Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Ba zan sauya matsayina na janye sojin Amurka daga Afghanistan ba - Biden

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, musamman halin da ake ciki a Afghanistan.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh and Nasidi Adamu Yahaya

  1. Mu kwana lafiya

    A nan za mu kawo karshen labarai da rahotanni da muke kawo muku a wannan shafi na kai-tsaye.

    Ku kasance tare da mu gobe da safe domin samun sabbin labarai da rahotanni, musamman kan abubuwan da ke faruwa a Afghanistan.

    A ko da yaushe za ku iya karanta karin labaranmu na bbchausa.com

    Kazalika za mu iya tafka muhawara a shafukanmu na sada zumunta.

  2. Ba zan sauya matsayina na janye sojin Amurka daga Afghanistan ba - Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden ya ce ba zai sauya matakin da ya dauka na janye dakarun Amurka daga kasar Afghanistan ba duk da sukar da ake yi wa gwamnatinsa.

    Ya bayyana haka ne a yayin da yake jawabi ga 'yan kasar kai-tsaye ta gidan talabijin.

    "Ba zan sauya matakin da na dauka ba," in ji Biden.

    Ya kara da cewa "a ko da yaushe ina yi wa Amurkawa alkawarin cewa ba zan boye musu komai ba", amma ya kara da cewa yadda 'yan Taliban suka yi gaggawar kwace ikon Afghanistan ya faru cikin sauri.

    Ya kara da cewa ya shaida wa 'yan Taliban cewa ma'aikatansa za su ci gaba da zama a kasar kuma idan wani mummunan abu ya same su, to kungiyar za ta dandana kudarta.

  3. Labarai da dumi-dumi, Amurka na sanya ido sosai kan abin da ke faruwa a Afghanistan - Biden

    Shugaban Amurka Joe Biden yana gudanar da jawabi game da abubuwan da ke faruwa a Afghanistan daga fadar White House.

    A jawabin, wanda yake gabatarwa kai-tsaye ta talabijin, ya ce tawagarsa kan tsaron kasa tana "sanya ido sosai" kan abubuwan da ke faruwa a Afghanistan.

    Jawabin nasa, wanda yake jawabi karon farko tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace ikon Afghanistan ranar Lahadi, ya ce ba burin Amurka ne ta zauna ta gina Afghanistan yana mai cewa babban abin da ya kai su kasar shi ne hana kai harin ta'addanci kan Amurka.

  4. Dalibai suna fargaba kan rayuwa karkashin shugabancin Taliban

    BBC ta tattauna da dalibai matasa wadanda a halin yanzu suke birnin Kabul.

    Wata mace ta bayyana birnin da cewa ya yi "tsit". Kungiyar Taliban ce take jagorancin birnin kuma kowa yana zaune a gida, a cewarta.

    "Na yi tsare-tsare da dama game da rayuwata amma ba zan iya zuwa aiki ko jami’a," in ji ta.

    "Ban san yadda makomata za ta kasance ba. Wannan lamari ya sa fatana ya gushe. Ina son barin Afghanistan domin na kammala karatuna da kuma rayuwata.

    Wani mazaunin birnin ya ce hankalinsu ya tashi bayan da suka fantsama kan tituna.

    "Muna cikin mawuyacin hali. Ba mu da kwarin gwiwa, domin kuwa kamar jiran azal muke - muna jira tamu ta same mu - su zo su kama mu," in ji shi.

    "Kowannenmu a nan yana kokarin tserewa zuwa wata kasar domin gudun kada a yanke masa hukuncin kisa".

  5. Ba za mu yi watsi da 'yan kasar Afghanistan ba - Guterres

    Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce dole ne kungiyar Taliban ta yi kaffa-kaffa wajen gudanar da mulki ta yadda za ta kare rayukan 'yan kasar.

    Da yake jawabi ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce ya "samu rahotanni game da matukar take hakkin dan adam a daukacin kasar".

    "Na damu matuka musamman game da bayanan da nake samu na keta hakkin mata da 'yan mata a Afghanistan," in ji shi.

    "Bai kamata mu yi watsi da mutanen Afghanistan ba."

    Ya yi kira ga Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi amfani da "dukkan abin da ya kamata" domin dakushe 'yan ta'addar duniya da ka iya amfani da Afghanistan sannan ya tabbatar an kare hakkokin jama'a, yana mai cewa ya kamata kowacce kasa ta karbi 'yan gudun hijira da suka fito daga Afghanistan.

    Guterres ya kara da cewa har yanzu akwai ma'aikatan Majalisar Dinkin Duniya da ofisoshinta a yakunan da ke karkashin jagorancin Taliban, yana mai cewa za su ci gaba da zama a can bisa tsarin tsaron da ke kasa.

  6. Ana zaman tashin hankali a filin jirgi na Kabul

    Hankali a tashe yake a filin jirgin sama na Kabul babban birnin Afghanistan yayin da 'yan ƙasar ke hanƙoron guduwa.

    Sojojin Amurka sun kashe wasu mutum biyu ɗauke da bindiga a yau Litinin.

    Kazalika wasu mutum uku sun mutu bayan sun faɗo daga jikin wani jirgi da suka maƙale jim kaɗan bayan ya tashi.

    Dandazon mutane sun taru a filin jirgin tun bayan da Taliban ta ƙwace iko da birnin na Kabul.

    Dakarun Amurka sun yi harbi a sama domin tarwatsa waɗanda suka yi yunƙurin shiga jirage ta ƙarfin tsiya.

  7. Buhari ya yaba wa shugaban kasar Zambiya kan karbar kaddarar shan kaye

    Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya taya dan jam'iyyar hamayya Hakainde Hichilema murna kan nasarar da ya yi a zaben shugaban kasar Zambiya da aka kammala.

    A wata sanarwa da ya fitar, Buhari ya kuma yabi 'yan kasar da suka fita kwansu da kwarkwatarsu don zaben dan takarar da suke so, yana mai cewa "gina Afirka da hadin kanta ya ta'allaka ne kan damar 'yan nahiyar su zabi wadanda suke so su mulke su.

    Sannan kuma ya yabi shugaban kasar mai barin gado kan yadda da kaddarar da ya yi ta shan kaye a zaben sa amincewa ya mika mulki cikin lumana.

    "Matakin da Mista Lungu ya dauka na amsa shan kaye daga abokin hamayya ya cancanci yabo daga dukkan masu son ci gaba dimokradiyya."

    Shugaba Buhari ya ce yana fatan yin aiki kut da kut da sabon zababben shugaban kasar don kawo ci gaban kasashen biyu.

  8. An kama maza shida da suka ci zarafin wata mace a Saudiyya

    An kama wasu maza shida da suka ci zarafin wata mace yayin da take ziyara a Riyadh, babban birnin Saudiyya, kan laifukan da sai a shekarun baya-bayan aka fara hukunci a kansu, a cewar wani mai shigar da ƙara a ranar Litinin.

    "An fara bincike a kan wasu ƴan ƙasa shida da suke cikin shekarunsu na 20 kan wani abu da ya faru da suka zagaye motar wata ƴar yawon buɗe ido suka ci zarafinsu da kalamansu da kuma ɗabi'un da suka nuna," kamar yadda wani mai shigar da ƙara ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na ƙasar SPA.

    An kama mutum shidan da ake tuhuma, waɗanda sun amsa laifin nasu, kuma an tsare su yayin da ake ci gaba da bincike, a cewar majiyar.

    A yanzu suna fuskantar hukuncin ɗaurin shekara kusan 10 a gidan yari kan laifin, a cewar majiyar.

    A baya-bayan nan aka fara ƙoƙarin magance matsalar cin zarafi a Saudiyya.

    A watan Mayun 2018 gwamnati ta ayyana cin zarafi a matsayin laifi tare da hukuncin shekara biyar a gidan yari da kuma tarar riyal 300,000.

  9. Kalli yadda mutane suke ɗane jirgin sama don neman tserewa daga Afghanistan

    Wani bidiyo ya nuna dubban 'yan Afghanistan a filin jirgin saman Kabul suna kokarin tserewa daga kasar yayin da kungiyar Taliban ta kwace iko da babban birnin.

    An ji karar harbe-harbe ranar Litinin, kuma ganau sun shaida wa BBC cewa an kashe fararen hula.

    Rahotanni sun ce dakarun Amurka sun yi harbi a iska da zummar tarwatsa dandazon jama'ar da ke yunkurin shiga jirgin kasar.

    Kungiyar Taliban ta kwace iko da kasar, kusan shekaru 20 bayan wata gamayyar dakarun tsaro da Amurka ta jagoranta ta kore su daga mulki.

  10. Labarai da dumi-dumi, Pentagon: An hana jirage sauka ko tashi daga filin jirgi saman Kabul

    Wani mai magana da yawun ma'aikatar tsaron Amurka wato Pentagon ya ce an dakatar da sauka da kuma tashin dukkan jiragen soji da na farar hula daga filin jirgin saman Kabul, babban birnin Afghanistan.

    Ba a san takamaiman lokacin da za a ci gaba da jigilar jiragen sama ba, a cewarsa.

    A halin da ake ciki dakarun Amurka na aiki tukuru domin samar da tsaro a filin jirgin saman.

    Matakin da Amurka ta dauka ya yi sanadin mutuwar mutum biyu da ke dauke da makamai, in ji Pentagon.

  11. Za a aika helikwafta birnin Jos don ayyukan tsaro

    Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce za ta aika helikwafta da kuma tawaga biyu ta 'yan sandan kwantar da tarzoma birnin Jos da ke jihar Filato domin tabbatar da tsaro.

    Sanarwar da kakakin rundunar 'yan sandan, Frank Mba, ya aike wa manema labarai ranar Litinin ta ce Babban Sufeton 'yan sandan kasar, Usman Alkali Baba ya ce jirgin zai yi aikin tattara bayanai ne da kuma taimaka wa jami'anta da ke garin.

    Kazalika sanarwar ta ce 'yan sanda sun kama ƙarin mutum 13 da ake zargi da kashe mutum kusan 30 ranar Asabar, inda suka zama 33 jumilla.

    A gefe guda kuma, jagoran rundunar bincike ta musamman da aka tura, DIG Sanusi N. Lemu, ya isa garin Jos, inda ya fara ayyukan kyautata zaman lafiya da kuma bincike.

    'Yan sanda sun ɗora alhakin kisan a kan wasu matasan ƙabilar Irigwe bayan sun tare motar matafiya Musulmai sannan suka afka musu da sara da suka, inda suka kashe mutum 25 nan take sannan suka raunata wasu da yawa.

    Matafiyan na kan hanyar su zuwa kudancin Najeriya ne bayan sun halarci taron bikin sabuwar shekarar Musulunci a garin Bauchi.

  12. Shugaban Amurka Joe Biden zai yi jawabi kan halin da Afghanistan ke ciki

    Shugaban Amurka Joe Biden zai koma Fadar White House a yau domin yin jawabi kan halin da ake ciki a Afghanistan.

    An tsara zai yi jawabin da ƙarfe 8:45 agogon Najeriya da Nijar da Kamaru da Chadi.

  13. Paralympic: Za a yi gasar nakasassu ba tare da 'yan kallo ba

    Ba za a bar 'yan kallo su shiga wasannin nakasassu ba na Paralympic da za a gudanar a birnin Tokyo na Japan saboda annobar korona.

    Masu shirya gasar sun ce gwamnatin Japan ta ƙudiri aniyar tsawaita dokar ta-ɓacin da ta saka yayin da ake shirin fara gasar ranar 24 ga Agusta.

    "Muna matuƙar nadamar yadda wannan yanayi ya shafi wasannin Paralympic," kamar yadda masu shirya gasar suka bayyana cikin wata sanarwa.

    Baya ga filayen wasanni, an buƙaci 'yan kallo kar su halarci wasannin kan titi.

    Sai dai za a ƙyale yara 'yan makaranta su halarci wasannin idan makarantunsu sun buƙaci yin hakan.

  14. An harbo jirgin yaƙin Afghanistan a Uzbekistan

    Ma'aikatar tsaro a ƙasar Uzbekistan ta ce dakarun sama sun harbo wani jirgin yaƙin soji na Afghanistan bayan da ya keta iyakarta.

    Wani mai magana da yawun ma'aikatar ya ce jirgin ya yi ƙoƙarin ratsa sararin samaniyar ƙasar ne.

    Bai san ko mutum nawa ne a cikin jirgin ba kuma ko akwai waɗanda suka tsira.

    Sai dai wani likita Bekpulat Okboyev, a kudancin yankin Surkhondaryo da ke kan iyakar Afghanistan, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an kai wasu marsa lafiya biyu sanye da kakin soji asibitinsa a ranar Lahadi da yamma.

    Ya ce dayan da ya sauka da lemar sauka ya samu karaya.

    Hukumomin Uzbekistan sun ce sojojin Afghanistan 84 ne suka shiga ƙasarta a ranar Lahadi.

    • Wani ɗan Nijar da ya zauna a Afghanistan ya yi sharhi kan Taliban

      BBC Hausa ta ji ta bakin Malam Abdurrahman Alkasum, wani dan Jamhuriyyar Nijar da ya taba zama a Afghanistan, kuma a cewarsa, ƙwace iko da ƙasar da Taliban ta yi ya zo da mamaki.

    • Wane hali ake ciki a Kabul bayan fara mulkin Taliban?

      A yau Litinin a babban birnin Afghanistan, Kabul, ta ko ina mayaƙan Taliban ne a shingayen binciken da a baya sojojin ƙasar ke tsayawa.

      Sai dai yau babu ruɗani a cikin birnin.

      Ƴan Taliban ne ke kula da cunkoson ababen hawa inda suke binciken motoci, musamman ma motocin yan sanda da na sojoji.

      Suna ƙwace motocin suna mayar da su nasu.

      A tsakiyar birnin dai rayuwa na tafiya daidai. Babu cunkoso. Yawanci shaguna a kulle suke. Amma mutane suna cikin kwanciyar hankali a yau fiye da jiya da kowa ke cikin fushi.

      Na ga ma'aurata maza da mata a kan tituna. Suna sanye da takunkuman fuska da mayafai. Suna tafiya a kan tituna, suna duk abin da suke so, kuma Taliban ba ta nuna damuwa kan hakan ba.

      Sai dai babu ƙarar sauti a kan titi. Ina wani otel ne, wanda a da sukan kunna sauti. Yau duk ba su kunna ba. Mutane na cike da tsoro. Amma dai al'amura na ci gaba da wakana a birnin.

      Amma abin da ke faruwa a filin jirgin sama ne dai babu dadin ji. Iyalai da yara da tsofaffi duk suna tafiya da ƙafa zuwa can don ƙoƙarin tserewa daga ƙasar.

      Sai dai da zarar ka tunkari ƙofar filin jirgin za ka ga ƴan Taliban riƙe da manyan makamai, suna ƙoƙarin tarwatsa mutane ta hanyar harbin iska.

      Masu son zuwa filin jirgin na haura katanga. Kowa ƙoƙarinsa shi ne ya shiga ta kowane hali.

    • Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar ƙudurin man fetur PIB

      Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan ƙudurin dokar man fetur ta 2021 wato PIB.

      Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kan yaɗa labarai Femi Adesina ya fitar ta ce shugaban ya sanya hannu kan dokar ne a yau Litinin a ƙoƙarinsa na cika alƙawarin bin dokokin tsarin mulki.

      Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar ne a yayin da ayke aiki daga gida yana killace kansa kamar yadda kwamitin yaƙi da cutar korona ya ba shi shawara, bayan komawarsa gida daga Landan.

      Za a yi bikin sanya hannu kan dokar a ranar Laraba, bayan ya kammala kwanakin killace kan.

      A karshen watan Yuni ne Majalisar Dokokin Najeriya ta amince da sabon kudirin dokar man fetur da ake kira Petroleum Industry Bill (PIB).

      'Yan majalisar da suka fito daga yankin arewacin ƙasar ne a wannan karon suka suka fi nuna goyon bayansu ga kudirin dokar, saboda abin da suka bayyana da cewa alfanun da suka hango tattare da ita.

      Sun kuma shafe lokaci mai tsawo suna tafka muhawarori domin samun masalaha wajen amincewa da wannan doka da har yanzu akasarin 'yan kasar musamman a kudanci ke nuna adawa da hakan.

      Tun a shekarar 2008 ne aka fara gabatar da kudirin dokar fetur ta (PIB) inda aka rika tafka muhawara a kanta.

      Ana kuma sa ran wannan doka za ta yi wa kowanne ɓangare da ya shafi harkar mai a kasar garanbawul.

      BBC ta tattauna da dan Majalisar Wakilai Abdullahi Mahmud Gaya, wanda shi ne shugaban kwamitin harkar man fetur game da amfanin dokar ga ƙasar.

    • China da Rasha sun ce ba za su rufe ofisoshin jakadancinsu ba

      A yayin da ƙwace ikon da Taliban ta yi da Kabul ya harzuƙa Amurka da ƙawayenta har suka kwashe ya nasu-ya nasu suka bar ƙasar, China da Rasha sun nuna ba su da sha'awar yin wani shiri na rufe ofisoshin jakadancinsu.

      China ta gargaɗi ƴan ƙasarta da kar su fita ko ina kuma su kasance cikin shirin ko ta kwana, amma kuma ta ce ta tuntuɓi ɓangarori daban-daban a Afghanistan don a ba ta tabbacin za a kare ƴan ƙasarta.

      Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta shaida kafafen yada labarai a ranar lahadi cewa, gwamnati ba ta da wani shiri na kwashe mutanenta.

      A ƙarshen watan Yuli wakilan Taliban sun ziyarci China inda suka gana da ministan harkokin wajenta Wang Yi.

      A lokacin an bayyana ganawar a matsayin amincewa da Taliban kamar wata gwamnati.

      Ma'aikatar harkokin wajen China ta ce za ta zama "ƴar ba ruwana" a cikin harkokin cikin gida na Afghanistan.

    • Bidiyon da ke nuna mutane na bin jirgin sama da gudu don ɗane shi a Afghanistan

      Wani bidiyo da aka yaɗa a shafukan sada zumunta ya nuna yadda wasu ƴan Afghanistan ke ƙoƙrin ɗane jirgin yaƙin Amurka a yayin da yake shirin tashi daga babbanfilin jirgin sama na Kabul.

      A cikin bidiyon, wanda BBC ba ta tabbatar da shi ba, an ga mutane da dama na ɗane gefen jirgin Amurkan a yayin da yake tafiya a cikin filin jirgin.

      I

      A cewar wasu rahotanni, wadanda su ma ba a tabbatar da su ba, a ƙalla mutum biyu ne suka mutu bayan faɗowa daga jirgin da suka ɗane a lokacin da yake tashi.

    • Hotunan yadda aka wayi gari da mulkin Taliban a Afghanistan

      Ƴan Afghanistan mazauna Kabul sun wayi gari ƙarƙashin mulkin Taliban.

      A ranar Lahadi ne ƙungiyar ta shiga babban birnin, a yayin da gwamnatin ta rushe kuma Shugaba Ashraf Ghani ya tsere.

      An yi ta ganin mayaƙan Taliban a kan tituna a faɗin birnin Kabul, yayin da ɗariruwan fararen hula suke tururuwar tafiya filin jirgin sama a ƙoƙarinsu na tsananin son barin ƙasar.