Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Saudiyya ta yi magana kan gwamnatin Taliban
Labaran abubuwan da ke faruwa a Najeriya da Nijar da sauran sassan duniya baki daya
Rahoto kai-tsaye
Imam Saleh and Awwal Ahmad Janyau
Saudiyya ta ƙaryata zargin tana da hannu a harin 9/11
Saudiyya ta yi maraba da sakin wasu bayanan sirri da suka shafi harin 11 ga watan Satumban 2001 a Amurka a ranar Laraba.
A cikin wata sanarwa, ofishin jakadancin Saudiyya na Amurka ya ce "duk wani zargi cewa Saudiyya na da hannu a hare-haren ranar 11 ga Satumba ƙarya ce kawai."
Shugaban Amurka Joe Biden a ranar Juma'a ya ba Ma'aikatar Shari’a umarnin sake nazari kan bayanan binciken sirrin da hukumar bincike ta FBI ta gudanar kan harin 9/11 domin tantancewa da kuma sake sakin bayanan.
Iyalan waɗanda harin na 11 ga Satumba ya rutsa da su, su suka buƙaci a sake gudanar da bincike kan zargin FBI cewa ta yi ƙarya ko ta ɓoye shaidar da ke tabbatar da hannun Saudiyya da kuma alƙarta da ƴan bindigar da suka kai harin.
Saudiyya ta ce ba ta da hannu da ƙwace ikon jirgin da ya kai hare -haren.
Ofishin jakadancinta ya ce Saudiyya ce ta yi kira da a sake fitar da bayanan binciken harin na Amurka.
“Kamar yadda binciken da ya gabata ya bayyana ... babu wata shaida da ta nuna cewa gwamnatin Saudiyya ko jami'anta suna da masaniya a baya game da harin ta'addancin ko suna da hannu wajen kitsa kai harin,”
Hisbah ta kama motoci maƙare da giya a Kano
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta ce ta samu Nasarar kama Motoci biyu ƙirar J5 maƙare da giya.
Babban kwamandan Hisbah a Kano Dr Harun Ibn-Sina, cikin wani hoton bidiyo da yake bayani ya ce kimanin Kwalbar giya 5,760 jami’an hukumar suka kama kan hanyar Madobi a ranar Laraba.
Hisbah ta sha kamawa da tarwatsa kwalaben giya a jihar Kano
Shugaban Hisbah ya jaddada cewa an haramta shan giya da sayar da ita a faɗin Kano, yana mai cewa hukumar za ta ci gaba da yaƙi da duk wata baɗala a jihar.
Saudiyya ta yi magana kan gwamnatin Taliban
Saudiyya ta ce tana fatan gwamnatin riƙon ƙwarya a Afghanistan za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da kawo ƙarshen tashin hankali da tsattsauran ra’ayi.
Ministan harakokin wajen Saudiyya ne ya bayyana haka a wani taron ministoci kan rikicin Afghanistan.
Yarima Faisal bin Farhan ya kuma jaddada goyon bayan Saudiyya kan abin da ya kira “zaɓin mutanen Afghanistan kan makomar ƙasarsu da kuma tsira daga katsalandan na wasu ƙasashen waje,” kamar yadda kamfanin dillacin labaran Saudiyya SPA ya ruwaito.
Taliban dai ta razana ƙasashen yammacin duniya kan yadda ta naɗa tsoffin mayaƙanta masu tsaurin ra’ayi a manyan muƙamai a sabuwar gwamnatin da ta kafa, cikinsu har da waɗanda Amurka ke nema ruwa a jallo.
Yarima Farhan ya ce Saudiyya mai ƙarfin faɗa a ji a Gabas Ta Tsakiya na da matuƙar muhimmanci ga tasirin taimakawa Afghanistan magance ƙalubalen da ke gabanta.
Tsohon shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya faɗi dalilin tserewa ƙasar
Sama da mako uku bayan tserewarsa daga Afghanistan, tsohon shugaban kasar Ashraf Ghani ya bayyana dalilin da ya sa ya tsere daga Kabul bayan Taliban ta ƙwace ƙasar.
Gani wanda ya bayyana dalilin a shafinsa na sada zumunta, ya ce ya bar kasar ne domin gudun zubar da jini a Kabul babban birnin kasar mai yawan al’umma miliyan shida.
Ya kuma musanta wawushe baitil malin ƙasar a lokacin da ya tsere daga ƙasar.
Tsohon shugaban ya nemi afuwar al'ummar kasar kan yadda abubuwa suka kasance.
Sai dai bai ce komi ba kan Taliban da kuma gwanatin da ta kafa.
Kamfanin MTN ya sabunta lasisinsa a Najeriya
Kamfanin sadarwa na MTN ya sabunta lasisinsa a Najeriya zuwa wasu shekaru 10 daga watan Satumba.
MTN ya ce ya biya naira biliyan 71.6 domin sabunta lasisinsa a Najeriya, kamar yadda kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ruwaito.
Lasisin kamfanin ya ƙare ne a ranar 31 ga Agustan 2021, kuma yanzu ya sake sabunta lasisin wanda ya fara aiki a ranar 1 ga Satumba.
Mene ne ra'ayinku kan katse layukan wayar salula a Zamfara?
Hukumomi a jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun ce matakin da suka dauka na katse layukan wayar tarho da intanet don magance hare-haren 'yan bindiga yana amfani.
Wannan mataki dai ya sa ba a iya sada zumunci ta hanyar waya kuma harkokin kasuwanci suna fuskantar tsaiko ganin cewa ana yin wasunsu ne yanzu ta hanyar waya.
A wannan bidiyon, Umaymah Sani Abdulmumin, ta yi nazari kan tasirin matakin.
Dalar Amurka ɗaya ta kai naira 535
Darajar naira ta ƙara faɗuwa kan dalar Amurka, kamar yadda ƴan kasuwar bayan fage suka bayyana.
Sun ce ana canza ɗala ɗaya kan naira 535 a ranar Laraba.
Tun a watan Yuli naira ke shan kashi, sakamakon matakan da babban bankin Najeriya ya ɗauka a kasuwar canji.
Tsadar dala a Najeriya kan shafi kayan masarufi a ƙasar.
Najeriya na dab da fara amfani da 5G
Najeriya na dab da soma amfani da tsarin fasahar 5G a ƙasar bayan da gwamnatin ƙasar ta amince da tsarin.
Sanarwar da fadar shugaban Najeriya ta fitar ta ce gwamnati ta amince da tsarin ne a taron majalisar ministoci da aka gudanar a ranar Laraba bayan ministan sadarwa Isa Ali Pantami ya gabatar da tsarin a majalisar.
Gwamnatin ta ce tsarin 5G na tsawon shekara biyu, ya shafi neman shawarwari da tuntuɓa da gwaji domin tabbatar da ingancinsa.
“Nan ba da jimawa ba za a saki fasahar ga kamfanonin sadarwa na salula da suka cika sharuɗɗa,” in ji sanarwar.
Gwamnatin Najeriya ta ce ta amince da fasahar ne bayan yin gwaji na tsawon wata uku da aka fara a ranar 25 ga Nuwamban 2019.
Sanarwar ta kuma ce hukumar lafiya ta duniya da kungiyar kamfanonin sadarwa ta duniya sun tabbatar da cewa tsarin ba shi da wata illa ga lafiyar bil adama.
Gwamnatin ta ce tuni ƙasashe da dama na duniya suka soma amfani da fasahar 5G, da suka haɗa da Amurka da Birtaniya da Afirka ta Kudu da Koriya ta Kudu.
Sanarwar ta ce tsarin zai sauƙaƙe amfani da salula musamman ƙarfin intanet da rage yawan cin batir.
An haramta wa wasu ɗalibai zuwa makaranta saboda yaɗa bidiyon batsa
An haramta wa dalibai shida a wata makarantar Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo halartar kowacce makaranta a kasar bayan wani bidiyo da suka dauka ana jima'i ya watsu a kafafen sada zumunta a cewar shafin intanet na Actualite Congo.
An kori daliban daga makaranta ne bayan umarnin da Ministan Ilimin kasa Tony Mwaba ya bayar.
An nadi bidiyon ne a wajen makarantarsu da ke Kinshasa, babban birnin kasar sai dai an nuna su sanye da kayan makaranta.
Bidiyon ya nuna dalibai maza biyar da mace daya.
Sai dai Ministan Kare Hakkin Dan Adam Albert-Fabrice Puela matakin da aka dauka ya saba wa dokar da ke kare hakkin kananan yara.
Minista ya rasa ransa garin ceto mai ɗaukar hoto
Ministan da ke kula da ayyukan agajin gaggawa na Rasha Yevgeny Zinichev ya mutu yayin wani atasaye da ake yi a yankin Arctic mai tsananin sanyi na arewacin duniya.
Ma'aikatarsa ta ce hatsarin ya auku ne lokacin da Mista Zinichev ya yi kokarin ceto ran wani mutum a yankin Norilsk.
Wani rahoton tashar talabijin ta kasar, wato RT ya ce ya mutu ne yayin da ya yi kokarin ceto wani mai daukan hoto wanda ya fado daga saman wani dutse yayin da ministan ke tattaunawa da manema labarai.
Kakakin ma'aikatar Margarita Simonyan ta ce ministan ya garzaya domin taimaka wa mutumin amma sai ya fada kan wani dutse mai tsini wanda ya yi ajalinsa take.
Ƴan Taliban "sun lakaɗa wa mata masu zanga-zanga duka"
Wasu gomman mata sun fito zanga-zangar nuna adawa da ƙin jinin jagorancin kungiyar Taliban a Kabul babban birnin Afghanistan da kuma lardin Badakhshan da ke arewa maso gabashin kasar.
Matan na kuma nuna bacin ransu kan rashin ganin sunan wata mace ko da guda, a kunshin sabuwar gwamnatin kasar da aka sanar.
Wasu rahotanni na cewa dakarun na Taliban sun yi wa matan duka kafin tarwatsa su.
Wata kafar yada labarai mai suna Etilaatroz ta ce an tsare wasu daga cikin 'yan jaridar da ke mata aiki na wani lokaci, kuma an dake su saboda sun dauki rahotannin abubuwan da su ka faru a wajen zanga-zangar.
Kungiyar wadda kawo yanzu ba ta mayar da martani kan batutuwan da matan ke bore a kai ba, ta ce ba za ta lamunci a ci gaba da yi ma ta zanga-zanga irin wannan ba.
Gobara ta kashe mutum 41 a gidan yari
Gobara a wani gidan yari da ke Indonesia ta kashe a kalla mutum 40.
Mai magana da yawun gwamnatin kasar ya ce gobarar ta tashi ne a gidan yarin Tangerang da sanyin safiyar yau Laraba.
Tuni hukumomi sun kaddamar da bincike don gano musabbabin gobarar, to amma ana tunanin daga tangardar wutar lantarki ce.
Saudiyya ta ɗage haramcin shiga ƙasar daga Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa
Saudiyya ta yanke shawarar dage haramcin tafiye tafiye ga kasashe uku da suka hada da Hadaddiyar Daular Larabawa da Afirka ta Kudu da Argentina daga yau Laraba.
Wata majiya a ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar ta ce kasar ta yanke shawarar ɗage dakatarwar ne daga waɗannan ƙasashe ta tashar jiragen ruwa da ta sama sannan kuma za a ba wa ƴan Saudiyya damar tafiya zuwa waɗannan ƙasashe,
A cewar majiyar, matakin ya dogara ne da rahoton da ƙwararru a fannin kiwon lafiya suka gabatar game da halin da ake ciki na annobar korona a kasashen.
Majiyar ta jaddada mahimmancin bin duk matakan kiyaye yaduwar cutar don dakile ta
Ba likitan da ke bin mu bashi - Gwamnatin Najeriya
Ministan ƙwadago na Najeriya Chris Ngige, ya ce babu wani likita a ƙasar da yanzu haka yake bin gwamnatin tarayya bashin ko anini.
Ya bayyana hakan ne lokacin da yake ganawa da kwamitin shugaban ƙasar kan ƙayyade albashi, jim kadan bayan ganawa da gayammar kungiyoyin ma'aikatan lafiya na Najeriya a Abuja.
Ya ce yin wannan bayani ya zama dole, don kore iƙirarin da ƙungiyar likitoci masu neman ƙwarewa ta kasar NARD da yanzu haka ke yajin aiki ta yi.
''Sun je suna gaya wa yan Najeriya cewa mun rike musu albashi, sannan ba ma ɗaukar harkar lafiya da muhimmanci, wannan ba gaskiya bane ko kadan'' inji ministan.
Ya ce ''Sun ɓoye wa jama'a cewa ƴan uwansu da suke ikirarin an riƙewa albashin an ɗauke su aiki ne ta haramtacciyar hanya, don haka gwamnati bata ma san da su ba''.
Makiyaya sun sace shanu sun kashe mutum 13 a Kenya
An bada rahoton mutuwar aƙalla wasu mutane goma sha uku yayin rikici a Kenya.
Bayanai sun ce wasu makiyaya dauke da muggan makamai ne suka kutsa wani kauye a garin Laikipia, suka sace awaki suka bankawa gidaje wuta kana suka lalata gonaki dama.
Tuni aka sanya dokar hana fita a yankin, sannan an ba wa jami'an tsaro umarnin su fatattake su.
Ana ci gaba da samun rashin fahimtar juna game da wuraren yin kiwo da amfani da madatsun ruwa a Kenya.
Za a samu rushewar gidaje da karuwar haɗurra a Najeriya - NIMET
Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargadin samun rushewar gine-gine da hadarurruka a titunan kasar sakamakon ambaliya, yayin da ake ci gaba da zabga ruwan sama a fadin kasar.
Hukumar ta shawarci ƴan Najeriya su yi shirin ko ta kwana, don kiyaye ɓarnar da hakan ka iya haifarwa.
Sakamakon hasashen da ta yi na baya bayan nan, hukumar ta yi gargadi a kan santsin hanyoyi, da samun ƙaƙarfar iska mai kaɗawa.
Haka kuma ta ce akwai yiwuwar ambaliyar za ta shaifi su kansu hanyoyi da tituna, ta kuma janyo rushewar gadojin da jama'a ke amfani da su.
Nnamdi Kanu ya maka Buhari a kotu
Jagoran ƴan awaren Biafra Nnamdi Kanu, ya kai ƙarar shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kotu, saboda zargin take masa haƙƙi.
Ya buƙaci a bada damar mayar da shi Burtaniya don ya ci gaba da zamansa cikin salama.
Cikin karar da Mista Kanu ya gabatar a gaban wata kotu da ke jihar Abia, a kudu maso gabashin Najeriya, ya bukaci shugaba Muhamadu Buhari ya biya shi diyyar Nira biliyan 5, saboda asarar da aka janyo masa a tsawon lokacin da aka kwashe ana kokarin kama shi.
Jagoran ƴan awaren na tsare a hannun hukumar tsaron farin kaya ta Najeriya DSS a halin da ake ciki, bayan kamo shi daga kasashen waje.
Ana zarginsa da laifuka da dama ciki har da cin amanar kasa, da tayar da yamutsi.
Yau za a gurfanar da mutanen da ake zargi da tayar da bom a Paris
Hukumomin Faransa na shirin gurfanar da mutum 20 a gaban wata kotu da ke Paris, saboda da zarginsu da hannu a harin bam da aka kai birnin shekaru shida da suka wuce.
Mutun 130 ne suka mutu daruruwa kuma suka jikkata, a lokacin da yan bindiga suka kai wasu jerin hare hare a Paris.
Wakilyar BBC ta ce mutum 20 ne za su gurfuna bayan zarginsu da hannu a harin kuma cikinsu akwai Salah Abdessalam wanda a baya tarayyar turai ke nema ruwa a jallo.
An kai jerin hare-haren a gidajen abinci da na rawa da kuma filin wasan kwallon kafa na kasa da ke Paris din.
Gwamnatin Kaduna ta musanta shirin katse layukan waya
Gwamnatin jihar Kaduna ta musanta wata jita-jita da ke yawo a shafukan sada zumunta da ke cewa gwamnatin jihar na shirin katse sadarwa a jihar don yaki da 'yan bindiga kamar yadda aka yi a jihar Zamfara.
Wata sanarwar mai ba wa gwamnan jihar shawara kan harkokin watsa labarai Muyiwa Adekeye, gwamnatin ta bayyana cewa bata tuntubi kowacce hukuma ta gwamnatin ƙasar da zummar neman a katse layuna sadarwa ba, don haka jama'a su yi watsi da batun.
''Zance ne mara tushe ballantana makama, babu wannan batu a jihar Kaduna, a bayyana muke komai da ya shafi tsaro, idan akwai wannan bukata za mu dauki matakin da ya dace.
Jihar Kaduna dai na cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, kuma yayin da gwamnatin Zamfara ta katse layukan sadarwa, ana ganin suma sauran jihohin da ke maƙotaka da ita da ke fama da wannan matsala za su dauki irin wannan mataki nan gaba wataƙila