Dalilin da ya sa muke bambanta tsakanin talaka da mai kudi idan sun yi laifi - Hisbah
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
NDLEA ta kama wani mutum da hodar iblis dauri 87

Asalin hoton, NDLEA
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wani mutumi da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi da ake kira Ibeh Kenneth Ejike, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja, dauke da hodar iblis dauri 87.
Mutumin mai shekara 41 an kama shi ne a ranar Laraba 25 ga watan Agustan da muke ciki, bayan saukarsa a jirgi.
Kakakin hukumar Femi Babafemi, ne ya bayyana haka a ranar Lahadi a Abuja yayin gabatar da wannan hodar iblis mai nauyin kilogiram1.88
"Ibeh, wanda yake shigo da kayayyakin sayarwa, ya fito ne daga kauyen Owerrizikeala a karamar hukumar Orumba da ke jihar Anambra, in ji Babafemi.
An kwace kilogiram 400.37 na miyagun kwayoyi gada hannunsa.
Manchester United ta kafa sabon tarihi a Premier

Asalin hoton, Getty Images
Ranar Lahadi Manchester United ta je Molineux ta doke Wolverhampton da ci 1-0 a wasan mako na uku da fara kakar Premier League.
Mason Greenwood ne ya ci wa United kwallon da ta hada maki ukun da take bukata a fafatawar.
Da wannan sakamakon United ta kafa tarihin yawan buga wasanni a waje a babbar gasar Ingila ba tare da an doke ta ba ranar Lahadi.
Kungiyar ta Old Trafford ta yi wasa 28 a waje kenan ba tare da yin rashin nasara ba, wadda ke rike da tarihin ita ce Arsenal mai wasa 27 a kakar 2003/04.
United ta yi wasa na 27 a waje ba a doke ta ba a makon jiya da ta tashi 1-1 a gidan Southampton a karkashin jagorancin Ole Gunnar Solkjaer.
Wani harin jirgi mara matuki ya kashe soji 30 a Yemen

Wani hari da aka kai sansanin soji a kudancin Yemen ya kashe a ƙalla sojoji talatin tare da raunata wasu da dama.
Wani soji da ya shaida lamarin a sansanin na al-Anad ya ce an kai harin ne da jirgi marar matuƙi.
Ya ce: " Mun taru a wani wurin ajiye jiragen sama don yin karin kummalo, sai mu ka ga wani jirgi marar matuƙi yana shawagi a sama kuma mun yi ƙoƙarin harbo shi amma muka kasa samunsa."
An yi ƙoƙarin harbo jirgin amma hakan bai yiwu ba, kuma ya harba makamai masu linzami guda biyu. Rundunar sojin ta zargi ƴan tawayen Houthi da ke iko da mafi yawan arewacin Yemen, da kai harin.
Shugaban Taliban na dab da bayyana a bainar jama'a

Asalin hoton, Getty Images
Wani jami'in Taliban ya shaida wa BBC cewa shugaban ƙungiyar Mullah Hibatullah A-khund-zada yana birnin Kandahar na kudancin Afghanistan kuma ana sa rai zai bayyana a bainar jama'a kwanan nan.
Wannan ya tabbatar da cewa Mullah A-khund-zada ya dawo Afghanistan tun bayan da mayaƙan suka shiga Kabul makonni biyu da suka gabata.
A gefe guda kuma, jami'an ƙungiyar Taliban sun ce za a bai wa mata matasa damar yin karatu a jami'o'in Afghanistan nan gaba amma za a raba masu aji da ɗalibai maza.
A lokacin da ya ke jawabi a gaban wani taro na maza zalla, sabon ministan ilimi mai zurfi, Abdul Baqi Haqqani, ya ce Taliban na so ta samar da manhaja da za ta tafi da tsarin addinin Musulunci.
Wasu ƴan Afghanistan sun nuna ɓacin ransu game da sanarwar, inda suka ce matakin rarraba aji tsakanin maza da mata ba zai yiwu ba a makarantu da dama.
Babu maganar cakuduwar mata da maza a makarantu a mulkin Taliban - Rahotanni

Asalin hoton, Bashir Ahmad Gwakh
Bayanan hoto, Ministan Ilimi mai zurfi na Taliban Abdul Baqi Haqqani 'Yan jarida a Afghanistan na ruwaito cewa Taliban ta sanar da haramta cakuduwar maza da mata a makarantu.
Ziar Khan Yaad - wani dan jaridar Afghanistan da ke aiki da gidan jaridar Tolo - ya ce mukaddashin ministan ilin kasar ya sanar da cewa an daina hada maza da mata wuri daya a jami'o'in kasar " kuma hakan zai ci gaba kamar yadda dokar addinin musulunci ta tanada".
Bugu da kari, wani dan jarida mai zaman kansa Bashir Ahmad Gwakh ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Minisatan ilimi mai zurfi ya sanar da haramta wa maza su koyar da mata a makarantu.
Tun bayan da Taliban ta karbe iko da Afghanistan a farkon wannan watan, ana ta samun maganganun damuwa kan sha'anin mata da yara mata kanana a kasar.
Kauce wa XYa kamata a bar bayanan X?Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X
Labarai da dumi-dumi, 'Yan bindiga sun kashe dan gidan Sanata Bala Na'allah

Asalin hoton, Others
Rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta ce wasu da ake zargin 'yan bindiga ne sun kashe Kyaftin Abdulkarin Bala Ibn Na'allah babban ɗa ga Sanatan.
Cikin wata tattaunawa da ya yi da BBC kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Kaduna ASP Muhammad Jalige, ya tabbatar da mutuwar Kyaftin din sojin.
Rahotanni daga Najeriya na bayyana Abdulkarim a matsayin Kyaftin din sojin Najeriya, sai dai da BBC ta tambayi ASP Jalige kan matsayin marigayin sai ya ce "gaskiya ban san matsayinsa ko aikin da yake ba, amma har yanzu muna tattara bayanai kan wannan lamari."
Duk da cewa 'yan sanda sun ce ba su kammala bincilke kan batun ba, amma rahotanni na cewa za ayi jana'izarsa a makabartar anguwar sarki a Jihar ta Kaduna.
Dalilin da ya sa muke bambanta tsakanin talaka da mai kudi in sun yi laifi - Hisbah

Asalin hoton, Getty Images
Hukumar Hisbah ta Jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta bayyana dalilanta na banbanta mai kudi da talaka a duk lokacin da aka same su da laifi.
Hukumar ta musanta zargin da ake yi mata na cewa ba ta hukunta masu hali lokacin da aka kama su da aikata laifi irin daya da talaka, suna cewa kawai yadda suke mu'amalantarsu ne ya sha banban.
A baya-bayan nan an ta sukar hukumar ne kan dauke ido akan bushashar da ta gudana a auren dan gidan shugaban kasa Yusuf Buhari.
A wata hira da ya yi da gidan rediyon Freedom babban daraktocin hukumar Aliyu Kibiya ya ce ya sabawa koyarwar addinin Musulunci a rika sukar shugabanni a bainar jama'a.
A wata hirar kuma ta daban a wasu shirye-shiryen gidan rediyon shugaban hukumar Haroun Ibn-Sina, ya ce sun kakkama 'yan masu kudi da yawa tare da daukar mataki a kansu, kuma har yanzu suna kamawa.

Asalin hoton, Getty Images
Me yasa Arsenal ke son rabuwa da Willian?

Asalin hoton, Getty Images
Arsenal na fatan kawo karshen kwantiragin da ke tsakaninta da Willian, inda hakan zai ba shi damar komawa Corinthians.
Idan har Gunners ta raba gari da dan kwallon, zai koma taka leda a Corinthians a matakin wanda bai da yarjejeniya da wata kungiyar kenan.
Hakan kuma zai sa Arsenal ta samu rarar albashin da take biyan sa, wanda ke karbar kusan fam 200,000 a kowanne mako, yana da sauran kaka biyu a Emirates.
Willian, mai shekara 33, ya koma Arsenal daga Chelsea, bayan da kwantiragin sa ya kare a kungiyar ta Stamford Bridge.
Labarin kashe 'yan ƙabilar Igbo 230 a Jos ba gaskiya ba ne - 'Yan sanda

Asalin hoton, Nigerian Police
Rundunar 'yan sandan Jihar Filato ta bayyana rahoton da ke cewa wasu mahara sun kashe mutum 230 'yan ƙabilar Igbo a Jos a matsayin labarin ƙarya.
Kakakin rundunar, ASP Ubah Ogaba, shi ne ya musanta rahoton cikin wata sanarwa a ranar Lahadi.
Rahotanni sun karaɗe shafukan zumunta cewa maharan sun cinna wa wa motocin bas da ke ɗauke da mutanen 'yan ƙabilar Igbo wuta, inda suka kashe 230.
Mista Ogaba ya jaddada cewa labarin ba shi da ƙanshin gaskiya sannan ya nemi mutane da su guji yaɗa shi.
Lamarin na zuwa ne bayan rikicin ƙabilanci ya yi sanadiyyar kashe mutum kusan 30 a garin Yelwan Zangam a makon da ya gabata. Kazalika, wasu mahara sun tare wa matafiya hanya tare da kashe 27 mako uku da suka wuce a Jos.
Labarai da dumi-dumi, Taliban: An ji ƙarar fashewa a kusa da filin jirgi na Kabul
Rahotanni daban-daban na cewa an ji ƙarar wata fashewa a kusa da filin jirgi na birnin Kabul.
Wasu hotuna da aka wallafa a shafukan zumunta sun nuna baƙin hayaƙi na dunƙulewa a sararin samaniya.
Wani ma'aikacin lafiya ya tabbatar da faruwar fashewar a yankin.
Ya zuwa yanzu babu tabbacin abin da ya haifar da fashewar.
Paralympics: Najeriya ta samu zinare na biyu a gasar nakasassu

Asalin hoton, Other
'Yar Najeriya Bose Omolayo ta lashe zinare ranar Lahadi.a wasan ɗaga nauyin 79kg na gasar nakasassu ta Paralympics da ke gudana a Tokyo.
'Yar Ukraine Natalia Oliinyk ce ta lashe azurfa yayin da 'yar China ta ci tagulla a wasan.
Bose mai shekara 32 ta ci zinare a wasannin gasar ta 2016 da aka yi a Rio na Brazil sannan ta sake lashe wani zinaren a Gasar Tsalle-Tsalle ta Duniya a Kazakhstan a 2019.
Wannan ne zinare na biyu da Najeriya ta lashe a gasar bayan Latifat Tijani ta yi nasara a wasan ɗaga nauyin 45kg.
Dalilin da ya sa aka kasa daƙile aikata laifuka a Najeriya, ma'anar Ranar Hausa
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari Shirin Amsoshin Takardunku Shirin Amsoshin Takardunku na wannan makon ya duba dalilan da suka sa har yanzu aka kasa kawo ƙarshen aikata miyagun laifuka a Najeriya da kuma ma'anar Ranar Hausa ta Duniya.
Shirin na zuwa muku ta rediyo a ranakun ƙarshen mako kuma Sani Aliyu ne ya gabatar da na wannna makon.
Faransawa 160,000 sun yi zanga-zangar Allah-wadai da dokokin korona

Asalin hoton, Disclose TV
Jumillar 'yan Faransa 160,000 ne suka yi zanga-zangar nuna ɓacin rai da dokokin yaƙi da cutar korona ranar Asabar da suka ce suna matsa wa waɗanda ba a yi wa rigakafin cutar ba.
Ma'aikatar Harkokin Waje ta ce an tarwatsa taron zanga-zanga 222, ciki har da mutum 14,500 da suka fito a birnin Paris.
An kama mutum 16 sannan an ji wa 'yan sanda uku ƙananan raunuka, yayin da aka shafe ranakun ƙarshen mako bakwai a jere ana zanga-zangar ƙin jinin dokokin kulle.
A yankin Bordeaux, masu zanga-zanga da dama sun ce ba za su bari a yi wa 'ya'yansu rigakafi ba 'yan kwanaki kaɗan kafi a koma makaranta.
"Mu ba ɓerayen ɗakunan gwaji ba ne," a cewar wani yaro mai shekara 11 wanda ke zanga-zanga tare da mahaifinsa.
PDP za ta yi taronta na ƙasa a Abuja

Asalin hoton, PDP
Babbar jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta zaɓi birnin Abuja a matsayin wurin da za ta yi taronta na ƙasa.
An cimma matsayar ce yayin taron Kwamatin Zartarwa na 92 da ta gudanar ranar Asabar, wanda shugaban riƙo Elder Yemi Akinwonmi ya jagoranta.
Kazalika, 'yan kwamatin zartarwar sun yanke shawarar sake zama a watan Satumba.
Jam'iyyar PDP na fuskantar rikice-rikice a 'yan kwanakin nan da suka haɗa da barin jam'iyyar da wasu gwamnoni suka yi da kuma sauke shugabanta, Uche Socondus, da wata kotu ta yi. Sai dai wata kotun ta ba shi damar komawa kan muƙamin nasa daga baya.
Tun farko Socondus ya nemi Elder Yemi Akinwonmi ya jagoranci taron wanda shi ne jam'iyyar ta zaɓa a matsayin shugaban riƙo a matsayinsa na mataimakin shugaba daga yankin Kudu, kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya tanada.
Labarai da dumi-dumi, Harin Houthi ya kashe sojojin ƙawance na Saudiyya 30 a Yemen
Aƙalla soja 30 aka kashe sannan wasu 60 suka jikkata ranar Lahadi sakamakon wani da mayaƙan ƙungiyar Huthi suka kai kan rundunar ƙawance da Saudiyya ke jagoranta a Yemen.
Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito mai magana da yawun dakarun kudancin Yemen na cewa 'yan Huthi sun kai hare-haren ne ta hanyar amfani da jirage marasa matuƙa da kuma makamai masu linzami.
Mohamed al-Naqeeb ya ce sojoji tsakanin 30 zuwa 40 aka kashe sannan aka raunata 60, yana mai cewa adadin zai iya wuce haka yayin da masu ceto ke ci gaba da aiki.
Dakarun na kudancin Yemen na ƙarƙashin ƙawancen sojoji da Saudiyya ke jagoranta a yaƙin da ta ƙaddamar a 2015.
Shaidu sun bayyana cewa an kai gawarwaki da dama asibitin garin Lahj tare da mutum 16 da suka ji rauni.
Babu tabbas ko akwai fararen hula a cikin waɗanda harin ya ritsa da su.
'Yan Najeriya 322,000 na gudun hijira a maƙotan ƙasashe - Sadiya Farouq

Asalin hoton, Basheer Garba Mohammed
Ministar agaji da ci gaban al'umma a Najeriya, Sadiya Umar Farouq, ta ce 'yan Najeriya 322,000 ne ke gudun hijira a maƙotan ƙasashe.
Hajiya Sadiya ta bayyana hakan ne ranar Asabar a Abuja yayin da take sauka daga muƙamin shugabancin hukumar kula da 'yan gudun hijira ƙarƙashin tawagar Technical Working Group (TWG), inda ta miƙa wa Hajiya Imaan Sulaiman-Ibrahim muƙamin.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa an miƙa mulkin ne yayin da hukumomi ke ƙoƙarin yi wa 'yan gudun hijirar Najeriya da ke zaune a Kamaru da Nijar da Chadi rajista.
A cewar ministar, 186,957 na zaune ne a Nijar, 118,409 a Kamaru da kuma 16,634 a Chadi.
Ta ƙara da cewa gwamnatin Najeriya na shirin ƙulla yarjejeniya da Nijar da Chadi game da dawo da mutanen gida kamar yadda ta ƙulla da Kamaru.
Yaƙin Boko Haram da kuma hare-haren 'yan fashin daji ne musabbabin tserewar mutane daga muhallansu a arewacin Najeriya, inda dubbai ke tsallakawa maƙotan ƙasashe.
Taliban: Birtaniya ta kammala aikin soja na shekara 20 a Afghanistan

Asalin hoton, CROWN COPYRIGHT
Tawagar ƙarshe ta sojoji da ma'aikatan difilomasiyyar Birtaniya sun koma gida daga Afghanistan, kamar yadda Fadar Downing Street ta bayyana.
Komawar tasu ta kawo ƙarshen shekara 20 na ayyukan soja da suka shafe suna yi a ƙasar ta Afghanistan.
Birtaniya ta kwashe fiye da 'yan Afghanistan 15,000 tun daga ranar 14 ga Agusta.
Firaminista Boris Johnson ya ce wannan dama ce da za a yi nazarin nasarorin da aka cimma a 'yan makonnin nan - da kuma shekara 20, kamar ilimin yara mata da kuma rage wa ƙungiyar al-Qaeda ƙarfi.
Cikin wata wasiƙa da ya aike wa dakarun, Mista Johnson ya ce ƙwace birnin Kabul da Taliban ta yi abin takaici ne ga sojojin.
Ƙarin mutum 650 sun kamu da korona a Najeriya
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 650 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Asabar.
Kazalika, rahoton hukumar ya nuna cewa akwai ƙarin mutum 53 da suka rasu, kodayake ba duka ne suka rasu ranar Asabar ɗin ba.
Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranarAsabar:
- Lagos-261
- Ondo-95
- Rivers-80
- Akwa Ibom-59
- Oyo-24
- Ekiti-22
- Delta20
- Edo-18
- Enugu-15
- Bayelsa-14
- Ogun-11
- Kaduna=8
- Plateau-7
- Kano-6
- FCT-5
- Gombe-3
- Abia-2
A jimillance adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 190,983, sai dai 178,047 sun warke.
Akwai kuma mutum 2,361 da suka mutu.
Maraba
Barkanmu da hantsin Lahadi.
Ku biyo mu domin samun rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya tare da ni Umar Mikail.
