An kashe mutane 46 yayin rikici da masu satar shanu a Madagascar
Akalla mutane 46 ne aka bada rahoton sun mutu, yayin wata arangamar da mutanen wasu kauyuka suka yi da masu satar shanu a Madagascar.
An kai harin ne Marovitsika da ke kudancin kasar.
Bayanai sun ce mahara kusan 120 ne dauke da manyan makamai suka dirar wa jama'a kauyen da na kewayensa.
Hukumar kare hakkin dan adam ta kasar ta ce za ta kaddamar da bincike mai zaman kansa a kan yadda lamarin ya faru.
Dama an jima ana samun rikici tsakanin barain shanu da mazauna kauyukan.