Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Gwamnatin Afghanistan na gab da rushewa bayan Shugaba Ghani ya fice daga ƙasar

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Fauziyya Kabir Tukur

  1. Taliban ta umarci mayaƙanta su tsaya a ƙofofin shiga birnin Kabul

    Lamarin na sauyawa cikin sauri a safiyar nan.

    Taliban ta fitar da wata sanarwa da ke umartar mayaƙanta cewa su tsaya a bakin ƙofofin shiga birnin Kabul, suna masu nuna damuwa game da fararen hula da ka iya cutuwa.

    Sanarwar ta ce har yanzu gwamnati ce ke da alhakin tsaron birnin, sannan ta ce tana tattaunawa da gwamnati domin karɓar birnin cikin ruwan sanyi.

    Kazalika ta nemi 'yan ƙasar da kar su gudu tana jaddada cewa "Taliban na son mutane daga kowane ɓangare na al'umma su zauna a ƙarƙashin gwamnatin Musulunci wadda za ta amfani kowa".

    Sai dai kuma, rahotanni na cewa ana jin ƙarar harbe-harbe sannan an ga mayaƙan riƙe da tutoci a kan tituna.

  2. Gwamnatin Afghanistan ta nemi 'yan ƙasa su kwantar da hankalinsu

    Wani saƙo da aka wallafa a sahfin Twitter na Shugaban Ƙasar Afghanistan ya nemi 'yan ƙasar su kwantar da hankalinsu duk da rahotannin cewa 'yan Taliban sun shiga birnin Kabul.

    "Ba a kawo hari Kabul ba, jami'an tsaron ƙasa na aiki da abokansu na ƙasashen duniya don tabbatar da tsaron birnin, babu wata matsala," a cewar saƙon da aka wallafa cikin harshen Pashto.

    Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta ce mayaƙan ƙungiyar na shiga Kabul ta kowane ɓangare yanzu haka.

    Kabul ne birni ɗaya tilo da ya rage a hannun gwamnatin ƙasar bayan mayaƙan Taliban sun ƙwace dukkan sauran biranen lardi cikin mako biyu da suika wuce.

  3. Taliban ta umarci mayaƙanta su guji tashin hankali a Kabul

    Ƙungiyar Taliban ta umarci mayaƙanta da su guji tashin hankali a Kabul, babban birnin Afghanistan yayin da suke yunƙurin shiga domin ƙwace shi daga hannun gwamnati.

    Reuters ya ambato wani jagoran ƙungiyar a Doha yana umartar su da su ƙyale duk wanda yake son barin garin ya fice.

    Kazalika ya buƙaci mata da su samu wajen fakewa.

  4. Labarai da dumi-dumi, Mayaƙan Taliban na shiga birnin Kabul

    Rahotanni na cewa mayaƙan ƙungiyaer Taliban na yunƙurin shiga Kabul, babban birnin Afghanistan.

    Da ma Kabul ne babban birnin da ya rage a hannun gwamnatin ƙasar bayan Taliban ta kame dukkan biranen lardin ƙasar.

    Wata majiya a Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Afghanistan ta faɗa wa kamfanin labarai na Reuters cewa yanzu haka mayaƙan 'yan tawayen na shiga birnin na Kabul ta kowane ɓangare.

  5. Fashewa ta kashe mutane masu yawa a Lebanon

    Ƙungiyar bayar da agaji ta Red Cross a Lebanon ta sanar da mutuwar akalla mutun 20 tare da jikkatar wasu da dama bayan fashewar wani tankin man fetur a birnin Al-Tleil da ke kan iyakar Syria.

    Wasu bidiyo sun nuna yadda samaniyar birnin ta yi jajir da kuma yadda mutane ke ci da wuta.

    Yanzu haka ana kan neman mutane da yawa yayin da motocin agaji ke ci gaba aikin kwasar wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

    Kawo yanzu ba a iya tantance abin da ya haddasa fashewar tankin ba.

  6. Cutar korona ta kashe ƙarin mutum takwas a Najeriya

    Ƙarin mutum 665 sun kamu da cutar korona a Najeriya cikin awa 24 da suka gabata, a cewar hukumar NCDC.

    Hukumar mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa ta ce cutar ta kashe wasu mutum takwas a ranar Asabar.

    Rahoton NCDC da ta wallafa ya ce an samu sabbin kamuwar ne a jiha 13 na ƙasar ciki har da Abuja, babban birninta.

    Jihohin su ne:

    • Lagos (369)
    • Anambra (68)
    • Oyo (63)
    • Akwa Ibom (48)
    • Kwara (28)
    • Rivers(26)
    • Edo(21)
    • Ekiti (15)
    • Ondo (13)
    • Delta (7)
    • Abuja (3)
    • Ogun (3)
    • Gombe (1)

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 181,962 ne suka kamu da cutar korona a Najeriya, yayin da 2,219 suka rasu. Sai dai an sallami 166,826 bayan sun warke.

  7. Barka

    Maraba da shigowa shafin labarai kai-tsaye. Umar Mikail ke fatan kun wayi hantsin Lahadi lafiya.

    Za mu kawo rahotannin abubuwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da kuma maƙota.

    Ku biyo mu.