Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mayaƙan ISWAP da Boko Haram sun kashe kansu a wani bata-kashi

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Real Madrid ta miƙa tayin yuro miliyan 160 don sayen Mbappe

    Real Madrid ta miƙa tayin yuro miliyan 160 don sayen ɗan wasan gaba Kylian Mbappe daga Paris St-Germain.

    Ɗan wasan mai shekara 22 da ya lashe Kofin Duniya, ya koma PSG a 2017 kan kuɗi da suka kai fan miliyan 165 wanda kuma yarjejeniyarsa za ta zo ƙarshe a Yunin 2022.

    Mbappe ya ci wa PSG ƙwallo 133 cikin wasa 174 da ya buga mata, inda ya lashe kofin gasar Ligue 1 uku da French Cup uku.

    Real Madrid wadda ake bi bashin da ya kai kusan fan biliyan ɗaya, David Alaba kaɗai ta ɗauka a wannan kakar daga Bayern Munich kuma kyauta.

    Ganin cewa Sergio Ramos da Raphael Varane waɗanda ke ɗaukar albashi mai yawa sun bar ƙungiyar, Real na ganin za ta iya sayo Mbappe ba tare da matsalar kuɗi ba.

    Sai dai babu cikakken bayani kan yadda za a tsara biyan kuɗin sannan kuma har yanzu PSG ba ta ce komai kan tayin ba tukunna.

  2. 'Yan sandan Ghana za su binne gawar mutum 200 a ƙabari ɗaya

    'Yan sanda a Ghana sun bayyana wa 'yan ƙasar cewa za su binne gawar mutum 200 lokaci a ƙabari ɗaya na mutanen da ba a gane su ba sannan kuma danginsu ba su neme su ba.

    Za a fara aikin binne su daga "ƙarshen makon nan", a cewarsu cikin wata sanarwa ranar Litinin.

    An ɗauki matakin ne domin rage cunkoso a wuraren ajiye gawa na 'yan sandan ƙasar, kamar yadda wani jami'i ya shaida wa BBC.

    Gawarwakin waɗanda suka taru a tsawon wata shida, sun haɗa da na mutanen da aka kashe a tituna da kuma talakawa da suka rasu a kan hanyoyi.

    Kazalika, akwai waɗanda aka kashe su bisa zalunci amma aka kasa gane su da kuma waɗanda suka mutu a gadon asibiti amma 'yan uwansu ba su neme su ba.

  3. Jihohi bakwai a Najeriya ka iya fuskantar ambaliyar ruwa a makon nan

    Cikin kwana uku masu zuwa, akwai yiwuwar za a samu ruwan sama "mai ƙarfin gaske" a jihohin Katsina da Jigawa da Neja da Kogi da Nasarawa da Benue da Cross River, a cewar hukumar kula da yanayi ta Najeriya NiMet.

    Kazalika, akwai yiwuwar a fuskanci "matsakaici zuwa mai yawa" na ruwan a wasu yankunan Jihohin Sokoto da Kano da Zamfara da Bauchi da Ebonyi da Enugu da Abia da Akwa Ibom daga Laraba zuwa Juma'a, kamar yadda ta bayyana.

    A gefe guda kuma, za a iya fuskantar "matsakaicin ruwan sama" a yankunan jihohin Rivers da Kwara da Delta da birnin Abuja da arewacin Kaduna.

    "Sakamakon hasashen ruwan sama kamar da bakin ƙwarya da za a samu cikin kwana uku masu zuwa, akwai yiwuwar a samu ambaliyar ruwa a kan tituna da gidajen da ke cikin kwari da ƙoramu da kuma koguna," a cewar NiMet cikin wani rahoto.

    Tuni wasu jihohi suka fuskanci ambaliyar ruwan a Najeriya, inda ta yi ajalin wasu sannan ta raba wasu da muhallansu.

  4. Korona ta kashe ƙarin mutum biyar a Najeriya, 655 sun kamu

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 655 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Talata.

    Rahoton hukumar ya nuna cewa an samu mutum biyar da cutar ta yi ajalin su har wa yau.

    A jihohi 14 ka samu sabbin mutanen da suka kamu a Talatar. Su ne:

    • Lagos-288
    • Rivers-188
    • Oyo-64
    • Akwa Ibom-31
    • FCT-28
    • Ekiti-21
    • Edo-17
    • Bayelsa-11
    • Kaduna-7

    Jumillar mutanen da suka kamu da korona a Najeriya sun kai 188,243, sai kuma 169,035 da suka warke. Kazalika, akwai kuma mutum 2,281 da suka mutu.

  5. Barka

    Maraba da shigowa shafinmu na labarai kai-tsaye.

    Umar Mikail ne zai kasance da ku a wannan hantsi na Laraba - ta bawa ranar samu.

    Ku biyo mu don samun rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.