Sheikh Ibraheem Zakzaky da matarsa Malama Zeenah sun maka gwamnatin Najeriya a babbar kotun kasar don ƙalubalantarta kan ƙwace masu fasfo ɗinsu da Hukumar Jami'an Tsaro ta Farin Kaya ta DSS da Antoni Janar na ƙasar suka yi.
Sheikh Zakzaky da Malama Zeenah, ta bakin lauyan da ke wakiltarsu, Mr Femi Falana sun bayyana wa kotu cewa an yi wa fasfo ɗin nasu gani na ƙarshe ne a hannun Hukumar Leƙen Asiri ta Najeriya, kuma hukumar ta musanta cewa suna hannunta.
Tuni dai malamin da matarsa suka ayyana cewa fasfo ɗin nasu sun bata, sai dai da suka yi ƙoƙarin sabuntawa a ofishin Hukumar Shige da Fice, an shaida masu cewa Hukumar DSS ta dakatar da fasfo ɗin saboda ana gudanar da bincike a kansa.
Sheikh Zakzaky da matarsa sun buƙaci kotu ta tursasa wa hukumomin su sakar masr fasfo ɗinsu ko kuma a ɗage dakatarwar.
Haka kuma, sun buƙaci kotun ta sa hukumomin su biya su naira biliyan biyu a matsayin diyya don ɓata masu suna da shiga haƙƙinsu da aka yi.
Sannan sun ce karɓe masu fasfo ɗin barazana ce ga rayuwarsu tunda an hana su fita Najeriya don samun kulawar likita a asibiti.