Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

NNPC ya ci ribar farko cikin shekaru 44 a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Wane hali ake ciki game da kwashe fararen hula daga Kabul ?

    Dubban mutane na ci gaba da kasancewa a Afghanistan duk da ci gaba da jigilar fararen hulla da jiragen soji ke yi inda aka kwashe mutane kusan dubu ashirin cikin awanni ashirin da hudu da suka gabata.

    Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Antony Blinken, ya dage cewa kokarin Amurka na taimaka wa mutane barin kasar zai ci gaba.

    Mista Blinken ya ce kungiyar Taliban na ci gaba da bada hadin kai ba tare da kawo cikas ga wannan aiki ba, kana shugaban kasa ya nemi a yi shiri na musamman ko da zai yanke shawarar dakarunmu su ci gaba da zama a Afghanistan bayan wa'adin da aka sanya.

    To sai dai Taliban ta ki amincewa da karin wa'adin, yayin da sakataren tsaron Burtaniya ya fada wa 'yan majalisar kasar cewa zai fi kyautuwa ga 'yan Afghanistan din da ke son ficewa su yi hakan ta kasa.

  2. Sabon shugaban Zambia ya ce ba zai zauna a fadar shugabancin kasar ba

    Sabon shugaban Zambia Hakainde Hichilema zai ci gaba da zama a gidansa, inda rahotannin jaridar Zambia Daily Mail suka ce ba zai shiga fadar shiugabancin kasar ba.

    Wannan kuma na zuwa ne duk da cewa Edgar Lungu zai bar fadar a wannan makon.

    Yanzu sabon shugaban na haya ne a wani gidan ɗan kwallon kafa dan Zambia da ke zaune a China Stopilla Sunzu, kamar yadda rahotanni suka ce.

    Amma an rawaito sakataren shugaban, Batuke Imenda, na cewa babu abin da zai hana shi yin aiki a fadar gwamnatin kasar, amma ya zuwa yanzu zai ci gaba da zama a gidansa domin ci gaba da aiki, a gidn nasa da ake kira da Community House.

    "Kamar yadda na fadi da farko, an rantsar da shi, shugabanmu zai ci gaba da aiki daga gidansa da ke New Kasama. Ya fi samun kwanciyar hankali a Community House. In kuma ka kwatanta za kaga gidansa ya fi kyau, in ji Imenda kamar yadda jaridar ta ruwaito.

  3. Yau ne za a raba jadawalin Champions a Istanbul

    Yau hukumar kwallon kafa ta Turai za ta raba jadawalin gasar Champions mai zuwa wanda za a yi a birnin Istanbul na Turkiyya.

    Beşiktaş da za ta wakilci Turkiyya a gasar da samu kanta cikin kwarya ta hudu ta kungiyoyin da za su buga gasar.

    Za a fara kasa jadawalin daga karfe 19:00 a dakin taro na Haliç da ke Istanbul.

    Za a fara wasannin rukuni a ranar 14 da 15 ga watan Satunba a kuma kammala a ranakun 7 zuwa 8 ga watan Disamba.

    Ga yadda kwaryar da aka sanya kungiyoyin ta ke:

    Kwaryar farko ta hada da: Chelsea, Villarreal, Atletico Madrid, Manchester City, Bayern Munich, Inter, Lille, Sporting

    Kwaryar ta biyu: Real Madrid, Barcelona, Juventus, Manchester United, PSG, Liverpool, Sevilla, Dortmund

    Kwaryar ta uku: Porto, Ajax, Shakhtar, Leipzig, Salzburg, Benfica, Atalanta, Zenit

    Kwaryar ta hudu: Besiktas, Dinamo Kiev, Dinamo Zagreb, Club Brugge, Young Boys, Milan, Malmo, Wolfsburg

  4. Sojojin Najeriya sun dakile harin 'yan Boko Haram a Jihar Yobe

    Sojojin Najeriya sun hana 'yan Boko Haram satar kayan abinci a kauyen Babangida da ke karamar hukuar Tarmuwa a Jihar Yobe da ke arewacin Najeriya.

    Jaridar PRNigeria ta ruwaito cewa sai da 'yan tada kayar bayan suka fara fasa wasu shaguna suka kwashi kayan abinci da magunguna kafin daga bisani su tsere bayan da sojojin Najeriya suka hare su.

    Ba dai a tabbatar da cewa ko maharan 'yan Boko Haram ba ne ko kuma 'yan ISWAP ba.

    Wani jami'i ya tabbatar wa da PRNigeria cewa maharan sun gudu sun bar wasu daga cikin kayan da suka sata da ganin sojojin.

  5. Za a binne tsohon shugaban kasar Chadi Hissène Habré a Senegal

    Za a binne tsohon shugaban Chadi Hissène Habré a ranar Alhamis.

    Tsohon shugaban ya mutu ne a ranar Talata sakamakon annobar korona yayin da yake tsare a gidan yarin Senagal a matsayin daurin rai da rai sakamakon laifin cin zarafin dan adama.

    Iyalinsa sun ce za a rufe shi a Dakar babban birnin Senegal.

    A 2016 ne, aka samu Harbe da laifin cin zarafin dan adama lokacin da ya shugabanci kasar tsakanin 1982 zuwa 1990.

  6. Matawalle na son a kafa dokar ta-ɓaci a jihohin arewacin Najeriya

    Gwamnan Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya Mohammed Bello Matawalle ya yi kira da a sanya dokar ta-baci a duka jihohin arewacin kasar dangane da matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin.

    Ya yi wannan kira ne yayin wata tattaunawa da ya yi da mataimakin shugaban 'yan sanda da ke lura da shiyya ta 10 da ke Gusau Ali Janga.

    Gwamnan, wanda ya nuna damuwa matuka kan yadda ake kai hare-hare a mafi yawan jihohin yankin, ya yi amannar cewa sanya dokar ta-ɓacin za ta taimaka wajen shawo kan matsalar tsaron.

    Yankin arewacin Najeriya ya hadar da shiyoyi uku, shiyyar arewa maso gaba - da arewa maso yamma da kuma arewa ta tsakiya ga kuma babban birnin kasar na Abuja da ke yankin.

    Shekaru masu yawa, yankin ke fama da ayyukan 'yan tada kayar baya da suka hada sace mutane don neman kudin fansa da tashe-tashen bam, da harin 'yan fashin daji da dai sauransu.

    Kuma kafin yanzu an kashe daruruwan mutane a yankin yayin da irin wadannan rikice-rikice suka tilasta wa mutane da yawa barin gidajensu domin tsira da rayuwarsu.

    Kungiyar Boko Haram da ISWAP sune suka fi damun yankin arewa maso gabas, yayin da sace mutane domin kudin fansa da kuma 'yan fashin su ke damun yankin arewa maso yamma da kuma maso tsakiya.

  7. Turkiyya za ta fara kwashe sojojinta daga Afghanistan

    Turkiyya ta sanar da fara kwashe sojojinta daga Afghanistan.

    Sama da sojojin Turkiyya 500 ne suke zaune a Afghanistan a matsayin sojin kawancen NATO.

    A baya, an ta rade-radin cewa dakarun Turkiyya za su ci gaba da zama a kasar har bayan 31 ga watan Agusta domin ci gaba da tafiyar da filin jirgin Kabul.

    Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato shugaba Recep Tayyip Erdogan na cewa a kwai bukatar Afghanistan ta koma cikin hayyacinta.

    Kuma ya ce Turkiyya za ta ci gaba da tattaunawa da duka bangarorin biyu domin ganin an cimma wannan nasara.

  8. An kashe 'yan Boko Haram da ISWAP 43 a Nijar

    Dakarun kawancen kasashen Afrika da ke aiki yankin Jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar sun kashe mayakan Boko Haram da na ISWAP 43 a wani harin ramuwar gayya da suka kai a yankin Baroua.

    Cikin wata sanarwa da kakakin tawagar kanar Muhammad Dole ya fitar a ranar Laraba ya ce an jikkata wasu mayakan da yawa cikin wadanda suka kai wa harin.

    Sanarwar ta ce an kama wani da ake zargin shugaban mayakan ne a a raye, an kuma samu nasarar kwace harhasasai masu yawa.

    Cikin abubuwan da aka lalata akwai motocin igwa hudu da mayakan suka fita da su.

    An kashe dakarun kawance bakwai a lokacin wannan dauki ba dadi, an kuma raunata hudu daga cikinsu wadanda a yanzu haka suna kwance a asibiti.

    .

    Da suke tattaunawa da dakarun Kanar Mamane Sani Kiaou da Janar Ibrahim sun ce duk da mika wuyan da mayanakan kungiyoyin biyu ke yi, ka da su sake hakan ya zama wani abu da zai rage musu azama a yakin da suke da kungiyoyin a yankin tafkin Chadi.

    A ranar Laraba ne dai, wasu da ake zaton mayakan Boko Haram ne da na ISWAP suka kai wa dakarun kawance hari a sansaninsu, abin da ya janyo mayar da martani kenan daga dakarun cikin ‘yan mintina kalilan

  9. Za a iya kai hari filin jirgin saman Kabul a ko wanne lokaci - Amurka

    Amurka da Burtaniyar sun yi gargadi game da barazanar kai hari filin jirgin saman Kabul dake Afghanistan din, suna jan hankalin yan kasashensu da kada su yi balaguro kasar.

    An shawarci wadanda ke ciki a yanzu haka su tattara yanasu ya nasu su fice. Gargadin na zuwa ne sa’o’i 24 bayan da Shugaba Biden ya yi karin haske kan hadarin da masu tsattsauran ra’ayi da ke da alaka da kungiyar ISIS ke haifarwa.

    Kwamandojin sojin Amurka a filin jirgin saman na Kabul na ƙara damuwa kan yiwuwar kai harin kunar bakin wake ko tashin bom a taron jama'ar da ke ƙoƙarin shiga filin jirgin don tserewa.

    Rahotanni daga Kabul sun ce 'yan Taliban sun rufe dukkan hanyoyin shiga filin jirgin saman.

  10. Zanga-zangar da ake yi a gabar yammacin Kogin Jordan ta dauki sabon salo

    Gungun masu zanga-zanga sun koma kan titunan Ramallah, a gabar yammacin Kogin Jordan da Isra'ila ta mamaye, don neman karin 'yancin fadin albarkacin baki.

    Yawancinsu sun shiga zanga zangar ne jim kadan bayan an sake su daga kurkuku, bayan da jami'an tsaron Falasdinawa suka cafke su a zanga -zangar lumana a karshen mako.

    Zanga -zangar adawa da shugabancin Falasdinawa, musamman Shugaba Mahmud Abbas ta kara kankama, bayan mutuwar wani fitaccen dan gwagwarmayar siyasa da ake tsare da shi watanni biyu da suka gabata.

    A ranar Talata, jami'an diflomasiyya daga kasashen Tarayyar Turai da Burtaniya sun bayyana damuwar su a kan kamen , da kuma yadda ake cusgunawa jama'a.

  11. An gano rigakafin Malaria da ka iya rage ta a duniya da kashi 70 cikin 100

    Sabon bincike a Yammacin Afirka ya nuna cewa hada allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro ko Malaria da magungunan yaki da ita na iya rage masu kamuwa da cutar da wadanda take kashewa da fiye da kashi saba'in.

    Amma babban mahimmin sharadin shine ayi wannan hadi kafin farkon daminar kowacce shekara da kan fara daga watan Yuni.

    Zazzabin cizon sauro ya fi shafar yara da matasa, sannan yana kashe sama da mutane dubu ɗari huɗu a kowace shekara, galibi a Afirka.

    An gudanar da sabon binciken ne kan wasu yara dubu shidda wadanda basu wuce wata biyar a duniya zuwa 17 ba a kasashen Burkina Faso da Mali.

    Sakamakon ya nuna cewa hada rigakafin cutar na farko da aka fara samarwa a duniya da magungunan yaki da ita ya fi tasiri ainun a kan cutar fiye da amfani da kowannensu shi kadai.

    Masana kimiyyar na London School of Hygiene sun bayyana sakamakon a matsayin "abin ta'ajibi" kuma mujarrabi.

  12. Karin mutum 637 sun kamu da korona a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 655 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Laraba.

    Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a jihar Lagos suke inda aka samu karin mutum 322 dauke da cutar, yayin da a Rivers aka samu mutane 70da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

    Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranarLitinin:

    • Lagos-322
    • Rivers-70
    • Edo-54
    • Delta-34
    • Akwa Ibom-31
    • Kwara-31
    • FCT-29
    • Ekiti-17
    • Ogun-14
    • Osun-10
    • Kebbi-8
    • Cross River-5
    • Plateau-3
    • Taraba-3
    • Kaduna-2
    • Bayelsa-2
    • Benue-1
    • Enugu-1
    • Kano-1

    A jimillance adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 188,880 , sai dai 169,382 sun warke.

    Akwai kuma mutum 2,288da suka mutu.

    A baya-bayan nan ne aka samu ɓullar sabon nau'in cutar korona da ake kira Delta a Najeriya, wanda masana ke cewa yana da saurin yaɗuwa matuƙa.

  13. Barka

    Maraba da shigowa shafinmu na labarai kai-tsaye.

    Buhari Muhammad Fagge me ke fatan kasancewa da ku a wannan yini domin ka wo muku labarai da rahotanni daga sassan duniya baki daya.

    Ku kasance da mu.