'Yan bindiga sun sace dagaci a Jihar Zamfara

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Buhari Muhammad Fagge

  1. Nan za mu rufe wannan shafin sai kuma gobe Idan Allah Ya kai mu

  2. Amurka ta fara amfani da jiragen kasuwanci don kwaso mutanenta daga Afghanistan

    BBC

    Amurka ta bayar da umarnin amfani da jiragen dakon fasinjoji goma sha takwas cikin gaggawa don kwaso mutane daga Afghanistan.

    Wata sanarwa da ta fito daga ma'aikatar tsaron Amurkar ta ce jiragen ba za su je Kabul ba amma za a yi amfani da su wajen ɗaukar mutanen da aka ɗauke daga Kabul aka kai su wasu sansanonin sojojin Amurka a Gabas ta Tsakiya.

    Haka kuma, sanarwar ta ce wannan zai ba jiragen soji damar mayar da hankali kan dakon mutane daga Kabul zuwa sansanonin.

  3. 'Mutum 2,200 ne suka mutu a girgizar kasar Haiti ya zuwa yanzu'

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumomi a Haiti sun ce kawo yanzu mutum dubu biyu da ɗari biyu ne aka tabbatar sun mutu a girgizar ƙasar da ta aukawa ƙasar a farkon wannan watan.

    Har yanzu ana aikin nema da ceton mutane kusan ɗari uku da hamsin da ba a san inda su ke ba.

    Lalacewar tituna da zaftarewar ƙasa sun janyo tsaiko a ayyukan agaji a ƙasar.

  4. NDLEA ta kama wani 'dilan' miyagun kwayoyi a coci

    NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA

    Hukuamar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi sun kama wani mutum da take nema ruwa a jallo wanda take zargi da fataucin miyagun kwayoyi mai suna Stephen Afam Ikeanyionwu, a wata coci a yankin Ojodu, a yankin Ikeja da ke Lagos a ranar Lahadi.

    Kakakin hukumar Femi Babafemi ne ya bayyana hakan, cikin wata sanarwa inda ya ce Ikeanyionwu dama ana nemansa ruwa a jallo saboda kokarin da ya yi na fitar da hodar iblis da ta kai nauyin kilogiram 69.65, da wasu sauran muggan kwayoyi da zai kai Burtaniya ta karkashin NAHCO a filin jirgin Murtala Muhammed da ke Legas.

    Babafemi ya ce mutanensu sun rika bibiyar wannan mutum a ranar lLahadin 15 ga watan Agusta 2021 har zuwa wata coci da ke Ojodu inda aka samu nasarar kama shi lokacin da ya shiga yin ibada.

    NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA

    NDLEA

    Asalin hoton, NDLEA

  5. 'Yan bindiga sun kashe mutum 12 a Jihar Katsina

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan bindiga sun kashe mutum 12 tare dajikkata wasu shiga na daban a wani hari da suka kai kauyen Duba a karamar hukumar Batsari da ke jihar Katsina a arewacin Najeriya.

    Jaridar The Nationcewa karamar hukumar Batsari wadda na cikin kauyukan da 'yan bindiga suka fi yi wa karan tsaye a Jihar Katsina na kusa da dajin Rugu ne mai cike da hadari.

    'Yan sandan jihar katsina sun tabbatar da faruwar lamarin.

    Kakakin 'yan sandan Isa Gambo ya shaida wa manema labarai cewa 'yan bindigar sun shiga Batsari su kusan 300 dauke da makamai da misalin karfe 8:45 na maraicen Asabar.

  6. Lukaku ya ci kwallo na 114 a Premier League a kan Arsenal

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Chelsea ta je Gunners ta kuma yi nasara da ci 2-0 a wasan mako na biyu a gasar Premier League da suka fafata a Emirates ranar Lahadi.

    Kungiyar ta Stamford Bridge ta ci kwallon farko ta hannun Romelu Lukaku a minti na 15 da fara wasa, sai Reece James ya kara na biyu saura minti 10 su je hutu.

    Romelu ya ci kwallon sa na farko a fafatawa ta 16 a kaka tara da ya yi a Stamford Bridge, wadda ya fara buga mata tamaula cikin watan Agustan 2011.

    Kuma kwallon da Lukaku ya zura a ragar Arsenal ya zama na 114 da ya ci a gasar Premier a West Brom da Everton da kuma Manchester United.

    Wannan bajintar ya sha gaban Ian Wright, yana cikin 'yan wasa 20 da suka ci kwallaye da yawa a tarihin Premier League.

    Haka kuma Lukaku ya zama na takwas a jerin wadanda ba 'yan kwallon Ingila ba da suka zura kwallo sama da 50 gida da waje a babbar gasar ta Ingila.

    Shi kuwa Reece James ya zama na biyu a Chelsea da ya ci kwallo ya kuma bayar aka zura a raga a gidan Arsenal a Premier League, bayan Juan Mata cikin watan Satumbar 2012.

    Lukaku mai shekara 28 ya koma Chelsea daga Inter Milan a makon jiya kan fam miliyan 97.5 a karo na biyu da zai buga mata tamaula, bayan zaman da ya yi tsakanin 2011 zuwa 2014.

  7. Rashford ya koma yin atisaye a Manchester United

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Dan wasan Manchester United, Marcus Rashford ya koma karbar horo a sansanin kungiyar da ke Carrington.

    Kocin United, Ole Gunnar Solskjaer ya ce dan kwallon na murmurewa daga aikin da likitoci suka yi masa a raunin da ya ji a kafada

    Dan wasan tawagar Ingila ya fada a makon jiya cewar likitoci sun yi nasarar yi masa tiyata a kafada a raunin da ya ji a lokacin atisayen tun kan fara kakar bana.

    Raunin ne ya bai wa dan kwallon mai shekara 23 cikas da bai buga wa tawagar Ingila karawa da yawa a Euro 2020 ba, wanda ya barar da fenariti a wasan karshe da Italiya a Wembley.

    Bayan da ya ji raunin Solskjaer bai fayyace lokacin da zai yi jinya ba, illa dai wasu jaridun Birtaniya sun yanke wa'adin mako 12, kafin ya koma taka leda.

    Ranar Asabar Manchester United ta tashi 1-1 a gidan Southampton a wasan mako na biyu da fara Premier League kakar 2021-22 a St Mary.

  8. Taliban za su fara neman abokan gabarsu ta hanyar zanen hannu

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Wani tsohon sojin ruwan Amurka Peter Kieman ya ce "muna bi kauye-kauye a Afghanistan muna shigar da bayanan munatane da kuma zanen hannunsu."

    Ya ce da wata na ura mai tsawon inci 12 da kuma fadin inci shida ana tantance zanen 'yan yatsun mutane da kuma idanunsu. kuma duk mun dauki hitunansu ta haka,"

    'Yan kwanakin nan da suka gabata Peter yana fama da aiki mai yawa. Lokacin da yake aiki a Afghanistan yana da masu yi masa fassara su 12.

    Suna taimaka masa wajen yin magana da mutane. kuma lokacin da yake bayyana wannan zance mafi yawan wadanda ya yi aiki da su suna Afghanistan ya ma yi ta kokarin ji dga gare su.

    A gaskiyar lamari zai fi kyau ga duk mutumin da ke aiki da jami'an tsaron Amurka ya gaggauta barin kasar nan da nan.

  9. 'Yan bindiga sun sace dagaci a Jihar Zamfara

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    'Yan bingida a Jihar Zamfara da ke arewacin Najeriya sun kai hari kauyen Adabka da ke karamar hukumar Bukkuyum tare da sace dagacin yankin Alhaji Nafi'u Shehu.

    Wani mazaunin kauyen ya shaida wa jaridar The PUNCHcewa da misalin karfe 12 da rabi na ranar Asabar ne 'yan bindigar suka dirarwa fadar dagacin tare da masu yi masa hidima.

    A cewarsa bayan sace dagacin sai da suka dauki sa'o'i a kauyen suna abin da suka ga dama.

    Wannan dai na zuwa ne mako guda bayan da aka janye 'yan sandan da ke bayar da tsaro a yankin da mako guda.

    Sun tuntubi 'yan sanda domin jin karin bayani, amma sai suka ce za su kira daga baya.

  10. Shugaban Rasha Putin ya soki Amurka da Turai kan kwashe 'yan Afghanistan

    Vladimir Putin

    Asalin hoton, Reuters

    Shugaban Rasha Vladimir Putin ya soki Amurka da ƙasashen Yamma saboda sun buƙaci ƙasashen Asiya su ɗebi 'yan gudun hijirar Afghanistan ba tare da biza ba.

    Kamfanin labarai na Reuters ya ruwaito Putin na bayyana haka ne a wurin wani taron siyasa.

    Ya ce: "Abokan aikinmu na Yamma na son ƙawayenmu na Nahiyar Asiya su karɓi 'yan gudun hijira (na Afghanistan) har sai sun gama sama musu biza a Amurka da sauran ƙasashe.

    "Shin hakan na nufin za su iya aika su zuwa waɗannan ƙasashe maƙotanmu ba tare da biza ba - amma su ba sa so su karɓe su ba tare da bizar ba?"

    Amurka na ci gaba da tattaunawa da wasu ƙasashe don su bai wa 'yan Afghanistan mafaka ta ɗan lokaci.

    Duk da cewa Rasha na karɓar 'yan ƙasashen Asiya tsofaffin mamba a Tarayyar Soviet ba tare da biza ba amma ya koka cewa 'yan bindiga ka iya amfani da wannan damar su shiga ƙasarsa.

  11. Taliban: Firaministan Birtaniya zai tattara kan shugabannin G7 game da Afghanistan

    Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce zai tattaro kan shugabannin ƙungiyar ƙasashe mafiya girman tattalin arziki ta G7 don tattaunawa kan rikicin Afghanistan.

    Cikin wani saƙon Twitter, Mista Johnson ya ce "abu ne muhimmi ƙasashen duniya su haɗa kai wajen tabbatar da kwashe mutane sannan su kare afkuwar bala'i tare da taimaka wa 'yan Afghanistan don samun alfanun nasarar da aka samu cikin shekara 20".

    Birtaniya ce ke jagorancin ƙungiyar G7 a yanzu - sauran mambobi sun ƙunshi Canada, Faransa Jamus, Italiya, Japan, Amurka.

    Kauce wa X
    Ya kamata a bar bayanan X?

    Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

    Gargadi: BBC ba za ta dauki alhakin bayanan da aka wallafa a shafukan da ba nata ne ba.

    Karshen labarin da aka sa a X

  12. 'Yan fashi sun sako ɗaliban Bethel Baptist 15 bayan an biya kuɗin fansa

    Bethel Baptist

    Asalin hoton, Daily Trust

    'Yan fashin daji sun saki ɗalibai 15 daga cikin waɗanda suka sace a sakandaren Bethel Baptist ta Jihar Kaduna.

    Shugaban ƙungiyar Kiristoci ta CAN reshen Jihar Kaduna, Rabaran John Hayab, ya shaida wa BBC Hausa cewa an saki ɗaliban ne ranar Asabar da dare bayan an biya kuɗin fansa.

    Ya ce har yanzu akwai yara 65 a hannun 'yan bindigar, yayin kusan 53 suka kuɓuta. A ranar 25 ga Yuli aka saki 28 daga cikinsu.

    'Yan bindigar sun sace yaran ne maza da mata a ranar 5 ga watan Yuli bayan sun afka makarantar tasu da ke kan Titin Kaduna zuwa Kachia a Ƙaramar Hukumar Chikun.

  13. Taliban: 'Aƙalla mutum 20 ne suka mutu a filin jirgi na Kabul'

    Kabul

    Asalin hoton, Other

    Aƙalla mutum 20 ne suka mutu cikin kwana bakwai da suka wuce a ciki da wajen filin jirgi na Kabul babban birnin Afghanistan, a cewar wani jami'in ƙungiyar NATO.

    "Rikici a wajen filin jirgi na Kabul abin takaici ne, burinmu shi ne mu kwashe dukkan 'yan ƙasashen waje cikin gaggawa," kamar yadda jami'in wanda ya nemi a ɓoye sunansa ya faɗa wa Reuters.

    Tun daga Lahadi da ta gabata, mutane sun cika a filin jirgin, abin da ke kawo tsaiko ga ayyukan kwashe Amurkawa da sauran ƙasashe har ma da 'yan Afghanistan da ke son barin ƙasar.

    Ya ƙara da cewa: "Dakarunmu na bakin ƙoƙarinsu wajen kauce wa duk wata hatsaniya da mayaƙan Taliban a kusa da filin jirgin."

    Kwana shida kenan da Taliban ta ƙwace iko da birnin Kabul, abin da ya sa ƙasashen ke rububin kwashe mutanensu da kuma 'yan Afghanistan da suka yi aiki tare da su.

  14. Taliban: 'Yar Afghanistan ta haihu a cikin jirgi

    Sojojin Amurka

    Asalin hoton, @AirMobilityCmd

    Wata uwa 'yar Afghanistan ta haifi 'yarta 'yan mintuna bayan sauka a sansanin sojan saman Amurka na Ramstein da ke Jamus ranar Asabar.

    Cikin wani saƙon Twitter, rundunar sojan Amurka ta ce matar ta fara naƙuda ne a cikin jirgin soja na C-17 ana tsaka da tafiya bayan sun tsere daga ƙasar sakamakon ƙwace mulki da ƙungiyar Taliban ta yi.

    Jirgin ya taso ne daga wurin da ya yi zango a Gabas ta Tsakiya zuwa Jamus.

    "Matuƙin jirgin ya sassauto ƙasa domin ya ƙara yawan iska a cikinsa, abin da ya taimaka aka ceci rayuwar uwar jaririyar," a cewar saƙon.

    Ya ƙara da cewa an kai uwar da 'yarta wani asibiti da ke kusa jim kaɗan bayan sun sauka kuma suna cikin ƙoshin lafiya.

    Ya zuwa yanzu, an kwashe dubban 'yan Afghanistan daga ƙasar zuwa ƙasashen Turai da na Gabas ta Tsakiya saboda gudun mulkin Taliban.

  15. Isra'ila ta kai hare-hare a birnin Gaza

    Gaza

    Asalin hoton, AFP

    Isra'ila ta kai hare-hare a birnin Gaza bayan arangama tsakanin sojojin ƙasar da Falasɗinawa masu zanga-zangar tunawa da ƙona Masallacin Ƙudus shekara 52 da suka gabata.

    Cikin wata sanarwa a daren Asabar, rundunar sojan Isra'ila ta ce ta kai hari kan wuraren ƙera makamai huɗu a Gaza mallakar Hamas, ƙungiyar da ke iko da yankin.

    Rahotanni na cewa mutum 11 ne suka jikkata a harin.

    Hare-haren na zuwa ne 'yan awanni bayan sojojin Isra'ila sun buɗe wuta kan Falasɗinawa masu zanga-zanga a kusa da iyakarsu da Isra'ila.

    Ma'aikatar lafiya ta Falasɗinu ta ce an raunata mutum 41 ciki har da yaro mai shekara 13 da aka harba a ka.

  16. Yajin Aiki: Likitoci sun yi watsi da tayin da gwamnatin Najeriya ta yi musu

    Wasu likitoci

    Asalin hoton, Daily Trust

    Ƙungiyar likitoci a Najeriya ta Nigerian Association of Resident Doctors (NARD) ta ƙi amincewa da tayin da gwamnatin tarayya ta yi mata da zummar ta janye yajin aikin da take yi yanzu haka.

    Shugaban ƙungiyar, Dr Okhuaihesuyi Uyilawa, shi ne ya bayyana hakan yayin da yake magana da manema labarai jim kaɗan bayan kammala taron da suka yi da wakilan gwamnatin ranar Lahadi a Abuja.

    Dr Uyilawa ya ce sun ƙi saka hannu kan yarjejeniyar ce saboda akwai sakin layin da ba a fayyace musu ba duk da cewa babbar ƙungiyar likitoci ta NMA ce ta ƙulla yarjejeniyar da gwamnati.

    Tun a ranar 1 ga watan Agusta ne likitocin suka shiga yajin aikin na sai baba ta gani domin neman a biya musu buƙatunsu.

    Ministan Kwadago Chris Ngige ya miƙa batun hannun Kotun Ɗa'ar Ma'aikata domin ɗaukar mataki, inda rahotanni ke cewa gwamnati na son ta dakatar da biyan albashin likitocin da ke yajin aikin.

  17. Guguwa ta kashe mutum takwas a Mexico

    Mexico

    Asalin hoton, Reuters

    Mutum aƙalla takwas ne aka tabbatar sun rasu bayan guguwa mai laƙabin Grace ta afka wa gabashin Mexico, inda ruwan sama da iska mai ƙarfin gaske suka katse wutar lantarki.

    Mace-macen da kuma ɓarna sun afku ne a jihar Veracruz, inda iskar ta dinga wurgi da bishiyoyi a ranar Asabar.

    Titina da dama sun zama koguna a babban birnin jihar, Xalapa.

    Daga bisani guguwar ta sauya zuwa ambaliya yayin da ta sauya alƙibla zuwa sauran sassan ƙasar.

  18. Ficewar sojojin Amurka daga Afghanistan abin kunya ne - Trump

    Trump

    Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana kwashe sojojin Amurka daga Afghanistan a matsayin "mumunnan abin kunya da amsa shan kaye" ga sojojin Amurka.

    Duk da shi ne ya saka hannu kan yarjejeniyar ficewa daga kasar kafin ya sauka daga mulki, Mista Trump ya ce rashin dabara ce a ce sojoji sun fice kafin kwashe fararen hula.

    Trump na magana ne a wani gangami da ya gudanar a Alabama, inda ya ce Shugaba Joe Biden ya nuna wa duniya cewa "sakarcin gwamnatinsa ya fi na lokacin yakin Vietnam".

    A cewarsa: "Idan akwai wanda ya taɓa ganin wani abu me kama da wannan sai ya fada mani. Biden ya sa an fara ganin yakin Vietnam babban nasara idan aka kwatanta da abin kunyar da ya ke yi a Afghanistan."

    Shi ma tsohon Firaministan Burtaniya Tony Blair ya bayyana shirin Amurka na kwashe jama'a daga Kabul a matsayin "dolanci".

    A lokacin da ya ke mulki, Mista Blair ya tura ɗaruruwan sojojin Burtaniya zuwa Afghanistan.

  19. Korona ta kashe ƙarin mutum 13 a Najeriya

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 1,064 ne suka kamu da cutar korona ranar Asabar.

    Rahoton na NCDC ya nuna cewa ƙarin wasu mutum 13 sun rasu sakamakon cutar.

    Sabbin kamuwar sun fito ne daga jihohi 10 kamar haka:

    • Lagos-776
    • Rivers-143
    • Ekiti-49
    • Kwara-33
    • Ogun-21
    • Benue-18
    • Oyo-13
    • FCT-5
    • Yobe-2

    Jumilla, adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar korona a Najeriya sun kai 186,635, sai dai 168,320 sun warke. Akwai kuma mutum 2,260 da suka rasu.

  20. Barka

    Barkanmu da hantsin Lahadi, da fatan an tashi lafiya.

    Ku biyo mu domin samun rahotanni kai-tsaye na abubuwan da ke faruwa a sassan duniya.

    Umar Mikail ne ke tare da ku a wannan safiya.