Bankwana
Masu bibbiyarmu a wannan shafin da haka zamu diga aya sai kuma gobe Talata idan Allah ya tashe mu da rai da lafiya. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a kwana lafiya.
Ga wasu daga cikin muhimman labaran da muka kawo muku a yau
- Ƴan bindiga su kashe mutane da garkuwa da 50 a Zamfara
- Kotun Musulunci ta yankewa ƴar Kannywood hukunci kan yaɗa 'hoton batsa'
- An ceto sama da mutum 100 daga hannun mayakan jihadi a Mozambique
- Kotu ta umarci likitoci su janye yajin aiki a Najeriya
- Matar tsohon shugaban Najeriya ta rasu
- Ƴan Ethiopia na zanga-zanga kan zargin cin zarafin da Saudiyya ke yi wa baƙi
- An samu raguwar yawan mutanen da ake kashewa a Najeriya – Bincike
- Ƙungiyar Fulani ta miƙa waɗanda ake zargi da fashi ga 'yan sanda
- Shugabar Tanzaniya na shan suka kan muzanta ƴan wasan ƙwallo ƙafa mata
- An ɗaure tsohon mininsta shekara 12 kan laifin rashawa a Indonesia
- 'Yan sandan Najeriya sun kama mutum huɗu da zargin fashi












