Buhari ya tafi Turai kwana biyu da dawowa daga Saudiyya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Mu kwana lafiya

    Ƙarshen rahotannin kenan a wannan shafi. Mu haɗu da ku a safiyar Litinin don ci gaba da samun sabbin rahotanni kai-tsaye.

    Kafin nan, Umar Mikail ke fatan za ku ƙarasa hutun ƙarshen mako lafiya.

  2. Idan ba mu yi nasara a taron Glasgow ba komai ya rushe - Boris Johnson

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya yi gargaɗin cewa muddin taron sauyin yanayi na COP26 a Glasgow ya gaza to komai ma zai wargaje.

    Mista Johnson ya ce babu wani uzuri mai gamsarwa da zai sa jan ƙafa wajen samar da matakan shawo kan sauyin yanayi.

    Ya ce, tuni aka ga irin matsalolin da sauyin yanayi ya haifar a duniya.

    "Mun samu ci gaba a taron G20 mai muhimmanci amma har yanzu akwai sauran aiki. Mun san cewa muna da fasaha, abin da muke bukata shi ne mu tara kuɗi," a cewar Mista Johnson.

    Tun da farko, Ministan Harkokin Wajen Rasha Sergey Lavrov ya ce "me ya sa kowacce kasa ba za ta iya rage gurɓatacciyar iskar da take fitarwa gaba ɗaya ba zuwa 2050," inda ya ce Rasha za ta cika alkawarin da ta dauka zuwa 2060.

  3. Matashi ya raunata mutum 16 da wuƙa

    Wani mutum da ya yi shiga kamar ta wani tauraro mai suna Joker a fim ɗin Batman ya caka wa mutane da dama wuka a cikin wani jirgin karkashin kasa a Tokyo, babban birnin Japan.

    Aƙalla mutum 15 sun samu raunuka, yayin da ɗaya yake cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai.

    An yi amanna cewa maharin sai da ya fara sanya wuta a daya daga cikin taragon jirgin.

    Wasu bidiyo da aka dauka sun nuna yadda fasinjojin da ke cikin jirgin wadanda suka firgita na kokarin tsira da ransu ta hanyar fita ta tagar jirgin.

    Tun da farko wasu daga cikin mutanen da ke jirgin sun yi tunanin cewa ko wasa ne na bikin tashe ne na Halloween.

    Tuni aka kama maharin mai shekara 20 da 'yan kai.

  4. Tinubu ya ziyarci Buhari

    Tinubu da Buhari

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karɓi baƙuncin jagoran jam'iyyarsu ta APC, Bola Ahmed Tinubu, a fadarsa da ke Abuja ranar Lahadi.

    Da isarsa ne kuma suka wata ganawa cikin sirri.

    Tsohon gwamnan na Legas ya ce ya kai wa Buhari ziyara ne domin ya gode masa.

    "Na zo ne na gode wa Shugaba Buhari saboda ziyarar da ya kai mani a Landan lokacin da nake jinyar ƙafa. Ya nuna mani ƙauna. Shugaba ne na musamman," in ji shi.

    A watan Agusta ne Buhari ya ziyarci Tinubu bayan an yi masa tiyata a ƙafarsa.

    Tinubu da Buhari

    Asalin hoton, State House

  5. Buhari ya tafi Turai kwana biyu da dawowa daga Saudiyya

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari

    Asalin hoton, State Hosue

    Kwana biyu bayan dawowarsa daga Saudiyya, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kama hanyar tafiya birnin Glasgow na Scotland ranar Lahadi.

    Shugaban ya yi balaguron ne domin halartar taron sauyin yanayi da aka yi wa lakabi da COP 26, inda zai haɗu da takwarorinsa na ƙasashen duniya.

    Wata sanarwa da kakakin shugaban kasar, Garba Shehu ya aike wa manema, ta ce sai a ranar Talata Buhari zai gabatar da nasa jawabin a wurin taron sannan kuma zai bayyana irin matakan da ƙasarsa ke ɗauka wajen rage ɗumamar yanayi.

    Ana sa ran shugaban zai gana da shugaban Amurka Joe Biden da kuma na Faransa Emmanuel Macron.

    Taron sauyin yanayin da aka yi wa lakabi da COP 26, taro ne da Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya kuma shugabannin kasashen duniya za su halarta domin duba ina aka kwana game da irinsa na baya da aka gudanar da birnin Paris a shekarar 2015.

    Shugaba Buhari zai samu rakiyar wasu daga cikin kusoshin gwamnatinsa.

    Sanarwar ta Malam Garba Shehu ta kara da cewa Shugaba Buhari zai nausa kasar Faransa domin halartar wani taron kan zaman lafiya da za a yi a birnin Paris.

    Balaguron na shugaba Buhari na zuwa ne kwana biyu bayan ya dawo daga Saudiyya, inda ya halarci wani taron kan zuba jari sannan kuma ya gudanar da aikin Umrah.

  6. Zan yi takarar gwamnan Kaduna a PDP - Shehu Sani

    Shehu Sani

    Asalin hoton, Facebook/Shehu Sani

    Tsohon sanata mai wakiltar Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya ce zai nemi takarar gwamna a jihar tasa ƙarƙashin jam'iyyar adawa ta PDP a babban zaɓen 2023.

    Sanatan wanda aka gani kwatsam a babban taron jam'iyyar na Asabar, ya kwana biyu da bayyana ficewarsa daga jam'iyyar PRP amma ya ƙi fayyace inda ya koma.

    Tsohon ɗan gwagwarmayar ya faɗa wa wakilin BBC Haruna Tangaza cewa mutane ne ke neman ya tsaya takara "amma gara mutum ya nemi muƙamin da zai iya sauya duk abin da aka yi".

    "Hakan yana nufin na koma PDP a hukumance," in ji shi.

    Da aka tambaye shi ko yana da niyyar takara a PDP, sai ya bayar da amsa da cewa: "Mutane na kira mu tsaya takara kuma za mu nema a wajen Allah. Takarar gwamman Kaduna zan yi."

  7. Masu kutse na Iran sun yi garkuwa da shafin 'yan luwaɗi na Isra'ila

    Masu kutse

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu masu kutse da ake kyautata zaton suna da alaƙa da Iran sun fara yaɗa bayanan da suka sato daga shafin soyayya na 'yan luwaɗi mallakar 'yan Isra'ila.

    Wata ƙungiya mai suna Black Shadow ce ta saki bayanan da ta kwaso na dubban ma'abota shafin.

    Bayanan sun ƙunshi sunaye da lambobin waya da kuma abubuwan da mutane suka fi sha'awa a tattare da abokan hulɗarsu.

    Gungun mutanen sun yi barazanar ci gaba da sakin bayanan har sai an biya su fansar dala miliyan ɗaya ta kuɗin intanet cikin kwana biyu.

    Ma'abota shafin sun faɗa wa kafar yaɗa labaran Isra'ila irin fargabar da suke ciki cewa za a iya yaɗa hotunansu tsirara da kuma hirarraki tsakaninsu da masoyansu.

  8. Shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu

    Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Shirin Taɓa Kiɗi Taɓa Karatu na 31/10/2021
  9. Masu yawon buɗe ido da dama sun sun ci guba a otal ɗin Masar

    Kafofin yaɗa labaran Rasha sun ce masu yawon buɗe ido da dama ne suka ci guba a wata otal din Masar da ke Hurgada.

    Kusan mutum 40 aka rahotanni suka ce ke kwance asibiti, yawancinsu yara ƙanana.

    Birnin Hurgada na daga cikin biranen da ake zuwa yawon buɗe ido a Masar kusa da ruwan maliya.

    A cewar sashen Rashanci na BBC, al'amarin ya sa hukumomin Masar sun rufe otal ɗin..

    Ƴan yawon buɗe idon sun ce sun bayyana damuwa game da tsaftar lafiyar otal ɗin ta Masar. Wadanda suka ci gubar sun bayyana cewa sun ce suna jin zazzaɓi mai ƙarfi da da amai da gudawa

    Hurgada

    Asalin hoton, Getty Images

  10. Ƴan Nijar sun kai ƙarar Faransa kan zargin kisan ƙare dangi

    Bayanan sautiƳan Nijar sun kai ƙarar Faransa kan zargin kisan ƙare dangi
  11. Ƴan bindiga sun kashe ƴan sanda biyar a Burkina Faso

    Wasu ƴan bindiga da ba tantance ba sun kashe ƴan sanda biyar a ofishinsu a arewacin Burkina Faso a ranar Assabar, kamar da majiyoyin gwamnati da na tsaro suka tabbatar.

    Lamarin ya faru ne a lardin Sourou da ke kusa da Mali, inda mayaƙan Al Qaeda da IS suka tsawwala kai hare-hare a shekarun baya bayan nan duk da ƙoƙarin ƙasashen duniya na kakkaɓe su.

    Bayanai sun ce maharan sun ce sace mota da babur guda takwas.

    Ƴan bindiga masu da'awar jihadi sun sha kai hare-hare a yankin Sahel inda suka kashe dubban mutane da tursasawa miliyoya da Burkina Faso da Mali da Nijar barin gidajensu.

  12. Ta yaya za ku gane idan kuna da kansar nono?

    Kansar mama ita ce cutar daji da mata suka fi fama da ita inda take shafar aƙalla mace miliyan biyu da dubu ɗari ɗaya duk shekara, a cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO.

    ƙwararriyar likita Hajiya Zainab Bagudu Shinkafi, ta yi bayanin yadda mata za su iya duba kansu don gane ko sun kamu da kansar nono.

    Bayanan bidiyo, Bidiyon Hajiya Zainab Bagudu Shinkafi
  13. SERAP ta sake kai Buhari ƙara kan zargin ɓatan naira biliyan 881

    shugaba Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Ƙungiyar SERAP mai fafutukar yaƙi da cin hanci a Najeriya ta sake kai ƙarar shugaba Buhari inda ta nemi kotu ta tilasta masabincikar zargin “bacewar sama da naira biliyan 881 a ma’aikatun gwamnati da hukumomi 367.”

    SERAP ta ce ta shigar da ƙarar ne a babbar kotun Abuja kuma ta nemi a gano kuɗaɗen da suka salwanta tare da hukunta waɗanda aka samu da laifin salwantarsu.

    Ta ce gano kuɗaɗen zai taimakawa gwamnati maimakon karɓo rance.

    SERAP ta ce ta shigar da ƙarar ne bayan zarge-zargen da ke kunshe a cikin kashi na biyu na rahoton 2018 na babban akawun Najeriya da ya nuna cewa ma’aikatun gwamnati sun kashe sama da biliyan 880 ba tare da amincewa ba.

    SERAP ta sha kai gwamnatin Najeriya ƙara kan batutuwa da dama amma har yanzu babu shari’a ɗaya da aka yanke.

  14. Wane ne Iyorchia Ayu sabon shugaban jam'iyyar PDP?

    Shugaban PDP

    Asalin hoton, Other

    Jam'iyyar PDP ta zaɓi Sanata Iyorchia Ayu a matsayin sabon shugabanta a a babban taron da ta gudanar a Abuja.

    Ana kallon Ayu a matsayin ɗan takarar da taron ya amince da shi a matsayin shugaban PDP. Ya gaji Uche Secondus, wanda aka dakatar a watan Agusta a matsayin shugaban jam'iyyar.

    An haifi Iyorchia Ayu ne a garin Gboko na jihar Benue da ke tsakiyar Najeriya ranar 15 ga watan Nuwambar 1952.

    Ya yi karatunsa na digiri a Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ko da yake daga bisani ya tafi Jami'ar Jos da ke jihar Filato inda ya koyar da Ilimin Sanin halayyar dan adam wato Sociology.

    Ya taɓa zama shugaban kungiyar malaman jami'a, ASUU, reshen Jami'ar Jos.

    Mista Ayu ya tsunduma cikin harkokin siyasa inda a shekarar 1992 ya zama Sanata a karkashin jam'iyyar SDP kuma 'yan majalisar dattawan lokacin suka zaɓe shi a matsayin shugaban majalisar dattawa tsakanin 1992-1993.

    'Yan Majalisar dattawan sun tsige shi Mista Ayu daga kan kujerarsa a watan Nuwamban 1993 sakamakon adawar da ya yi ta kafa gwamnatin riƙon kwarya ta Cif Shonekan.

    Ya riƙe mukamai daban-daban na ministoci. Kuma Mukaman da ya riƙe sun hada da na Ministan Ilimidaga 1993 zuwa 1998 da Ministan Masana'antu tsakanin1999 zuwa 2001.

    Kazalika ya riƙe muƙamin Ministan harkokin cikin gidadaga watan Yulin 2003 zuwa watan Yunin 2005.

    Sannan ya zama Ministan Muhalli daga watan Yunin 2005 zuwa Disambar 2005.

  15. Jagoran Taliban da ba a gani ya ‘bayyana’ a Kandahar

    Taliban ta ce babu wani hoto na Hibatullah Akhundzada  - amma kafofin yaɗa labaran Afghanistan suka fito da wannan hoton

    Asalin hoton, AFGHAN ISLAMIC PRESS

    Bayanan hoto, Taliban ta ce babu wani hoto na Hibatullah Akhundzada - amma kafofin yaɗa labaran Afghanistan suka fito da wannan hoton

    Rahotanni sun ce karon farko shugaban Taliban Haibatullah Akhundzada, da ba kasafai ake ganinsa ba ya fito a bainar jama'a a Kandahar da ke kudancin Afghanistan.

    Ba a sake ganin shi ba tun lokacin da ya zama babban jagoran Taliban shekaru biyar da suka wuce; har ma a lokacin da ƙungiyar ta karɓe iko da Afghanistan a watan Agusta.

    Hakan ya haifar da cece-kuce game da rawar da ya taka a gwamnati, har ma da jita-jitar cewa ya mutu.

    Sai dai babu wasu hotuna ko bidiyon bayyanarsa a Kandahar, amma akwai wani saƙon murya na tsawon minti goma da aka yaɗa a shafukan sada zumunta na Taliban.

    Wanda ke magana a saƙon ya roƙi Allah ya sakawa ƴan Afganistan da suka yaƙi abin da ya kira "kafirai da azzalumai" tsawon shekaru 20.

  16. Amurka ta yi kiran dakatar da yaƙi a Ethiopia

    Ma'aikatar harakokin wajen Amurka ta bayyana damuwa kan ci gaba da faɗan da ake gwabzawa tsakanin dakarun gwamnatin Ethiopia da ƴan tawayen Tigray a arewacin ƙasar.

    Amurka ta sake yin kira ga ƴan tawayen Tigray su fice yankin Amhara da Afar, tare da janye wa daka biranen Dessie da Kombolcha da suka dosa.

    Gwamnatin Habasha ta musanta ikirarin da ƴan tawayen suka yi cewa sun ƙwace ikon Dessie, wanda nisansa bai wuce kilomita 400 ba da Addis Ababa babban birnin Ethiopia.

    An gwabza faɗa a yankin wanda ya tilastawa dubban mutane neman mafaka a Dessie.

    Tigray

    Asalin hoton, Getty Images

  17. An harbe masu zanga-zanga uku a Sudan

    Sudan

    Asalin hoton, Getty Images

    Likitoci a Sudan sun ce aƙalla mutum uku suka mutu bayan da jami'an tsaro suka yi harbi tare da watsa barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga-zangar adawa da juyin mulkin da sojoji suka yi.

    Dubban masu zanga-zanga ne suka fito titunan Khartoum da sauran biranen Sudan a ranar Asabar suna neman a dawo da Firaminista Abdullah Hamdok kan madafan iko.

    A makon da ya wuce ne jagoran juyin mulkin Janaral Abdel Fattah Burhan, ya wargaza gwamnatin farar hula tare da cafke shugabannin siyasa.

    Janaral din da ya ayyana dokar ta-baci, ya ce, ''na dauki matakin ne domin kauce wa fadawar kasar cikin yakin basasa tare da dakatar da rikicin siyasa.''

    Juyin mulkin da sojojin Sudan suka yi ya janyo Allah wadai daga sassa daban-daban na duniya.

  18. Wani ya kashe matarsa saboda ta ƙi musulunta

    Yan sandan Indiya

    Asalin hoton, Getty Images

    Ana zargin wani mutum da kashe matarsa mai shekara 28 a ƙauyen Churai Dalpatpur a a Indiya saboda ta ƙi yarda da tursasawarsa na dole ta musulunta

    Ƴan sanda a Mirgani sun ce suna tsare da mutumin.

    An samu gawar matar mai suna Nisha a rataye a ɗakinta a ranar Talata cikin dare, kamar yadda ƴan sanda suka bayyana.

    Babban jami’in ƴan sandan yankin Raj Kumar Agarwal ya ce binciken da aka gudanar ya nuna ta mutu ne ta hanyar shaƙure wuyanta da igiya ta hanyar rataya.

    Jaridar Hindustan Times ta ce Mahaifiyar matar Kaushal Devi ce ta shigar da ƙara ofishin ƴan sanda tana mai zargin surukinta da kashe ƴarta.

    Ta ce sun yi aure shekaru 10 da suka gabata, kuma mijin ya yi iƙirarin cewa shi Hindu ne, daga baya ne matarsa ta gano asalin addininsa. Sun haifi ƴaƴa biyu mata, amma ya ci gaba da tursasawa matarsa dole sai ta musulunta, kamar yadda mahaifiyar matar ta bayyana.

    Ƴan sanda sun ce sun shigar da ƙara kotu game da batun.

  19. Senata Iyorchia Ayuh PDP ta zaɓa sabon shugabanta

    Taron PDP

    Asalin hoton, Other

    Jam’iyyar PDP ta zaɓi sabbin shugabanninta a babban taron da ta gudanar a Abuja.

    Sanata Iyorchia Ayu ne aka zaɓa shugaban jam’iyyar a babban taron wanda ya zaɓi muƙamai 21 na shugabanni da za su jagoranci jam’iyyar ta adawa a Najeriya a zaɓen 2023.

    Shugabannin sun ƙunshi jagororin PDP a sassan ƙasa.

    An zaɓi wasu muƙaman ba hamayya, wasu muƙaman kuma mutum fiye da ɗaya suka yi takara a taron wanda aka fara a ranar Asabar zuwa Lahadi a dandalin Eagle Square Abuja.

    Ana kallon Ayu a matsayin ɗan takarar da taron ya amince da shi a matsayin shugaban PDP. Ya gaji Uche Secondus, wanda aka dakatar a watan Agusta a matsayin shugaban jam’iyyar.

    Zaben shugabannin PDP

    Asalin hoton, Other

    An zaɓi Umar Damagum a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar PDP a shiyar arewa Taofeek Arapaja a matsayin mataimaki shiyar kudu.

    Samuel Anyanwu ne sakataren jam’iyyar, yayin da aka zaɓi Ahmed Mohammed a matsayin ma’aji.

    Farfesa Stella Effah-Attoe aka zaɓa shugabar mata da Hajara Wanka a matsayin mataimakiya.

    Muhammed Suleiman aka zaɓa matsayin shugaban matasa. Ibrahim Abdullahi kuma jami’in hulɗa da jama’a na Jam’iyyar.

  20. Korona ta kama ƙarin mutum 22 a Bauchi

    Hukumar NCDC da ke ɗakile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya ta ce an samu ƙarin mutum 89 da suka kamu da korona a ranar Asabar.

    Bauchi ne inda cutar ta fi kama mutane a ranar Asabar inda alƙalumman suka bayyana ƙarin mutum 26 da suka kamu da cutar.

    Cutar ta kuma kama ƙarin mutum 17 a Edo da Abuja

    Mutum 15 suka kamu a Legas inda cutar ta fi bazuwa a Najeriya.

    An kuma samu ƙarin mutum 10 da cutar ta kama a jihar Filato, yayin da cutar ta kama mutum hudu a Kaduna.