Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

NNPC ya ci ribar farko cikin shekaru 44 a Najeriya

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Buhari Muhammad Fagge and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Bankwana

    Masu bibbiyar mu a wanna shafi da ke kawo muku bayanai kai-tsaye anan zamu diga aya sai kuma gobe Juma'a idan Allah ya tashe mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke muku fatan alheri.

  2. Labarai da dumi-dumi, An saki ɗaliban Islamiyyar Tegina da ƴan bindiga suka sace a Neja

    Rahotanni na cewa an saki sama da ɗaliban Islamiyyar Tegina 80 da ƴan bindiga suka sace a jihar Neja.

    Jaridar PRNigeria ta rawaito cewa majiyoyin tsaro sun tabbatar mata da cewa suna hanyar Minna ta Kagara bayan ƴantosu daga dajin Birnin Gwari.

    Ɗaliban sun shafe kwanaki 88 a hannun ƴan bindiga da suka yi garkuwa da su.

  3. Rikicin kabilanci ya yi ajalin mutum 200 a yankin Oromia na Ethiopia

    Sama da mutum 200 aka kashe a wni rikicin kabilanci a yammacin Ethiopia.

    Hukumar kare haƙƙin bil adama ta Ethiopia ta ce ƴan tawayen Oromo sun hallaka mutum 150.

    Bayanan da hukomomin yankin suka yiwa BBC na cewa an shafe mako biyu ana rikici tsakanin kabilar Amhara da Oromo.

    Wani shaidawa ya fadawa BBC cewa gawawaki da dama ruwa ya wuce da su a kogi, sannan an binne wasu.

    Dubbai sun rasa hidajensu wasu kuma sun yi gudun hijira sakamakon rikicin.

  4. Kisan mutanen mu 33 a Jos ya ba mu mamaki – Kabilar Anaguta

    Ana ci gaba da jimami da kuma zaman zullumi a birnin Jos da kewaye bayan wani mummunan hari da wasu ‘yan binidga suka kai a kauyen Yelwan-Zangam dake wajen birnin inda rahotanni ke cewa sun kashe mutane fiye da talatin.

    Dokar hana fita ba dare-ba-rana da gwamnatin jihar ta kafa na ci gaba da aiki a birnin da kewayensa.

    Galibin wadanda harin na Talata da dare ya rutsa da su dai ‘yan kabilar Anaguta ne.

    Shugaban Kungiyar ci gaban Al’umar ta Anguta na kasa, Mr Garba Sunday Bunu, ya yi wa Ishaq Khalid karin bayani kan halin da ake ciki.

  5. Magidanci ya rataye kansa bayan kashe matarsa a Bayelsa

    Wani magidanci mai shekara 46, Patrick Markson ya rataye kansa bayan kashe matarsa, Hannah Markson a jihar Bayelsa da ke kudancin Najeriya.

    Lamarin ya faru ne a unguwar Odede da ke birnin Yenagoa, abin da ya kai ga mutane sun shiga ruɗani da sanyi safiyar Alhamis.

    Ma'auratan kamar yada rahotanni ke cewa sun samu saɓanin abin da ya kai su ka dambe kafin kisan.

    Shaidu sun shaida cewa magidancin ya bugi matar da guduma kuma nan take ta faɗi ta mutu.

    Bayan lura da abin da ya aikata, sai mutumin ya sha guba ya mutu, kuma ya rataye kansa.

    Jaridar Daily Trust a Najeriya ta rawaito cewa ma'auranta sun mutu sun bar yara shida.

    'Yan sanda a Bayelsa sun tabbatar da faruwar al'amarin.

  6. Labarai da dumi-dumi, Kungiyar IS ta ce ita ta kai harin bam filin jirgin sama na Kabul

    Kungiyar IS ta dauki alhakin kai hare-haren bam da aka kai filin jirgin sama na Kabul.

    Ikirarin ya biyo bayan wani sako ne da ta wallafa a shafinta na Instagram.

    Kungiyar ta ce wani dan kunar bakin wake ne - ya sanya rigar bam ya shiga tsakanin 'yan Afghanistan da dakarun Amurka.

    Jami'an hukumar tsaron Amurka sun ce sun yi amannar mayakan IS da ke yankin ne suka kai harin.

  7. Gwamna Matawalle ya yaba wa Buhari kan tura dakaru na musamman 100 Zamfara

    Gwamnan jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Najeriya Bello Matawalle ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari kan bayar da umarnin aika Dakarun kar ta kwana na musamman don yaki da ‘yan bindiga a jihar.

    Gwamnan ya bayyana hakan ne a yau Alhamis lokacin da ya karbi baukuncin babban kwamandan runduna ta takwas da sojin Najeriya da ke Sokoto da kwamandan rundunar hadin gwiwa na yankin arewa maso yammacin kasar na rundunar Hadarin Kaji.

    Gwamnan y ace ya ji dadin aike wa da dakaru na musamman har 100 da shugaban kasa ya yi jihar Zamfara, yana mai cewa matakin zai kawo karshen ta’addancin da ake yi a jihar.

    Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da bai wa rundunar sojin Najeriya dukkan hadin kan da take bukata don magance matsalar rashin tsaro.

  8. Jam'iyyar PDP ta yi sabon shugaba

    Kwamitin amintattun babbar jam`iyyar hamayya a Najeriya, wato PDP ya amince da mukaddashin shugaban jam'iyyar, Elder Yemi Akinwonmi, wanda ya maye gurbin shugaban jam'iyyar Uche Secondus, wanda kotu ta dakatar da shi.

    Kwamitin dai ya yi zama ne sakamkon kokarin da yake yi na sama wa jam`iyyar mafita daga cikin rigingimun shugabancin da ya dabaibaye ta.

    Ƴan kwamitin da dama sun halarci taron, ciki har tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, wanda cikin raha ya musanta rade-radin da ake yi cewa ya tare Dubai tun watan Satumban bara.

    Ya ce ya yi bulaguro ne saboda ya koma makaranta.

    Kuma a yanzu ya kammala karatunsa a watan Mayun da ya wuce a jami'ar Cambridge, inda ya yi digiri na biyu a kan huldar kasa da kasa. Saboda haka yana faran cikin sake dawowa gida.

    Kuma ya shaida cewa ba zai sake tafiya Dubai ba.

    Kwamitin amintattun dai ya ce zai ci gaba da yin wani zaman gobe juma'a, inda zai fadada zauren domin halartar gwamnoni da wasu gaggan 'yan jam'iyyar da nufin share hanyar taron majalisar koli ta zartarwar jam'iyyar PDP da za a yi jibi Asabar.

  9. Mutum 60 ne suka mutu a hare-haren bam na filin jirgin saman Kabul

    A kalla mutum 60 ne suka mutu,140 kuma suka jikkata a hare-haren bam din da aka kai a filin jirgin saman Kabul, a Afghanistan, a cewar wani babban jami'in lafiya.

    Ma'aikatar tsaron Amurka Pentagon ta tabbatar da mutuwar wasu sojojin kasar a harin bam din da aka kai a filin jirgin saman Kabul, baya ga wasu fararen hula da su ka rasa rayukansu.

    Jami'ai sun ce bama-bamai biyu ne su ka fashe -- na farko a bakin kofar shiga filin jirgin mai suna Abbey Gate - wurin da aka ajiye sojojin Amurka da na Birtaniya domin kula da cincirindon dubban masu son ficewa daga kasar -- na biyun kuwa ya tashi ne a otel din Baron da ke kusa.

    Daya daga cikin bam din na kunar bakin wake ne, wanda aka tayar sa'o'i bayan da Amurka da kawayenta suka rika yin gargadin aukuwar harin ta'addanci daga kungiyar IS.

  10. NNPC ya ci ribar farko cikin shekaru 44 a Najeriya

    Kamfanin mai na Najeriya, NNPC ya samu ribar farko a tarihi cikin shekaru 44, kamar yadda gwamnatin ƙasar ta shaida.

    Shugaba Muhammadu Buhari, wanda shi ne babban ministan harkokin fetur, ya ce wannan wani ɓangare ne a kokarinsu na dabarun tattali.

    A shekara ta 2020 NNPC ya ci ribar dala miliyan 700.

    A shekarun baya kamfanin ya fuskanci gagarumar asara.

    Har yanzu dai babu cikakun bayanai kan yada NNPC ya samu irin wannan riba a lokacin da tattalin arzikin kamfanin ke taggayara saboda sauyin farashi a kasuwar duniya da annobar korona ta haifar.

    Sanarwar shugaba Buhari na zuwa ne adaidai lokacin da gwamnatinsa ke kokarin rusa NNPCn domin bai wa yan kasuwa damar shiga harkar da nufin samar da haɓɓaka

  11. Najeriya na gab da soma amfani da fasahar 5G

    Shugaban hukumar sadarwa ta NCC a Najeriya, Umar Garba Danbatta ya ce gwamnati ta shirya domin kaddamar da tsarin soma amfani da fasahar 5G a faɗin ƙasar.

    Tuni dai wasu ƙasashen duniya irinsu Australia da China da New Zealand da Thailand suka soma amfani da fasahar, bayan wuce 4G da har yanzu wasu ƙasashen ke kai.

    A lokacin wani taro a Abuja, Danbatta ya ce NCC a shirye take domin soma amfani da fasahar a fadin ƙasar.

    Ya kuma yi tsokaci kan gasar da ake sake samu tsakanin kamfanonin sadarwa, abin da ya ce ya taimaka wajen saukaka tsadar data a ƙasar.

  12. 'Maharan NDA sun kutsa gidajen sojoji biyar a lokacin harin'

    Ƴan bindiga da suka kai hari makaranta sojoji ta NDA a Kaduna, sun kutsa gidajen sojoji biyar a lokacin harin.

    Wannan na kunshi cikin wani kundin bayanai da ya shiga hannun jaridar Daily Trustta Najeriya.

    A cewar binciken sirri, maharan sun ci karansu ba babbaka saboda sojoji ba su amsa kirar ankararwa da aka yi musu ba.

    Harin na ranar Litinin da ya haifar da ce--ce-ku-ce kan sake tabarbarewa lamuran tsaro a Najeriya

    An kashe manyan sojoji biyu, da garkuwa da wani Manjo a harin.

    Sannan akwai jami'in da aka jikkata wanda yanzu haka ke samun kulawa a asibiti.

    Shugaban hafsoshin sojin Najeriya, Lucky Irabor ya ce ba zasu raga ba wajen zakulo wadanan mahara da kawo karshen hare-haren ƴan bindiga a fadin ƙasar.

  13. 'Mayakan Tigray sun kashe mutum 35 a yankin Amhara'

    Jami'ai a yankin Amhara na kasar Habasha sun ce mayaka daga yankin Tigray mai makwabtaka sun kashe akalla mutum talatin da biyar kuma sun wawashe dukiyar jama'a a yankin Gondar ta Kudu.

    Mazauna garin Nefas Mewcha sun ce mutum talatin aka kashe cikin kwanakin da aka kwashe ana fada tsakanin mayakan Tigray da dakaran gwamnatin tarayya da na gwamnatin yankin - tare da taimakon wasu kungiyoyin 'yan sa-kai.

    Sun kuma ce an lalata gine-ginen gwamnati da asibitoci da makarantu da bankuna har ma da gidaje.

    Baya ga matsalar yakin basasan, akwai kuma matsalar yunwa wadda ke karuwa saboda rashin hanyoyin raba abinci da kayan agaji, kuma kungiyar TPLF ta ce tasirin matsalar zai dade yana shafar mazauna yankin.

    Kawo yanzu kungiyar ta TPLF wadda ke fada da dakarun gwamnatin kasar na tsawon wata goma ba ta ce ko ita ce ke da alhakin kai wadannan hare-haren ba.

  14. Abin ya sa ba a gani na a taron PDP - Atiku

    Tshohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar ya ce ya je karutun digiri na biyu ne a ƙasar waje, shi ya sa ba a ganin sa a tarukan jam’iyyar PDP.

    Atiku ya bayyana haka a wajen taron kwamitin amintattun jam’iyyar da ake yi a halin yanzu.

    Ya ce ya yi digiri na biyu ne a kan harkokin kasa da kasa, kuma ya kammala karatun nasa, saboda haka a nan gaba ba zai na yawaita bulaguro ba.

  15. Iyakokin Afghanistan na ƙara cika da jama'a

    Dubban mutane ne su ka taru a kan iyakar Afghanistan da Pakistan, kuma yawansu sai karuwa yake yi a kullum.

    Pakistan ta bar kofofin da ke kan iyakarta a kusa da garin Spin Boldak wanda ya ba wasu 'yan Afghanistan damar tsallakawa. Amma an rufe daya daga cikin manyan wuraren da ake tsallakawa a Torkham.

    Babu wanda ya san halin da ake ciki a sauran kan iyakokin Afghanistan da kasashen da ke makwabtaka da ita.

    Tun da Taliban ta sanar da cewa ta umarci mata su daina zuwa aiki domin rashin tsaro, BBC ta tattauna da wasu mata masu aiki a Afghanistan wadanda ke cewa yanzu su na son barin kasar.

    Sai dai akwai wadanda ke komawa Afghanistan, inda wani cikinsu ke cewa ya yi imani mulkin Taliban zai kawo kwanciyar hankali a kasar.

  16. Ana tattarawa 'yan fashin daji a Zamfara diyyar kashe dan uwansu da aka yi

    Mazauna wasu kauyukka tara a kudancin jihar Zamfara sun tattara kudade domin biyan 'yan fashin daji diyyar dan uwansu da 'yan banga suka kashe a yankin domin kauce wa hare-hare daga garesu.

    Rahotanni sun ce dangin mutumin da aka kashe sun ce sun yafe kisan da aka yi masa amma dole ne a biya kudaden da suka bata bayan kashe shi da kuma babur dinsa nan da Jibi Assabar.

    Kan haka ne sarakunan gargajiya a yankin suka umarci ko wane kauyen ya kawo Naira dubu 300 domin fansar rayukansu.

  17. Za a haramta kiɗa ƙarƙashin shugabancin Taliban - Zabihullah Mujahid

    Kakakin Taliban ya ce za a haramta kiɗa karkashin sabuwar gwamnatinsu.

    Zabihullah Mujahid ya shaida wa wata jaridar Amurka The New York Times cewa "kiɗa haramun ne a Musulunci.. amma mai makon matsa wa mutane su daina za mu fahimtar da su, su gane hakan ba daidai ba ne."

    A shekarun 1990 lokacin da Taliban ke mulki an haramta kallon Talabijin da zuwa sinima da kuma yin kiɗa, kuma kin biyayya ga hakan yakan janyo a hukunta mutum.

    Amma bayan hambarar da su daga mulki, kiɗa ya dawo kamar wani abun yayi.

    An kafa wata cibiya ta Afghanistan da ke koyar da kida kuma kusan duk shekara akan shirya bikin kida a kasar lokaci zuwa lokaci.

    Cibiyar na da wata tawagar mata da ke yin kida a ciki da wajen kasar.

  18. Najeriya ta karbi 'yan gudun hijirar Kamaru 73,000

    Hukumar kula da 'yan gudun hijara da 'yan cirani ta Najeriya ta ce ta karbi 'yan gudun hijarar Kamaru tare da yi musu rijisata su 73,000.

    Jaridar DailyTrust ta ruwaito shugabar hukumar Imaan Sulaiman-Ibrahim, ce ta bayyana hakan a ranar Laraba a wani taron karawa juna sani game da yi wa 'yan gudun hijira da masu neman mafaka rijista a Abuja.

    Ta ce "Tikicin siyasar Kamaru ya ki ci ya ki cinye wa tun 2016, kuma hakan ya janyo karuwar cin zarafin dan adam tare da asarar rayuka da dukiyoyi musamman a yankuna biyu na arewa maso yamma da kuma kudu maso yamma na kamaru.

    Wani babban koma baya da rikicin ya haifar shi ne yadda aka rika samun karuwar 'yan cirani daga Kamaru zuwa Najeriya amma a matsayin 'yan gudun hijira. wadanda ya zuwa watan Yuni 2021 munyi wa 73,000 rijista,

    A gefe guda kuma, akan samun 'yan gudun hijirar da ba su gaza 3,000 gada Kamaru suna shiga Najeriya a duk mako.

    Shugaban ta kuma jaddada bukatar da ake da ita ta ganin an kare sansanonin 'yan gudun hijirar tana cewa da zarar an gaza hakan, to zai iya zama koma baya ga harkokin tsaron Najeriya.

  19. Labaran duniya cikin minti daya

    • Rahotanni daga Zambia na cewa sabon shugaban kasar Hakainde Hichilema ba zai shiga fadar gwamnatin kasar ba, zai ci gaba da aiki daga gidansa.

    Wannan kuwa na zuwa ne duk da cewa shugaba Edgar Lungu zai tattara nasa ya nasa ya fice a wannan makon.

    • Yau hukumar kwallon kafa ta Turai za ta raba jadawalin gasar Champions na 2021/22 wanda za a yi a birnin Istanbul na Turkiyya.

    Beşiktaş da za ta wakilci Turkiyya a gasar da samu kanta cikin kwarya ta hudu ta kungiyoyin da za su buga Champions din.

    • A yau Alhamis ne ake sa ran binne tsohon shugaban Chadi Hissène Habré a Dakar babban birnin Senegal.

    Tsohon shugaban ya mutu ne a gidan yari a ranar Talata sakamakon annobar korona.

    • Gwamnan Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya Bello Matawalle ya yi kira da a sanya dokar ta-baci a duka jihohin arewacin kasar saboda matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin.

    Ya yi wannan kira ne yayin wata tattaunawarsa da mataimakin shugaban 'yan sanda da ke lura da shiyya ta 10 da ke Gusau Ali Janga.

    • A fagen wasanni PSG na son Real Madrid ta biya yuro miliyan 220 idan har tana son dan Kylian Mbappe.

    Pep Guardiola zai bar Manchester City idan kwantiraginsa ya kare bayan kakar 2022-23.

  20. Adadin mutanen da suka mutu a ambaliyar ruwa a Venezuela ya kai 20

    Adadin mutanen da suka mutu a yayin bala'in ambaliyar ruwan da rutsa da su a Andes dake Venezuela ya karu zuwa ashirin.

    Gwamnan jihar da lamarin ya fi kamari, Ramon Guevara, ya ce gidaje sama da dubu sun lalace kuma har yanzu ana ci gaba da neman mutane goma sha bakwai.

    Hotunan da aka yada a kafafen sada zumunta sun nuna yadda motoci ke mamaye tituna, da gine -gine da wuraren kasuwanci da ke cike da laka, da duwatsu da yashi a kan hanyoyi.

    Yankuna da dama a jihar sun rasa wutar lantarki yayin da injiniyoyi ke aikin dawo da ita.