Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Taliban ta sake ƙwace biranen lardi biyu

Wannan shafi yana kawo muku bayanai kai-tsaye kan abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail

  1. Yuli ne wata mafi tsananin zafi a tarihi - Ƙwararru

    Masana a Amurka sun tabbatar da cewa Yuli ne wata mafi zafi da kasar ta taɓa gani a tarihi.

    Sun ce a watan da ya gabata irin tsananin zafin da ya rika tasowa daga gulbi abu ne da ba taba gani ba tun bayan karni na 20.

    Tsananin zafin da aka yi a Amurka cikin watan Yuli ya zarta wanda aka gani shekara 142 da suka wuce, a cewarsu.

    Su ma kasashen Turai da suka hada da Italiya da Portugal da Sifaniya na fuskantar tsananin zafin da ba su saba ganin irinsa ba.

    Wakilin BBC ya ce tsananin zafi a makon da ya wuce ya kai maki 48.8 a ma'aunin salshiyos a tsibirin Sicily, wani abu daba a taba gani ba a nahiyar Turai.

    Haka ma tsananin zafin ya dinga haifar da wutar daji a sassa daban-daban na Turan.

  2. Cutar korona ta kashe ƙarin mutum 12 a Najeriya ranar Juma'a

    Hukumar daƙile cutuka masu yaɗuwa a Najeriya, NCDC, ta ce karin mutum 12 sun rasa rayukansu sakamakon cutar korona ranar Juma'a.

    Rahoton da NCDC ta wallafa a daren jiya ya ce wasu 636 sun kamu da cutar a jiha 17 na ƙasar.

    Ya zuwa yanzu, adadin mutanen da suka kamu a faɗin ƙasar sun kai 181,297, sai dai 166,709 sun warke. Akwai kuma mutum 2,211 da suka mutu.

    Jihohin da aka samu masu cutar ranarJuma'a:

    Legas -291

    Ribas -117

    Taraba -58

    Akwa Ibom -54

    Kwara -28

    Ekiti -14

    Oyo -11

    Edo -9

    Osun -6

    Bayelsa -5

    Gombe -4

    Delta -4

    Abia -3

    Flato - 3

    Sokoto -1

  3. Assalamu alaikum

    Barkanmu da hantsin Asabar tare da fatan hutun ƙarshen mako na tafiya yadda ya kamata.

    Umar Mikail ke muku maraba da sake haɗuwa a shafin rahotanni kai-tsaye.

    Za mu kawo labaran abubuwan da ke faruwa a sassan duniya a wannna rana, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.