Mutum 784,000 ne ke gudun hijira a Zamfara
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.
Rahoto kai-tsaye
Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge
Jami'an tsaro a Sudan ta Kudu na kama masu rajin kare hakkin dan adam

Asalin hoton, AFP
Ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan Adam a Sudan ta Kudu sun ce jami'an tsaro sun kama mutane da dama ciki har da masu fafutuka da wani limamin coci gabanin wata zanga-zangar ƙin jinin gwamnati da aka shirya yi ranar Litinin.
Ƙungiyar People's Coalition for Civil Action da ta buƙaci a fita tattakin ta zargi manyan ƴan siyasa da gazawa kuma tana so Shugaba Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar su sauka daga mulki.
"Bisa dukkan alamu hukumomi a Sudan ta Kudu na fargaba game da zanga-zangar da za a gudanar ranar Litinin. Ƙungiyoyin fararen hula sun ce an tsare wani limamin coci a garin Yay bisa zargin yana da hannu a shirya zanga-zangar."
Wani mai magana da yawun rundunar ƴan sanda ya musanta kama mutanen.
Amurka ta kashe wasu kwamandodji IS a harin da ta kai Afghanistan

Asalin hoton, Getty Images
Jami'an tsaro a Amurka sun ce wasu ƴan ƙungiyar IS biyu sun mutu a Afghanistan kuma ɗaya ya samu rauni a wani harin jirgi marar matuƙi na Amurka cikin dare a lardin Nan-gar-har.
Sun bayyana mutanen da suka mutu a matsayin manyan mambobin ƙungiyar ta IS.
Babu tabbas ɗin cewa suna da hannu a harin da aka kai ranar Alhamis a filin jirgin sama na Kabul wanda ɗaruruwan mutane suka mutu ciki har da sojojin Amurka goma sha uku.
UNICEF za ta sa likitocin kwakwalwa su duba daliban Tegina kyauta

Asalin hoton, gy
Asusun kula da kananan yara na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai zai ba da taimako ta yadda za a duba lafiyar kwakwalwar daliban makarantar Salihu Tanko da ke Tegina a jihar Neja da ke arewacin Najeriya.
Yaran wadanda adadinsu ya kai 90, an sace su ne kimanin wata uku baya, an kuma sake su a ranar Alhamis da ta gabta.
Wannan kuwa ya biyo bayan kudaden fansar da iyayen yaran suka bayar kamar yadda wata maji ta shaida wa manema labarai, kuma yaro guda ya mutu a hannun 'yan bindigar.
Cikin wata sanarwa da UNICEF ta fitar ta ce ta fuskanci yaran na bukatar taimako domin a duba kwakwalensu a tabbatar da ba su samu matsala ba.
Sabon Ministan ilimi mai zurfi na Taliban ya kama aiki

Asalin hoton, MOHE
Sabon ministan ilimi mai zurfi karrkashin gwamnatin Taliban ya kama aiki tare da tsohon Minista Dr Abbas Bashir.
Kwanaki uku da suka gabata, aka sanar da ssakamakon jarrabawar shiga jami'a.
Daya daga cikin yara matan da suka zauna jarrabawar wadda ta fito daga Kabul, ita ce ta fi kowa cin jarrabawar.
Ta zabi ta karanta aikin likitanci a jami'ar Kabul.
Har yanzu dai Taliban ba ta ce komai ba kan karatun mata.
Mutum 179,929 ne suka zauna zana wannan jarrabawa, kuma cikin 68,930, sun samu shiga jami'a, 11,435 kuma sun shiga kwaleji-kwaleji yayin da 95,201 suka shiga jami'o'i masu zaman kansu.

Asalin hoton, MOHE
Mutum 784,000 ke gudun hijira a Zamfara

Asalin hoton, Getty Images
Kwamishinar da ke lura da ayyukan jinkai da agajin gaggawa ta jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya, Hajiya Fa’ika Ahmad, ta ce suna ta fama da 'yan cirani a jihar da sukai 784,000.
Jaridar DailyTrust ta ruwaito cewa kwamishinar ta ce cikin adadin akwai sama da 184,000 da suke mata sai kuma kananan yara da suka kai 600,000.
Fa’ika ta bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da take karbar kayan abinci da kuma wasu sauran kayan jinkai da ma'aikatar agaji ta kasa ta bayar.
Mataimaki na musamman ga Minista Sadiya Faruk, Alhaji Musa Ahmad Bungudu ne ya mika kayan ga hukumomin jihar.
Kwamishinar ta ce akwai tashin hankali idan aka kalli adadin mata da yaran da suka samu kansu cikin wannan yanayi, dan haka akwai bukatar daukar matakin gaggawa.
Wannan dai na zuwa ne lokacin da Najeriya ta karbi 'yan gudun hijarar Kamaru tare da yi musu rijisata su 73,000.
Farkon kakar wasa mafi muni ga Arsenal

Asalin hoton, Getty Images
Manchester City ta doke Arsenal da ci 5-0 a wasan mako na uku a Premier League da aka fafata a Etihad ranar Asabar.
Tun kafin hutun rabin lokaci City ta zura kwallo uku a ragar Gunners ta hannun Ilkay Gundogan da Ferran Torres da Gabriel Jesus.
Wannan ne karo na biyu da aka ci Arsenal kwallo uku ko fiye da hakan kafin hutu, bayan 4-0 da Chelsea ta ɗura mata a Maris din 2014, inda aka doke Gunners 6-0 a karawar.
An bai wa kyaftin ɗin Arsenal Granit Xhaka jan kati saura minti 10 su je hutu, kuma karo na hudu da ake korar sa daga wasa tun daga 2016/17.
Kazalika shi ne karon farko da Arsenal ta kasa cin wasa a karawa uku da fara kakar Premier League tun bayan ta 1954/55.
City ta zama ta uku da ta zira kwallo 10 a raga a wasa biyu da ta buga a gida na farko Premier League a kakar tamaula, bayan Arsenal da ta yi wannanbajintar a 2010/11 ta ci 10 da Manchester United da ta zura 11 a raga a 2011/12.
'Yan wasan da aka bai wa jan kati hudu a Premier League bayan Xhaka tun daga 2016/17 sun hada da Fernandinho da kuma David Luiz.
Korona: Masu jinyar nau'in Delta sun fi daɗewa a asibiti - Bincike

Asalin hoton, Getty Images
Wani bincike da aka yi a Birtaniya ya gano cewa majinyata da ke fama da cutar korona nau'in Delta za su fi daɗewa a asibiti fiye da wadanda ke dauke da wani nau'in da ba shi ba.
Mujallar lafiya ta Lancet ta ce an yi gwaji kan masu dauke da korona sama da 43,000 a tsakanin watannin Maris da Mayun wannan shekara.
An kuma gano cewa mafi yawan masu kamuwa da korona a Birtaniya a yanzu wadanda ba a yi wa rigakafi ba ne.
Haka ma an fi kamuwa da nau'in na Delta, wanda suka ce shi ne mafi haɗari.
Rikicin PDP: Uche Secondus ya janye daga taron Kwamatin Zartarwa

Asalin hoton, Other
Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya, Uche Secondus, ya janye daga taron Kwamatin Zartarwa na jam'iyyar da ke gudana yanzu haka.
Akwai yiwuwar cewa shugaban ya bi umarnin wata kotun Jihar Rivers ce da ta kore shi a matsayin shugaba, inda ya nemi mataimakinsa ya jagoranci taron.
Mai Shari'a Edem Kufre ne ya umarci Secondus da kar ya sake bayyana kansa a matsayin shugaban PDP biyo bayan ƙarar da wani ɗan jam'iyyar mai suna Enang Wani ya shigar.
Kwana biyu bayan haka ne kuma wata kotu a Jihar Kebbi ta dawo da Secondus kan muƙamin nasa.
PDP ta bayyana sunan Elder Yemi Akinwonmi a matsayin shugaban riƙo, wanda shi ne mataimakin shugaba na yankin Kudu.
Taliban ta tsaurara tsaro don hana mutane zuwa filin jirgi na Kabul
Ƙungiyar Taliban ta tura ƙarin dakaru zuwa filin jirgin sama na Kabul domin hana cincirundon mutane taruwa da ke son barin ƙasar.
Ƙungiyar ta saka ƙarin wuraren duba abin hawa a kan titunan da ke danganewa da filin jirgin.
Wasu daga cikin wuraren na ƙarƙashin kulawar sojojin Taliban sanye da kaki.
Dakarun na ɗauke da kayan yaƙi da suka ƙwace daga sojojin gwamnatin Afghanistan tun bayan da suka ƙwace mulkin ƙasar.
NEDC: Ayyukan da hukumar inganta yankin arewa maso gabashin Najeriya ke gudanarwa
Bayanan sautiAyyukan da hukumar inganta yankin arewa maso gabashin Najeriya ke gudanarwa Shirin Gane Mani Hanya na wannan makon ya duba ayyukan da hukumar inganta yankin arewa maso gabashin Najeriya ke gudanarwa.
Haruna Shehu Tangaza ya zanta da shugaban hukumar, Muhammad J. Alkali, domin jin irin ayukkan da suka yi kawo yanzu da kuma martaninsu ga zarge-zargen cewa ba sa aiki.
'Yan bindiga sun kashe mutum uku a kudancin Kaduna

Asalin hoton, Getty Images
Aƙalla mutum uku aka kashe tare da raunata wasu sakamakon wasu hare-hare da aka kai a Ƙaramar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna.
Lamarin wanda ya faru ranar Juma'a a ƙauyukan Machun da Manuka, ya biyo bayan kashe mutum biyar da aka yi ne a farkon watan Agusta a yankin.
Kwamishinan Tsaro Samuel Aruwan ya tabbatar da kai harin cikin wata sanarwa, yana mai cewa maharan sun shiga garuruwan ne suna harbe-harbe a kan mai tsautsayi.
Aruwan ya ce jami'an tsaro sun amsa kiran gaggawa daga garin Machun, inda da isarsu wurin suka jiyo ƙarar harbi a ƙauyen Manuka mai maƙotaka.
Sai dai ya ce gawar mutum uku 'yan sandan suka tarar da kuma adadi mai yawa na waɗanda aka raunata bayan isarsu yayin da maharan suka tsere kafin su ƙarasa.
Yadda jinin haila ke zuwa da ciwon mara
Bayanan sautiLatsa hoton sama ku saurari shirin Lafiya Zinariya A wannan makon shirinmu na Lafiya Zinariya ya duba yadda mata masu al'ada suke fama da ciwon mara.
Matan da ba su wuce jinin haila ba kan fuskanci ciwo a kasan mararsu, kafin jinin al'adar ya fara zuba ko kuma bayan haka.
Hukumar Lafiya ta Burtaniya (NHS) ta ce ciwon mara abu ne da ya zama ruwan dare kuma wani ɓangare ne na haila. Kuma ciwon yakan dauki kwana biyu zuwa uku ko fiye ana yi.
Sannan yakan zama matsananci ga wasu mata, yayin da wasu kuma yakan zo musu ne sama-sama, in ji hukumar.
Haka kuma wani sa'in wasu kan ji kwankwasonsu na ciwo, ko da ba lokacin jinin haila ba ne.
Mata na jin ciwon mara ne a cewar NHS idan naman da ke jikin mahaifa ya murɗe.
Gwamnan Zamfara ya bayar da umarnin rufe wasu kasuwanni a jihar

Asalin hoton, ZFSG
Gwamnan Jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayar da umarnin rufe dukkan kasuwannin da ke ci mako-mako a jihar tare da taƙaita safarar kayan abinci.
Wata sanarwa da fadar gwamnatin jihar ta fitar a yammacin Juma'a ta ce daga yanzu an hana sayar da man fetur a gefen titi wato 'yan bumburutu, sannan kuma an haramta zuba shi a cikin jarka.
Kazalika, an haramta wa gidajen mai da ke ƙauyuka sayar da man sai a birnin Gusau da kuma hedikwatar ƙananan hukumomin jihar kaɗai.
Haka nan, gwamnan ya bayar da umarnin dakatar da shiga da kuma fitar da kayan abinci daga Zamfara. Sai dai za a ci gaba da harkokin a cikin jihar amma da sharaɗin sai mai shi ya yi cikakken bayanin inda zai kai kayan, a cewar sanarwar.
Mai taimaka wa gwamnan Zamfara kan kafofin yaɗa labarai, Zailani Bappa, ya ce an ɗauki matakan ne da zummar daƙile yi wa 'yan fashin daji safarar kayayyakin zuwa cikin dazukan jihar.
Jerin matakan na zuwa ne ƙasa da kwana ɗaya bayan 'yan fashin dajin sun sako ɗaliban Kwalejin Aikin Noma da Kiwon Dabbobi da suka sace a Bakura.
Ba China ce ta ƙirƙiri cutar korona ba - Hukumar asiri ta Amurka
Wani rahoton hukumar leƙen asiri ta Amurka ya ce ba China ce ta ƙirƙiri cutar Korona ba tare da musanta cewa an kirkiri annobar ce a matsayin makamin ƙare-dangi.
Wakilin BBC ya ce da ma China ta sha musanta cewa daga wani ɗakin gwaje-gwaje na gwamnati da ke Wuhan ne Korona ta ɓulla, har ma ta ce Amurka ce ta samar da shi.
Da dama daga masanan da suka yi aiki kan rahoton sun yarda cewa an samo Korona ne daga dabbobi, yayin da ƙalilan suka ce daga ɗakin gwaje-gwaje ta fito.
Birtaniya za ta gama aikin kwashe 'yan Afghanistan a yau

Asalin hoton, Getty Images
Dakarun sojan Birtaniya za su kawo ƙarshen aikin kwashe fararen hula daga Afghanistan a ranar Asabar, a cewar babban hafsan sojan ƙasar Janar Nick Carter.
"Mun kai ƙarshen kwashe mutane wanda za mu daina daga yau," kamar yadda ya shaida wa BBC.
"Kuma daga nan ya zama wajibi mu ɗebo sojojinmu da sauran jiragen.
"Ba mu samu damar kwaso kowa da kowa ba kuma ba mu ji daɗin hakan ba. Sai dai akwai ƙalubale da muka dinga fuskanta yayin aikin."
Jumillar mutum fiye da 100,000 na fararen hular Afghanistan aka kwashe zuwa ƙasashen waje yayin da dubbai ke can suna jira su tsere daga mulkin ƙungiyar Taliban wadda ta ƙwace mulki mako biyu da suka wuce.
Korona ta sake kashe mutum 10 a Najeriya
Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 618 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Juma'a.
Haka nan, cutar ta yi ajalin wasu mutum 10.
Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jihar Lagos suke, inda aka samu mutum 312 dauke da cutar, yayin da a Akwa Ibom aka samu 89.
Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranar Juma'ar:
- Lagos-312
- Akwa Ibom-89
- Edo-71
- Rivers-41
- Ekiti 20
- Plateau-20
- Delta-15
- Kwara-14
- FCT-11
- Osun-8
- Oyo-4
- Ogun-3
- Benue-3
- Gombe-1
- Kaduna-1
Jumillar adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 190,333, sai dai 169,815 sun warke.
Akwai kuma mutum 2,308 da suka mutu.
Barka
Maraba da shigowa shafinmu na labarai kai-tsaye, wanda zai kawo rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.
Sunana Umar Mikail kuma ni ne zan kasance da ku a wannan hantsi na Asabar.
