An ga hayaƙi a tashar sararin samaniyar duniya
An kaɗa ƙararrawar gargaɗi a tashar sararin samaniyar duniya, bayan da ma’aikatan jirgin suka bayar da rahoton ganin hayaki mai wani irin ƙauri kamar ana ƙona roba.
Lamarin ya fi kamari a wani yanki da ake kira Zvezda da Rasha ta gina a matsayin wurin yada zango ga halittu'' in ji rahoton kafofin watsa labaran Rasha.
Tashar sararin samaniyar da ta shafe shekaru aru-aru ta sha fama matsaloli a shekarun baya bayan nan, don ko a kwana-kwanan nan sai da wani jami’in Rasha ya yi gargadin cewa wasu naurori sun lalace.
Hukumar kula da sararin samaniyar Rasha ta ce bayan samun matsalar, injina sun ci gaba da aikinsu ba tare da wata matsala ba.
An gano hayakin ne yayin cajin batirin tashar, in ji hukumar, kuma yanzu ma’aikatan jirgin sun koma “horo na yau da kullum”.
An ce ƙaurin kona robar da ake ji a yanzu ya fara kai wa ga bangaren da Amurka ta samar a tashar sararin samaniyar.
Hukumar kula da sararin samaniya ta Amurka, Nasa, ta ce hakan ba zai hana ta aika ƴan sama jannatin da ta tsara yi ranar Alhamis ba.
Ku karanta cikakken bayani a kan Cibiyar Kimiyya Ta Sararin Samaniya.