Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Saudiyya ta yi magana kan gwamnatin Taliban

Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya baki daya

Rahoto kai-tsaye

Imam Saleh and Awwal Ahmad Janyau

  1. JAMB ta yi wa El-Rufai raddi kan shawarar fasa rage wa ɗalibai maki

    Hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami'o'in Najeriya JAMB ta mayar wa gwamnan Kaduna Nasir El-Rufa'i martani kan shawarar da ya bata, ta fasa rage wa ɗaliban arewacin Najeriya makin da ake bukata na jarrabawar.

    Hukumar ta ce ba ita ce ke da alhakin ragewa daliban yankin arewacin Najeriya maki ba.

    A cewar JAMB, ''Gwamna El-Rufa'i ya yi kurkure da ya yi tunanin cewa ɗaliban arewacin Najeriya na cin wata gajiya da takwarorinsu na kudancin ƙasar basa ci, wannan kurkusre ne''

    Ma magana da yawun hukumar Fabian Benjaminne ne ya mayar wa gwamnan martanin yayin wata zantawa da jaridar Punch a ranar Talata.

    Ya ce makin da ake bukata ya danganta da kwas ɗin da kowanne ɗalibi ke son yi, da kuma makin da kowacce jami'a ta iyakance.

  2. Amurka ta zargi Taliban da saɓa alƙawari tun ba a je ko ina ba

    Amurka ta soki Taliban kan yadda ta hada gwamnatin Afghanistan babu mata ko tsiraru a ciki.

    Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce ta yi mamakin yadda aka ki saka mata ama aka saka wadanda ake zargi da aikata kisa.

    A kan haka mai magana da yawun ma'aikatar tsaron yace tun yanzu ta fara karya alkawarin cewa za ta kafa gwamnatin kowa da kowa.

    Sabon Firanminista Mullah Muhammad Hassan da kuma ministan tsaro Sirajuddeen Haqqani na cikin yan Taliban da majalisar dinkin duniya da Amurka ke nema ruwa a jallo.

  3. Budewa

      • Marubuci, Imam Saleh
      • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Multimedia Broadcast Journalist

    Daga nan sashen Hausa na BBC Imam Saleh ke fatan kun wayi gari lafiya.

    Muna muku maraba da zuwa wannan shafi da muke kawo muku labaran duniya kai tsaye, musamman na irin abubuwan da ke faruwa a ƙasashen Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya baki ɗaya.

    Sai ku gyara zama don shafe yinin yau da mu.