Buhari zai tafi taron zuba jari da Umrah a Saudiyya

Wannan shafi ne da ke kawo maku labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe idan Allah Ya kai mu

  2. Wakilan kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya sun isa Mali

    Wakilan kwamitin tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya sun isa Mali domin tattaunawa da ƴan siysar ƙasar a daidai lokacin ake zaman fargaba tsakanin da fararen hula da sojojin da suka ƙwace mulki da ne neman tsawaita dawo da mulkin ga farar hula.

    Ecowas ta jaddada cewa dole ne shugaban sojin ƙasar Kanal Assimi Goita, ya miƙa mulki idan an yi zaɓe a watan Fabrairu.

    Wakilan na Majalisar Ɗinkin Duniya waɗanda suka ƙunshi jekadun ƙasashen Faransa da Kenya da Nijar da Amurka za su kuma yi nazari kan yanayin halin tsaro a Mali.

    Mali ta daɗe tana fuskantar hare-hare daga masu da’awar jihadi da kuma rikicin kabilanci a yankin arewaci da tsakiyar ƙasar.

  3. Amsoshin Takardunku kan rikicin Tigray

    Bayanan sautiAmsoshin Takardunku kan rikicin Tigray
  4. Buhari zai tafi Saudiyya

    Shugaba Buhari

    Asalin hoton, Presidency

    Shugabn Najeriya Muhammadu Buhari zai tafi Saudiyya ranar Litinin domin halartar wani taron zuba jari a Riyadh.

    Fadar shugaban cikin wata sanarwa ta ce Buhari zai halarci babban taron na kwana uku wanda zai ƙunshi manyan ƴan kasuwa daga Najeriya da manyan masa’antu da masana makamashi domin tattauna batutuwa da suka shafi makomar saka jari a duniya.

    Bayan kammala taron shugaban na Najeriya zai gudanar da aikin Umrah kafin ya dawo gida Najeriya a ranar Juma’a, a cewar sanarwar.

    Shugaban zai tafi tare da rakiyar jami’an gwamnatinsa da suka haɗa da ministan sadarwa Dr. Isa Ibrahim Pantami da ƙaramin ministan harakokin waje Ambasada Zubairu Dada da ministan man fetur Timipre Sylva da kuma mai ba shugaban shawara kan harakokin tsaro Janar Babagana Monguno.

    Sauran ƴan kasuwa daga Najeriya da za su halarci taron sun haɗa da Alhaji Mohammed Indimi da Alhaji Aliko Dangote daTope Shonubi da Wale Tinubu da Alhaji Abdulsamad Rabiu da Hassan Usman da Omoboyode Olusanya da Abubakar Suleiman da Herbert Wigwe da kuma Leo Stan Ekeh.

  5. Fafaroma Francis ya roki kasashen duniya kan matsalar ƴan ci-rani a Libya

    Fafaroma Francis ya roki kasashen duniya da su kawo karshen matsalolin da 'yan cirani ke fuskanta a Libya.

    Fafaroma ya ce mata da kananan yara har da mazaje manya na fuskantar cin zarafi a kasar.

    Ya bayyana haka ne yayin gudanar da ibadar da aka yi a dandalin St Peters, inda ya ce dole ne kasashe su daina mayar da 'yan irani da 'yan gudun hijira kasashen da babu tsaro irinsu Libya.

    Fararoma ya ce dole ne akawo karshen mayar da 'yan cirani irin wadannan kasashen maimakon haka kamata ya yi a mayar da hankali kan wadanda ke nutsewa a teku.

  6. Dakarun Taliban sun harbe ƴan bindiga masu garkuwa da mutane

    Taliban

    Asalin hoton, AFP

    Hukumomi a Herat yammacin Afghanistan sun ce dakarun Taliban a wata musayar wuta sun harbe wasu ƴan bindiga guda uku da ake zargi masu garkuwa da mutane ne a yankin.

    Kakakin Taliban ya ce mutanen da ake zargi suna satar mutane, sun ɓuya ne a wani bene wanda jami’an tsaro suka yi wa ƙawanya.

    Mazauna yankin sun ce an shafe awanni ana musayar wuta ta hanyar amfani da ƙanana da manyan makamai.

    Wasu rahotanni sun ce masu garkuwar, mambobin ƙungiyar IS ne.

    Taliban ta yi alƙawalin tabbatar da tsaro a Afghanistan ta hanyar ɗaukar tsauraran matakai kan miyagun ayyuka da kuma fatattakar IS da ke kai wa mayaƙan Taliban hari da kuma ƴan shi’a.

  7. Isra’ila za ta ci gaba da gina gidajen Yahudawa a yankin Falasdinawa da ta mamaye

    Gwamnatin Isra’ila ta ci gaba da shirin gina matsugunin Yahudawa gidaje sama da 1,300 a yankin Yamma da Kogin Jordan da ta mamaye.

    An bayar da kwangiloli aikin ginin, wanda ake ganin shine mataki na karshe kafin fara ginin gidajen.

    Wannan shi ne karon farko da Isra’ila ta ci gaba da matakin tun hawan mulkin Shugaba Biden, wanda ke adawa da gina matsugunin na Yahudawa.

    Ana ganin irin wannan ci gaban a matsayin cikas ga kokarin zaman lafiya.

    Falasdinawa da adawa da matakin, wadanda ke son Yamma da Kogin Jordan ya zama wani ɓangare nasu.

  8. 'Yan sandan Jamus sun tarwatsa 'yan zanga-zanga masu tsattsauran ra'ayi

    Jamus

    Asalin hoton, Reuters

    'Yan sandan Jamus sun tarwatsa masu zanga-zanga ɗauke da makamai da ke son hana 'yan cirani shiga ƙasar daga Poland.

    Masu ɗauke da makamai fiye da 50 ne suka fito ɗauke da abin fesa wa mutane da gatari da sauran makamai, a cewar 'yan sanda.

    Ana ɗaukar ƙungiyar a matsayin mai goyon bayan Third Way, wata jam'iyya mai tsattsauran ra'ayi da ke da alaƙa da masu ra'ayin Nazi.

    Jam'iyyar ta yi kira ga mambobinta da su ɗauki mataki kan masu hauro boda zuwa ƙasar, waɗanda suka ƙaru tun daga watan Agusta.

  9. Shugaban Turkiyya Erdogan ya janye wa jakadun ƙasashe 10 rigar kariya

    Erdogan

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya umarci a cire wa mutum 10 jakadun ƙasashe rigar kariya, ciki har da na Amurka da Jamus da Faransa.

    Matakin ya biyo wani kira ne da jakadun suka yi na sakin ɗan gwagwarmaya Osman Kavala.

    Kavala ya kasance a tsare tsawon shekara huɗu sakamakon shiga zanga-zanga da yunƙurin juyin mulki, duk da cewa ba a yanke masa hukunci ba tukunna.

    Matakin cire rigar kariya da ake kira persona non grata na nufin janye dukkanin alfarmar da jakadun ƙasashe ke da su sannan kuma yana iya jawowa a kori jakada daga ƙasar.

    Kiran sakin Mista Kavala ya fito ne daga ofishin jakadancin Amurka da Canada da Faransa da Finland da Denmark da Jamus da Netherlands da New Zealand da Norway da Sweden. Ƙasashen bakwai ƙawayen Turkiyya ne a ƙungiyar tsaro ta Nato.

  10. Kwalejin tarayya a Jihar Bauchi ta kori malamai kan zargin lalata da ɗalibai

    Bauchi

    Asalin hoton, Federal Poly Bauchi

    Hukumar kwalejin gwamnatin tarayya a Jihar Bauchi ta kori malamai biyu sakamakon kama su da laifin cin zarafi ta hanyar lalata da ɗalibai mata.

    Shugaban kwalejin, Sanusi Gumau, shi ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai yana mai cewa an ɗauki matakin ne yayin zaman majalisar zartarwar kwalejin na 98 da suka yi ranar Asabar.

    Bayan samun ƙorafi daga ɗaliban, an kafa kwamatoci da zummar bincikar zarge-zargen waɗanda rahotonsu ne ya nuna cewa sun aikata laifin, a cewar Gumau.

    "Dokokin kwalejin sun bayyana cewa idan aka samu zargi mai girma irin wannan matakin farko da ake ɗauka shi ne bincike," a cewar shugaban.

  11. Kano Pillars za ta buga wasanninta a Sani Abacha a sabuwar kaka

    Sani Abacha Stadium

    Asalin hoton, Kano Pillars

    Hukumar kula da gasar ƙwallon ƙafar ƙwararru ta Nigeria Professional Football League(NPFL) ta amince wa Kano Pillars ta ci gaba da amfani da filin wasanta na Sani Abacha da ke Kano a kakar wasa ta 2021-22.

    Pillars ta fara amfani da filin wasa na Ahmadu Bello da ke Kaduna a matsayin filin wasanta na gida tun bayan ɓullar annobar korona, abin da ya sa aka mayar da Sani Abacha wurin killace masu jinyar cutar.

    Duk da cewa hukumar League Management Company (LMC) mai jan ragamar gasar ba ta sanya ranar fara sabuwar kakar wasan ta 2021-2022 ba, ta amince a yi amfani da Sani Abacha bayan zagayen duba shi da jami'anta suka yi, kamar yadda Pillars ta sanar.

    Ƙungiyar za ta buga dukkan wasanninta na gida a sabuwar kakar a ƙwaryar birnin Kano maimakon Kaduna.

    Ƙungiyar Akwa United ce ta lashe gasar da aka kammala ta 2020-21.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. 'Yan bindiga sun sace masu yi wa ƙasa hidima a Jihar Zamfara

    Masu yi wa ƙasa hidima

    Asalin hoton, NYSC

    Masu yi wa ƙasa hidima a Jihar Zamfara sun shiga halin fargaba sakamakon sace abokan aikinsu da wasu 'yan bindiga suka yi a kan hanyarsu ta zuwa sansanin horarwa na Ƙaramar Hukumar Tsafe.

    Rundunar 'yan sandan Zamfara ta tabbatar da sace masu hidimar biyu waɗanda aka fi sani copers. Sai dai wasu da suka shaida lamarin na cewa mutanen da aka sace sun zarta haka.

    Kakakin rundunar, SP Muhammad Shehu, ya ce Kwamashinan 'Yan Sanda Ayuba Elkana ya ziyarci sansanin, inda ya tabbatar wa jami'an hukumar NYSC yunƙurinsu na kare rayukan corpers ɗin.

    "Rahotan da muka samu daga jagoran NYSC na Zamfara na cewa masu yi wa ƙasa hidima biyu da aka tura daga Jihar Benue zuwa Kebbi da Sokoto na cikin waɗanda aka sace a kan hanyar Tsafe-Gusau ranar Talata 19 ga watan Oktoba," a cewar sanarwar SP Shehu ya fitar ranar Asabar.

    A ranar Laraba da ta gabata ne wani ɓangare na sabbin masu yi wa ƙasa a faɗin Najeriya suka shiga sansanoni don karɓar horo biyo bayan kammala manyan makarantu.

  13. 'Dalilin da ya sa nake yi wa Buhari waka'

    Bayanan bidiyo, Latsa hoton sama ku kalli bidiyo

    Fitaccen mawakin siyasa a Najeriya, Dauda Adamu Kahutu Rarara, ya ce gaskiyar Buhari ce ta sa yake yi wa shugaban na Najeriya waka.

    Rarara ya bayyana haka ne cikin wata tattaunawa da ya yi ta musamman da BBC Hausa, inda yake cewa tun yana yaro ake nusantar da shi kan gaskiya da amanar Buhari kuma har yanzu da ya taso ya gani.

    Ya kara da cewa burin da Buhari yake da shi na gyara Najeriya da ayyukan da yake yi a yanzu ba za su kirgu ba.

    Kodayake a yanzu ya ce yana dab da sakin wasu wakoki da za su bayyana irin ayyukan da shugaban yake yi da wadanda ya kammala, wanda a cewarsa "mutane za su gamsu da ceton Najeriya da Buhari ke yunkurin yi."

  14. Harin Uganda: Akwai yiwuwar na ta'addanci ne - Shugaba Yoweri Museveni

    Yuweri Museveni

    Asalin hoton, State House

    Shugaban Uganda Yoweri Museveni ya siffanta harin bam da ya kashe mutum ɗaya a Kampala babban birnin ƙasar da cewa "akwai yiwuwar na ta'addanci" ne.

    An kai harin ne a wani shahararren wajen cin abinci da ke yammacin birnin a ranar Asabar. Mutum bakwai ne suka jikkata a harin.

    An tsaurara tsaro a wurin da lamarin ya faru yayin da 'yan sanda ke ƙoƙarin gano hujja.

    Waɗanda suka shaida lamarin sun faɗa wa wata kafar yaɗa labarai cewa mutum biyu ne suka shiga wurin da wani abu a cikin kwalaba ƙunshe a jaka. Sai dai har yanzu 'yan sanda ba su tabbatar da nau'in abin fashewar ba.

    Hukumomi a Ugnada na zargin ƙungiyar 'yan aware ta ƙasar Congo mai suna ADF da shirya harin ta'addanci.

  15. Buhari zai ƙaddamar da kuɗin intanet na e-Naira

    Buhari

    Asalin hoton, State Hosue

    Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai ƙaddamar da kuɗin naira na intanet wato e-Naira ranar Litinin, kamar yadda Babban Bankin Najeriya CBN ya bayyyana.

    Tun farko an tsara ƙaddamar da kuɗin ne ranar 1 ga watan Oktoba amma sai CBN ya ɗage bikin yana mai cewa ya ci karo da wasu bukukuwan Ranar 'Yancin Kai.

    Amma a cewar wata sanarwa da daraktan yaɗa labarai na CBN, Osita Nwanisobi, za a ƙaddamar da kuɗin ranar Litinin mai zuwa.

    "Shugaban Ƙasa Buhari zai ƙaddamar da Nigerian Central Bank Digital Currency (CBDC), wanda aka fi sani da e-Naira, ranar Litinin 25 ga watan Oktoban 2021, a fadar gwamnati da ke Abuja," in ji sanarwar.

    CBN ya ce ya shafe shekaru yana bincike game da e-Naira kuma "an ɓullo da ita ne da zummar sauƙaƙa wa kowane ɓangare na al'umma wajen gudanar da harkokin kuɗinsu".

    Kafin yanzu, CBN ya haramta amfani da kowane nau'i na kuɗin intanet, har ma ya umarci bankuna su rufe asusun duk wanda ya ci gaba da mu'amala da shi.

    Ga masu neman ƙarin bayani game da sabon kuɗin na e-Naira, kuna iya shiga adireshin www.enaira.gov.ng ku karanta cikin Ingilishi.

    e-Naira

    Asalin hoton, CBN

  16. Mutum 944 aka kashe a Najeriya cikin wata ɗaya - Rahoto

    'Yan bindiga

    Asalin hoton, Getty Images

    Fararen hula kusan 500 ne aka kashe sakamakon hare-hare da tashin hankali daban-daban a faɗin Najeriya cikin watan da ya gabata na Satumba, a cewar wani rahoto.

    Rahoton wanda cibiyar West Africa Network for Peace Building (WANEP) ta wallafa kuma Daily Trust ta ruwaito, ya ce jumillar 'yan Najeriya 944 ne suka mutu kuma 496 daga cikinsu farar hula ne.

    Daga cikin kashe-kashen, 'yan fashin daji sun yi ajalin mutum 339 a jihohin Zamfara da Kano da Kaduna da Neja cikin watan na Satumba kaɗai, a cewar rahoton.

    An samu rahotannin kashe-kashe a dukkan ɓangarorin siyasar Najeriya shida.

    Yankin arewa maso yamma mai fama da hare-haren 'yan fashin daji ne kan gaba a yawan waɗanda aka kashe da mutum 193. An kashe 84 a Kaduna, 4 a Kano, 5 a Katsina, 5 a Kebbi, 70 a Sokoto da 25 a Zamfara.

    A cewar rahoton har wa yau, an kashe 13 a Jihar Yobe, 12 a Borno, 7 a Adamawa da kuma 4 a Bauchi, dukkansu a arewa maso gabas da ke fama da rikicin Boko Haram.

    A kudu maso gabas kuwa, an kashe 30 a Jihar Anambra, 16 a Imo, 5 a Ebonyi, sai kuma 3 a Enugu.

    A yankin kudu maso kudu ma an kashe 30 a Jihar Delta, 4 a Bayelsa, 1 a Akwa Ibom, 2 a Rivers, 3 a Edo.

    A ɓangaren kudu maso yamma kuma, mutum 8 ne suka mutu a Jihar Legas, 3 a Ogun, 3 a Osun, 2 a Ondo da kuma 1 da ya mutu a Oyo.

  17. An kama gawurtaccen mai safarar miyagun ƙwayoyi a Colombia

    Antonio Usuga

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Colombia Ivan Duque ya bayyana kama shugaban babbar kungiyar masu safarar muggan kwayoyi da aka fi nema a ƙasar mai suna Antonio Usuga.

    Wannan ne babban koma-baya ga duniyar masu sayar da ƙwayoyi tun bayan mutuwar ɗaya shugaban mai karfin fada-aji wato Pablo Escobar.

    Shugaba Duke ya ke ce "a yau mun yi nasarar cafke Antonio Usuga, wannan gagarumar nasara ce a yakin da muke yi da safarar kwayoyi".

    Wani samamen hadin gwiwa tsakanin sojin kasa da na sama da kuma jami'an 'yan sanda ne ya yi sanadin cafke Antonio Usuga wanda aka fi sani da Otoniel.

    A baya dai Amurka ta sanya tukwicin dala miliyan biyar ga wanda ya yi sanadin cafke shugaban kungiyar safarar kwaya da aikata muggan laifuka ta Clan del Golfo.

    Amurka na zargin sa da safarar tan mai yawa na hodar iblis zuwa kasar, kuma tun shekarar 2015 ake kokarin kama shi abin ya ci tura.

  18. Korona ta kashe ƙarin mutum ɗaya a Najeriya, 159 sun kamu

    Cutar ta yi ajalin ƙarin mutum ɗaya ranar Asabar a Najeriya, kamar yadda hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta bayyana.

    Cikin wani rahoto da ta wallafa a shafinta na intanet, NCDC ta ce an samu ƙarin mutum 159 ɗauke da cutar daga jiha 13.

    Jihohin su ne:

    • Kaduna (47)
    • Enugu (44)
    • Benue (36)
    • Delta (10)
    • Lagos (7)
    • Plateau (5)
    • Rivers (3)
    • Nasarawa (2)
    • Bauchi (1)
    • Bayelsa (1)
    • Edo (1)
    • Jigawa (1)
    • Kano (1)

    Kawo yanzu jumillar mutum 210,136 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a Najeriya, sai kuma 2,855 da suka mutu. Sai dai an sallami 198,117 daga wuraren kulawa bayan sun warke.

  19. Maraba

    Barka da shigowa shafin labarai kai-tsaye, inda za ku samu rahotanni kan abubuwan da ke faruwa daga sassan duniya.

    Umar Mikail ne zai kasance tare da ku a wannan hantsi na Lahadi.

    Da fatan hutun ƙarshen mako na tafiya lami lafiya