Najeriya: Nan da wata shida za mu cefanar da NNPC - Timipre Sylva
Ƙaramin Ministan Mai a Najeriya Timipre Sylva ya ce nan da wata shida masu zuwa za su mayar da kamfanin man fetur (NNPC) na 'yan kasuwa.
Ministan ya bayyana haka ne ranar Talata yayin wani taron manema labarai a Abuja babban birnin ƙasar, kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Ya ƙara da cewa tuni aka kafa wani kwamati da zai tabbatar da haɗe kamfanin, inda zai koma NNPC Limited.
Ranar Litinin ne Shugaba Buhari ya sanya wa dokar man fetur hannu mai suna Petroleum Industry Bill (PIB), wadda ta tanadi mayar da NNPC na kasuwanci sannan kuma ta maye gurbin dokar da aka kafa tun 1967.
Ana sa ran gwamnati ce za ta kula da kamfanin na NNPC Limited wanda zai kasance ƙarƙashin Ma'aikatar Kudi ta Najeriya.
Mista Silva ya ce duk da cewa sabuwar dokar PIB ta janye maganar ƙayyade farashi a harkar fetur amma tallafin da gwamnati ke bayarwa zai ci gaba har zuwa wani lokaci.
Nan gaba za a fitar da cikakken tsari game da maganar ƙayyade farashin mai domin rage wa talakawa raɗaɗin abin da zai faru, a cewarsa.