacin da ya zo yana ƙorafi.

    Ya zargi mai shagon da kokarin tursasa dokoki irin na mulkin Taliban a yankin.

  13. An buɗe taron sauyin yanayi na duniya a Scotland

    Firaministan Birtaniya, Boris Johnson ya buɗe taro mai muhimmanci kan sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya a Scotland yana mai gargadin cewa duniya na cikin mumunan haɗari, saboda matsalolin dumamar yanayi.

    Ya ce mun san abin da masana kimiya ke fada mana, mun kuma san cewa ba batutuwan kawar da kai ba ne.

    “Duniya ba za ta taɓa yafe mana ba, kuma ana cikin yanayi na fusata, musamman daga matasa— idan har ba mu dau matakan gaggawa ba domin takaita matsalolin karuwar sauyin yanayi,” in ji shi.

    Mista Johnson ya kuma ce idan aka ci gaba da jan kafa ko nuna gazawa, matsalolin za su ci gaba da girma.

    A nashi jawabin, sakatare janar na MDD, Antonio Guteress ya ce makamashin da aka amfani da su a wannan zamanin ke haifar da barazana a duniya.

  14. An sace sama da mutum 100 masu ibada a wani coci a Kaduna

    Ƴan bindiga sun sace sama da mutum 100 da hallaka mutum guda da kuma jikata wasu biyu a wani hari da suka kai wani coci a jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya, a cewar shugaban kungiyar Kiristoci ta Najeriya reshen jihar, Rabaran Joseph John Hayab.

    Rabaran Hayab ya shaida wa BBC cewa lamarin ya faru ne a Cocin Emanuel Baptist da ke ƙauyen Kakkaudaji a wajen garin Kaduna a ranar Lahadi, yayin da mutane ke tsaka da yin ibada.

    Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tana kan tattara wasu bayanai game da sabbin hare-haren da aka ƙara kai wa bayan na cocin kafin ta fitar da sanarwa gaba ɗaya.

    Bayanan da BBC ta tattara sun nuna cewa lamarin ya faru ne a daidai lokacin da mabiyan ke tsakiyar ibada a cikin cocin nasu, inda suka suka abka musu ta harbe-harbe.

    A baya 'yan bindigar sun tarwasta tare da fattakar al'ummar yankin ƙauyen Kakkaudaji wanda ke kusa da Unguwan Ayaba, suka kuma mamaye shi bayan wani mummunan hari da suka kai.

    Kungiyar Kiristoci ta Najeriya a jihar ta Kaduna ta nuna rashin jin dadinta game da yadda ake yawan kai hare-hare tare da sace-sacen jama'a don neman kudin fansa a jihar, duk kuwa da matakan da gwamnatin jihar ke cewa tana dauka.

  15. Shugaban Zimbabwe a Birtaniya a karon farko cikin shekaru 25

    Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya isa Birtaniya domin halartar taron sauyin yanayi.

    Wannan ne karon farko cikin shekara 25 da wani shugaba daga Zimbabwe ya taka ƙafarsa a Birtaniya.

    Dangantaka tsakanin zimbabwe da Birtaniya ta yi tsami zamanin mulkin shugaba Robert Mugabe wanda Mista Mnangagwa ya gada, bayan ƙwace gonakin fararen fata da kuma batun murƙushe ƴan adawa.

    A cikin wani saƙo a Twitter shugaba Mnangagwa ya yi godiya ga Firaministan Birtaniya da kuma Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya kan kyakkyawar tarba da ya samu a taron sauyin yanayi a Glascow babban birnin Scotland.

  16. Uganda ta haramtawa ƴan majalisar da ba yi wa rigakafin korona ba shiga zauren majalisa

    Za a hana wa ƴan majalisar dokokin Uganda da ba a yi musu allurar rigakafin korona ba shiga ginin majalisar daga ranar Litinin.

    Mataimakiyar shugaban majalisar AnitaAmong ta ce matakin shi ne don "nuna kyakkyawan misali na goyon bayan manufofin gwamnati na kiwon lafiyar jama'a".

    Shafin intanet na jaridar Nile Postta ce majalisar Uganda hukuma ta uku da aka hana waɗanda ba su yi rigakafi ba shiga.

    Shugaba Yoweri Museveni ya faɗa a makon da ya gabata cewa ƴan Uganda suna ƙauracewa rigakafin amma ya bayyana fatan yi wa mutane miliyan 12 kafin ƙarshen watan Disamba.

    Zuwa yanzu sama da mutum miliyan uku aka yi wa rigakafi a Uganda.

  17. An sake kama babban na hannun damar Omar al-Bashir

    An sake kama tsohon na hannun damar hamɓararren shugaban Sudan Omar al-Bashir, kamar yadda kamfanin dillacin labaran Reuters ya ambato iyalinsa da suka tabbatar.

    Tun da farko an sake Ibrahim Ghandour a ranar Lahadi wanda shi ne tsohon shugaban jam’iyya NCP mai mulki da kuma ministan harakokin wajen Sudan.

    Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya na kan hanyar zuwa Khartoum domin shiga tsakanin rikicin siyasar ƙasar.

    Ƴan ƙasar sun ƙaddamar da gagarumar zanga-zanga a ƙarshen mako domin adawa da juyin mulki.

    A bara ne aka kama ce kan zargin zagon ƙasa ga gwamnatin haɗaka.

  18. Shugabannin sojin Sudan sun saki jami’an gwamnatin Al-Bashir

    Sojojin da suka yi juyin mulki a Sudan sun saki jami’an gwamnatin tsohon shugaba Omar Hassan al-Bashir.

    Wata babbar alama ce da ke nuna akwai hannun tsohon shugaban- ko mutanen da ke masa biyayya a juyin mulkin makon da ya gabata.

    Tawagar Majalisar Ɗinkin Duniya na kan hanyar zuwa Khartoum domin shiga tsakanin rikicin siyasar ƙasar.

    Ƴan ƙasar sun ƙaddamar da gagarumar zanga-zanga a ƙarshen mako domin adawa da juyin mulki.

    Daga cikin waɗanda aka saki har da shugaban tsohuwar jam’iyya mai mulki kuma tsohon ministan harakokin waje. A bara ne aka kama ce kan zargin zagon ƙasa ga gwamnatin haɗaka.

  19. Labarai da dumi-dumi, Mutanen da korona ta kashe a duniya sun zarta miliyan biyar

    Masu bincike a Amurka sun ce yawan mutanen da korona ta kashe a duniya sun zarta miliyan biyar.

    Jami’ar Johns Hopkins da ke tattara alƙalumman annobar korona a duniya ce ta wallafa alƙalumman a ranar Litinin.

  20. Korona ta dawo a Nijar

    Ana ci gaba da samun ƙaruwar mutanen da ke kamuwa da cutar korona Jamhuriyar Nijar.

    A baya-bayan nan dai gwamnatin ƙasar ta sanar cewa cutar wadda ta tafi kwanan baya, yanzu ta dawo kuma a kowanne mako ana ganin ƙarin mutanen da take kamawa.

    Mutum 12 suka kamu da cutar a ranar Lahadi yayin da cutar ta kashe mutum ɗaya.

    Ku saurari rahoton wakiliyar BBC Tchima Illa Issoufou