Taliban: Yadda filin jirgi na Kabul ya wayi gari
Dubban mutane da ke son ficewa daga Afghanistan na can danƙam a kusa da filin jirgi na Kabul babban birnin Afghanistan.
Aƙalla mutum 20 ne suka mutu sakamakon harbe-harbe da kuma turmutsitsi tun daga makon da ya gabata.
An kwashe mutum fiye da 10,000 a ranar Litinin kaɗai, amma lokaci na ƙurewa yayin da wa'adin 31 ga Agusta ke ƙaratowa a matsayin lokacin da za a kammala aikin.
Wani jami'in NATO ya faɗa wa Reuters cewa ana gudanar da aikin ne "a yanayin yaƙi" yayin da dakarun ƙasashen waje ke ta ƙoƙarin kauce wa tsawaita wa'adin wanda aka ƙulla yarjejeniya da Taliban tun farko.
Taliban ta ce za ta ɗauki mataki matuƙar ƙasashen Yamma suka wuce wa'adin na 31 ga Agusta. Sai dai ana sa ran ƙungiyar G7 ta ƙasashe mafiya girman tattalin arziki za ta nemi Amurka ta tsawaita wa'adin a yau Talata.