Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kwastam ta kama hauren dala miliyan 54 a Legas

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotannin wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Sudan na shirin zama mamba a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya

    Majalisar ministocin Sudan ta amince da wani ƙudiri da zai sanya ƙasar cikin mambobin ƙasashen na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC).

    An amince da ƙudirin ne yayin da ake shirin yin wata ganawa tsakanin ministoci da kuma tawagar shugabannin ƙasar.

    "Adalci da gwamnati mai gaskiya ne ƙashin bayan sabuwar Sudan, wadda ke bin dokoki sau da ƙafa da muke muradin cimmawa," a cewar Mista Hamdok.

    Lamarin na ƙara matso da matakin Sudan kusa na miƙa waɗanda ake zargi da aikata laifukan yaƙi a yankin Darfur, ciki har da tsohon Shugaba Omar al-Bashir.

  2. Gwamnonin PDP za su yi taron gaggawa kan matsalolin jam'iyyar

    Gwamnonin babbar jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP) a Najeriya za su yi ganawar gaggawa domin tattauna matsalolin jam'iyyar bayan manyan jami'anta na ƙasa sun ajiye muƙamansu.

    Mutum bakwai daga cikin mataimakan shugabannin jam'iyyar ne suka sauka daga kujerunsu suna masu zanga-zangar abin da suka kira "rashin shugabanci na gari".

    Shugabannin sun zargi cewa ba a gudanar da shugabanci na gari da bayar da bayanan kuɗaɗen da ake kashewa.

    Sun ce za su ci gaba da yi wa PDP ɗa'a amma ba za su yi aiki da Kwamatin Gudanarwa na Ƙasa ba wato National Working Committee (NWC).

    Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa gwamnonin sun tsara ganawar gaggawa, sai dai bai faɗi rana da wurin yin taron ba.

    "Saboda haka, ƙungiyar gwamnonin PDP ta shirya taron gaggawa domin tattauna matsalolin jam'iyyar da kuma nemo mafita," a cewarsa cikin wata sanarwa a ranar Talata.

  3. Mahara sun far wa gidan minista a Afghanistan

    Ministan harkokin tsaro na Afghanistan ya tsallake rijiya da baya bayan wani hari da aka kai gidansa a Kabul, babban birnin ƙasar.

    Bismilla Khan Mohammadi ba ya gidan a lokacin da wasu ƴan bindiga suka sa abin fashewa sannan suka riƙa harba bindiga a lokacin da suka shiga gidan nasa da ƙarfin tsiya.

    Wakiliyar BBC ta ce an san cewa maharan sun shiga gidan ministan harkokin tsaron.

    "An gaggauta aikawa da jami'an tsaro na musamman kuma muna iya jiyo jirgin helikwafta yana shawagi a sama," a cewarta.

    Jami'an tsaro sun kashe duka maharan amma aƙalla wasu mutum hudu sun mutu a harin.

    Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce lamarin ya auku ne a kusa da yankin da ke ƙunshe da ofisoshin gwamnati da na diflomasiyya kuma mai yawan jami'an tsaro.

    Ta kuma ce harin na ɗauke da alamomin hare-haren 'yan ƙungiyar Taliban.

    Tuni ƙungiyar ta kama iko da kusan rabin Afghanistan tun bayan da ƙasashen waje suka sanar da janye dakarunsu daga ƙasar nan da ƙarshen Satumba.

  4. Cutar korona ta kashe ƙarin mutum uku a Najeriya

    Cutar korona ta kashe ƙarin mutum uku a Najeroiya cikin awa 24 da suka gabata, a cewar hukumar NCDC mai yaƙi da cutuka masu yaɗuwa.

    Kazalika, rahoton da hukumar ta fitar a daren Talata ya nuna cewa ƙarin mutum 505 sun kamu da cutar.

    Mutanen da suka harbu da cutar sun fito ne daga jiha 13 ciki har da Abuja babban birnin ƙasar.

    Ya zuwa yanzu, jumillar mutum 175,264 sun kamu da korona a Najeriya, 2,163 daga cikinsu sun rasu yayin da aka sallami 165,122 bayan sun warke.

    Jihohin su ne:

    • Lagos(275)
    • Rivers (63)
    • Akwa Ibom (62)
    • Gombe (22)
    • Ogun (8)
    • Abuja (4)
    • Edo (3)
    • Imo (2)
    • \Kano (1)
    • Nasarawa(1)
    • Sokoto (1)
    • Jigawa (1)
    • Ebonyi (1)
  5. Assalamu alaikum

    Marabanku da sake haɗuwa a shafin labarai kai-tsaye. Umar Mikail ke muku barka da hantsin Laraba - ta bawa ranar samu.

    Ku biyo mu domin sanin abubwan da ke faruwa a sassan duniya, musamman a Najeriya da Nijar da maƙotansu.