Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Buhari zai rusa kamfanin man fetur na NNPC

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Awwal Ahmad Janyau and Umar Mikail

  1. Ana kama mutumin da ya yi wa matarsa saki uku nan take ta waya daga Saudiyya

    Ƴan sanda a Saudiyya sun ce sun gurfanar da wani mutum bisa zarginsa yi wa matarsa saki uku nan take ta wayar salula.

    Ba a son yin saki uku nan take a shari’ar musulunci.

    A cikin ƙorafin da ta gabatar, matar mai suna Razia Bano ta yi zargin cewa mijinta Tasabbul ya yi mata saki uku saboda iyayenta sun kasa biyan buƙatunsa na sadaki, kamar yadda ƴan sanda suka bayyana.

    Ƴan sandan sun ce ƙarar ta shafi wasu dangin Tasabbul guda takwas.

    Bano ƴar asalin ƙauyen Chak Auhadpur ta auri Tasabbul da ke yankin gundumar Mohammadpur Gaunti a ranar 21 ga watan Mayun 2005.

    Ƴan sanda sun ce bayan auren, matar ta sha wahala a hannun Tasabbul da danginsa. Kuma a cewar jami’in ɗan sanda A K Gautam ya ce a ranar Litinin Tasabbul wanda ke aiki a Saudiyya yi wa matarsa saki uku ta wayar tarho.

  2. Malam Abduljabbar Nasir Kabara ya sake gurfana kotu

    Malam Abduljabbar Nasir Kabara ya sake gurfana gaban kotu a Kano kan laifukan da ake tuhumarsa na yin kalaman tunzura jama'a da ɓatanci ga addinin Islama. Zargin da ya sha musantawa.

    A ranar 30 ga watan Yulin da ya gabata aka fara gurfanar da Abduljabbar Nasir Kabara, inda aka gabatar da takardar korafin farko.

    Gwamnatin Kano ta ce ta gurfanar da Malamin ne, wanda ta ce ya yi ƙaurin suna wajen yin wa'azin da kan haifar da mahawara, saboda zargin furta kalaman da ka iya haifar da tunzuri, da kuma bata sunan Annabin Allah''.

    Wakilin BBC da ke cikin kotun da ake sauraren ƙarar Malam Abduljabbar ya ce an tsaurara tsaro fiye da zaman kotun da aka yi a farko.

    Ya kuma ce Malam Abduljabbar a ya rame a yanayin yadda ya bayyana a sauraren ƙararsa da ake yi a kotun a ranar Laraba.

  3. Ɗaruruwan mutane suka mutu a girgizar ƙasa a Haiti

    Hukumomi a Haiti sun ce mutum 1,941 ne aka gano sun mutu a girgizar ƙasar da ta auku ranar Asabar.

    Asusun Kula da Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya wato UNICEF, ya kiyasta cewa kusan kashi daya cikin dari na mutane miliyan biyu ne a kasar suka shiga halin tagayyara sakamakon girgizar kasar.

    Wakiliyar BBC ta ce fiye da gidaje dubu 87 girgizar kasar ta rusa ko ta lalata, don hatta a shafukan sada zumunta ma ana ta yada hotunan yadda mutanen da suka rasa matsugunansu ke neman abun rufa, sakamakon yadda ake tafka ruwan sama.

    Rabon da a ga girgizar kasa irin wannan a Haiti tun 2010, lokacin da ta hallaka fiye da mutane dubu 200.

  4. Shugaban siyasa na Taliban ya dawo gida

    Rahotanni sun ce ana sa ran manyan shugabannin kungiyar Taliban, ciki har da jagoran siyasar ƙungiyar, Mullah Abdul Ghani Baradar za su isa Kabul babban birnin Afghanistan a yau yayin da suke ƙoƙarin ƙara ƙarfin ikonsu.

    Baradar na cikin manyan shugabannin Taliban da suka dawo gida a ranar Talata. Sun dawo ne daga Qatar zuwa Kandahar, tushen Taliban.

    Baradar na cikin waɗanda suka assasa Taliban, kuma yana cikin shugabannin da ke jagorantar tattaunawa da Amurka a Qatar bayan sakinsa daga gidan yari domin taimakawa ga tattaunawar sulhu.

    A 2010 aka kama shi a wani samamen dakarun Amurka a Karachi.

  5. Mutum 34 sun kamu da korona a Gombe

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 357 ne suka kamu da cutar korona a faɗin ƙasar a ranar Litinin.

    Kuma alƙalumman sun nuna cewa cutar ta sake kashe mutum shida a ƙasar cikin sa'a 24.

    Hukumar ta ce akasarin waɗanda suka kamu a ranar Talata a jihar River suke, inda aka samu karin mutum 170, yayin da a jihar Ondo aka samu mutum 38 da gwajin da aka yi musu ya tabbatar da cewa sun kamu da cutar.

    A jihar Gombe ƙarin mutum 34 suka kamu da cutar.

    An kuma samu ƙaruwar yaɗuwar cutar a Abuja babban birnin Tarayya

    Ga jerin jihohin da aka samu bullar cutar ranarTalata

    • Rivers-170
    • Ondo-38
    • Gombe-34
    • Ogun-20
    • Ekiti-20
    • FCT-18
    • Anambra-16
    • Oyo-13
    • Kwara-10
    • Imo-6
    • Bayelsa-6
    • Edo-6
  6. Maraba

    Muna maku maraba da kasance da mu a wannan shafin inda za mu kawo maku labarai da rahotanni kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sassan duniya.