Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kotun Musulunci ta yankewa ƴar Kannywood hukunci kan yaɗa 'hoton batsa'

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Taliban: Ina 'yan gudun hijira za su tafi bayan Taliban ta karbe iko?

    A yanzu dai babu takamaiman adadin 'yan gudun hijirar da ke barin ƙasar, amma zuwa yanzu an kwashe mutum fiye da 30,000 daga ƙasar.

    Ƙungiyar Taliban ta karbe iko da duka iyakokin Afghanistan da maƙotan ƙasashe, kuma mayakan sun ce ba sa son 'yan kasar su fice.

    Rahotanni na cewa 'yan kasuwa ne kawai da wadanda ke da shaidar tafiya ake bari su tsallaka.

    "Mafi yawan 'yan Afghanistan ba a bari su bar ƙasar ta hanyoyin da aka saɓa," kamar yadda kakakin shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) ya bayyana ranar Juma'a. "Ya zuwa yanzu mutanen da suka fi zama cikin haɗari ba su da hanyar barin kasar nan."

    Amma wasu da yawa na ta kokarin ficewa daga kasar ta hanyoyi daban-daban.

    Da dama daga cikin 'yan kasar sun haure zuwa Pakistan jim kadan bayan Taliban ta karɓe iko, yayin da ake bayar da rahoton sama da 1,500 na daban sun tsallaka zuwa Uzbekistan kuma duka suna zaune a tantunan da aka kafa kusa da kan iyaka.

    A Kabul, dubban mutane ne suke ta nufar filin jirgi, kuma shi kaɗai ne ke aiki a fadin kasar baki daya a wani yunkuri da ake yi na neman ficewa daga kasar.

  2. Taliban: Faɗa ya ɓarke a wajen filin jirgi na Kabul

    Wani ƙazamin faɗa ya ɓarke tsakanin wasu 'yan bindiga da jami'an tsaro a ƙofar shiga filin jirgi na Kabul babban birnin Afghanistan, a cewar rundunar sojan Jamus.

    An kashe wani mai gadi ɗan Afghanistan sannan aka raunata uku a fafatawar da sojojin Jamus da na Amurka suka shiga.

    Filin jirgin ya zama matattarar rikici tun mako ɗaya da ya wuce bayan Taliban ta ƙwace iko da Kabul, yayin da dubban 'yan ƙasashen waje da na Afghanistan ke rububin tserewa daga ƙasar.

    A ranar Litinin wani jami'in ƙungiyar NATO ya faɗa wa Reuters cewa aƙalla mutum 20 ne suka mutu a filin jirgin tun daga ranar Lahadin wancan makon.

  3. Taliban: Birtaniya na son Amurka ta tsawaita wa'adin kwashe sojojinta daga Afghanistan

    Ana sa ran Firanministan Burtaniya Bosris Johnson zai bukaci shugaba Joe Biden na Amurka ya jinkirta kwashe sojojin Amurkar har sai an kammala kwashe fararen hula daga Afghanistan.

    A ranar Talata ne Mista Johnson zai gabatar da wannan bukata a taron gaggawa da shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki ta G7 za su yi ta intanet.

    Wakilin BBC ya ce taron na G7 zai tattauna makomar Afghanistan a shekaru masu zuwa amma kuma za a tattauna batun ficewar sojojin.

    Kasa da kwana 10 suka rage Amurka ta kammala kwashe sojojinta daga Afghanistan.

  4. Cutar korona ta kashe ƙarin mutum takwas a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 388 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Lahadi.

    Kazalika, rahoton na NCDC ya nuna cutar ta yi ajalin ƙarin mutum takwas.

    Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranar Lahadi:

    • Lagos-166
    • Akwa Ibom-88
    • Rivers-76
    • Oyo-15
    • Edo-12
    • Benue-11
    • Delta-7
    • FCT-4
    • Ogun-4
    • Kaduna-2
    • Gombe-1
    • Nasarawa-1

    Jumillar adadin mutanen da suka kamu da cutar korona a Najeriya sun kai 187,023, sai dai 168,455 sun warke. Akwai kuma mutum 2,268 da suka mutu.

  5. Maraba

    Kun shigo shafin labarai kai-tsaye, inda za mu kawo muku rahotanni na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.

    Umar Mikail ne ke fatan kun wayi hantsin Litinin lafiya.