Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Kwastam ta kama hauren dala miliyan 54 a Legas

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotannin wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

Rahoto kai-tsaye

Umar Mikail and Umaymah Sani Abdulmumin

  1. Rufewa

    Masu bibbiyarmu a wannan shafin da haka mu ke bankwana da ku, sai kuma gobe idan Allah ya kai mu. Umaymah Sani Abdulmumin ke cewa a huta lafiya.

  2. Mutanen da ke cikin hadarin ambaliyar ruwa ya karu

    Wani bincike da aka gudanar kan ambaliyar ruwa ya nuna cewa yawan mutanen da ke cikin hadari ya karu tun farkon wannan karnin.

    Masu bincike sun gano cewa adadin mutanen a duniya ya karu da miliyan 86.

    An yi amfani da hotunan tauraron dan adam na daruruwan ambaliyar ruwan da aka yi maimakon amfani da na'ura kamar yadda aka saba yi a baya.

    Galibin karuwar ta kasance a Asiya da yankin kudu da hamadar sahara.

    Wakilin BBC ya ce mummunar ambaliyar ruwan da aka yi a Jamus da China a makwannin baya-bayan nan ta janyo asarar rayuka tare da lalata dukiya sannan kuma dubban mutane sun rasa gidajensu.

  3. Gwamnatin Najeriya ta amince da gina layin dogo da zai haɗe biranen da ke gabar teku

    Taron majalisar zartarwar Najeriya ya amince da kwangilar dala biliyan 11.17 domin gina layin-dogo da zai haɗe duk biranen ƙasar da ke gabar teku cikin shekaru 6.

    Ministan yaɗa labarai da al'adu, Lai Mohammed ne ya sanar da hakan bayan taronsu na yau wanda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya jagoranta a fadar gwamnati da ke Abuja.

    Ministan ya ce ministan sufuri, Rotimi Amaechi shi ya gabatar da yada aikin zai kasance.

    Ya ce baya ga shirin gina layin dogo da zai haɗe Kano zuwa Jibia da Fatakwal zuwa Maiduguri, wannan zai hade Legas zuwa Calabar.

    Mista Lai ya ce aikin tsohon shiri ne da suka gada daga gwamnatin baya.

  4. Ƴan Ghana sun yi zanga-zanga kan tabarbarewar tattalin arziki

    Dubban masu zanga-zangar adawa da gwamnati a Ghana sun yi tattaki a titunan Accra, babban birnin kasar domin neman gwamnati ta yi wani abu kan tabarbarewar tattalin arziki da matsalolin da jama'a ke fuskanta.

    Zanga-zangar ta samu karbuwa a watannin baya-bayan nan. Gwamnatin Shugaba Nana Akufo Addo ta bijiro da wasu sabbin tsare-tsaren karbar haraji tare da kara kudin man fetur.

    Wasu masu zanga-zangar sun soki matakin shugaban kasar na gina wani cocin kasa da ya lakume dala miliyan dari biyu inda suke ganin akwai mahimman batutuwa kamar ilimi da ya kamata a ce an duba matsalolin da suke fuskanta.

    An fara zanga-zangar cikin watan Maris lokacin da wata kotu ta kori karar yan hamayya da ke kalubalantar nasarar da shugaba Akufo Addo ya samu a zaben da aka yi a watan Disamba.

  5. Kwastam ta kama hauren dala miliyan 54 a Legas

    Hukumar kwastam a Najeriya ta kama daruruwan hauren giwa da kwanson Pangolin da ake kira dan kunya ko batoyi a wani yanki na Lekki da ke birnin Legas.

    Wannan dai shine wani kame mafi girma da hukumar kwastam ta yi a Najeriya tun bayan da aka kafa ta.

    An kama Pangolin da nauyinsa ya kai kilogram dubu goma sha bakwai da dari daya da talatin da bakwai a cikin buhuhuna dari daya da casa’in da shida.

    Akwai hauren giwa mai nauyin kilogram dari takwas da saba’in, wanda aka kiyasta kudinsu kan dala miliyan 54.

    Kwanturola janar na hukumar kwastam kanar Hamid Ali mai ritaya ya bayyanawa BBC cewa suna zargin an shigo da kayayyakin ne daga Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kokarin fataucinsu zuwa yankin Asiya.

    An dai cafke mutane uku da ake zargi da hannu a harkar fataucin.

  6. Tasirin yajin aikin likitoci a Najeriya

    A Najeriya, kwana biyu da fara yajin aikin kungiyar likitoci masu neman kwarewa an fara ganin tasirin sa a wasu abitocin da ke fadin kasar.

    Marasa lafiya da dama a asibitoci musamman na gwamnati sun shiga wani mawuyacin hali inda suke kokawa kan rashin isassun likitocin da za su duba su.

    Kungiyar dai ta ce shiga yajin aikin ya zama wajibi, saboda gwamnati ta gaza wajen cika wadansu alkawuran da ta yi mata watanni hudu da suka gabata.

    Zahraddeen Lawan ya je wani asibiti a Abuja domin gane wa idonsa, kuma ga rahoton da ya hada mana.

  7. WhatsApp ya ɓullo da sabon tsarin ɓacewar hotuna da bidiyo

    Manhajar WhatsApp ya ɓullo da sabon tsarin da zai bai wa masu amfani da shafin damar ɓatar da hotuna da bidiyon da aka aiko musu bayan dan wani lokaci.

    Bayan wanda aka aikawa hoton ko bidiyon ya bude su a karon farko, za su ''kalla sau daya'', daga nan sai ya goge da kan shi ba tare da ya fada ma'ajiyar hotuna da ke cikin wayarsa ba.

    WhatsApp ya ce an dauki matakin ne domin bai wa masu amfani da shi karin damar sarrafa shi yadda suke bukata, da samun karin kariya.

    Sai dai, masu kare hakkin yara su na nuna damuwa kan bacewar hotunan ko sakwannin ko da kuwa mutum bai bukaci hakan ba, zai taimaka kan boye wata shaida musamman idan an ci zarafin yara ta hanyar lalata.

    Dama dai ana takun saka tsakanin hukumar yaki da cin zarafin kananan yara ta kasa da kasa da uwar manhajar WhatsApp, wato Facebook kan amfani da sakon sirri.

  8. Kwalara ta kashe mutum 23 a Sokoto

    Hukumomin lafiya a jihar Sakkwato da ke arewa maso yammacin Najeriya sun tabbatar barkewar cutar amai-da gudawa a yankunan kananan hukumomi 14 daga cikin 23 da jihar ke da.

    A cewar gwamnatin jihar mutane 23 uku ne suka rasa rayukansu kawo yanzu daga cikin fiye da mutum 260 da suka kamu da ita kawo yanzu.

    An daura alhakin barkewar cutar kan rashin tsafta, da bahaya a kan tittuna da rashin mayar da hankali wajen kula da muhalli musamman lokutan damuna.

    Cutar dai ya ci gaba da yaduwa a jihohi da dama na Najeriya da sanadi rayuka.

  9. Ethiopia ta dakatar da ayyukan agaji a yankin Tigray

    Gwamnatin Ethiopia ta dakatar da ayyukan kungiyoyin agaji dake aiki a yankin Tigray na arewacin Kasar wanda yake fama da tashin hankali na watanni 9.

    Kungiyar Likitoci ta MSF ta ce an tsaida ayyukanta a yankin Tigray da kuma wasu yankuna uku na kasar.

    Ita kuma kungiyar NRC mai kula da 'yan gudun hijira ta kasar Norway, na cewa lamarin ya shafi aikace aikacenta a fadin kasar.

    Gwamnatin Ethiopian dai ta zargi kungiyar NRC da ta MSF da yada bayanai na karya.

  10. Dakarun Afghanistan sun daƙile harin Taliban a kudancin ƙasar

    Dakarun gwamnatin Afghanistan sun ce sun dakile wani harin Kungiyar Taliban kan hedikwatar yan sanda da ke Lardin Helmand a Kudancin kasar.

    Tun da farko, rahotanni na cewa mayakan sun isa wajen ginin a Lashkar Gah, babban birnin Lardin.

    Ana ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin dakarun gwamnatin da mayakan Taliban.

    A cewar wakilin BBC, yan bindiga a Kabul sun shiga gidan mukaddashin ministan tsaron kasar bayan da wani bam ya tashi a motar Jami'ai sun ce zuwa yanzu mutum takwas ne suka mutu sanadin tashin bam din.

    Kungiyar Taliban kuma ta dauki nauyin kai harin.

  11. Kotu ta ba wa Jacob Zuma damar barin kurkuku

    Wata kotu a Afirka ta Kudu ta yanke shawarar bai wa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma damar barin kurkuku na wani dan lokaci a mako mai zuwa domin ya bayyana a shari’ar da ake masa kan zargin cin hanci a Pietermaritzburg.

    Masu gabatar da kara sun nemi a gudanar da zaman ta intanet saboda dalilan tsaro da annobar korona.

    Wakilin BBC ya ce akwai yiwuwar a tsaurara matakan tsaro.

    Ana tunanin Magoya bayan tsohon shugaban kasar za su taru a wajen kotun.

    Wannan zai zama karon farko da Mista Zuma ya bayyana a bainar jama’a tun bayan kisan sama da mutum dari uku a lokacin wani rikici da fashe-fashen shaguna wata daya da ya gabata lamarin da ya janyo aka kama shi.

  12. Ana zanga-zangar fyaɗe da kuma kashe 'yar shekara 9 a Indiya

    Masu zanga-zanga sun fito a rana ta huɗu a Indiya game da zargin fyaɗe da kisa da ƙona gawar wata yarinya mai shekara tara Delhi babban birnin ƙasar.

    Iyayen yarinyar sun zargi wani malamin addinin Hindu da wasu mutum uku da kai mata hari a lokacin da ta je ɗebo ruwa a wurin da ake ƙona gawa.

    Mahaifiyarta ta an rufe ƙofofin ginin sannan an yi mata barazana a lokacin da ta nuna rashin amincewa da ƙona gawar 'yar tata.

    Tuni 'yan sanda suka kama mutanen sannan suka ƙaddamar tuhumar fyaɗe da kisa a kan su.

  13. Isra'ila ta ce ta kai hare-hare a Lebanon bayan an harba mata makamai

    Rundunar sojin Isra'ila ta ce an harba makamin roka uku a kasar daga kan iyakar Lebanon.

    Hotuna daga garin Kiryat Shimona da ke kan iyaka sun nuna wuta na tashi daga kan wni dutse a wani wuri da ake ganin a nan aka kai harin makami mai linzami.

    Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar harba makamai masu linzami kan Lebanon.

    Kawo yanzu, babu rahotannin rasa rayuka daga dukkan bangarorin.

  14. Kotu ta dakatar da 'kama Sunday Igboho ko rufe asusun bankinsa'

    Wata Babbar Kotun Jihar Oyo da ke kudancin Najeriya ba ta amince da buƙatar 'yan sandan farin kaya (DSS) da ministan shari'ar Najeriya ba ta kama mai fafutikar kafa Ƙasar Yarabawa mai suna Sunday Adeyemo, a cewar rahoton Channels TV.

    Kazalika, kotun ta dakatar da DSS da Ministan Shari'a Abubakar Malami daga tilastawa ko kuma rufe asusun banki na Mista Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho.

    Channels ta ruwaito Mai Shari'a Akintola yana bayar da umarnin bayan lauyan Igboho, Yomi Aliu (SAN), ya gabatar da buƙatar hakan.

    Da yake magana da manema labarai bayan zaman kotun, Mista Aliu ya ce "kotun ta bayar da umarnin kar a kama shi [Igboho] ko tsare shi ko kashe shi a cikin kwana 14 masu zuwa".

    Umarnin kotun na zuwa ne a ranar da DSS ɗin ta gurfanar da mabiyan Igboho 12 a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.

    Ana zargin mabiyan nasa ne da "tara makamai da nufin haddasa tashin hankali a Najeriya".

    A gefe guda kuma, wata kotu a ƙasar Benin na tuhumar Sunday Igboho da sabbin laifuka da suka haɗa da shiga ƙasar ba bisa ƙa'ida ba da haɗa baki da jami'an shige da fice da kuma yunƙurin haddasa yamutsi.

    Jami'an tsaron Benin sun kama shi ne yayin da yake yunƙurin tafiya Jamus jim kaɗan bayan ya fice daga ƙasarsa Najeriya wadda ke zargin sa da haddasa fitina da kuma yunƙurin raba ƙasar.

  15. Labarai cikin minti ɗaya

    • Tare da Umar Mikail
    • Gwamnonin babbar jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya za su yi ganawar gaggawa domin tattauna matsalolin jam’iyyar bayan manyan jami’anta na ƙasa sun ajiye muƙamansu. Gwamnan Sokoto Aminu Tambuwal wanda ya bayyana hakan ya nemi mambobin jam’iyyar su kwantar da hankalinsu amma bai bayyana lokaci da wurin da za a yi taron ba. A jiya Talata ne wasu mutum bakwai daga cikin shugabannin PDP na ƙasa suka ajiye muƙamansu bisa zargin rashin shugabanci na gari.
    • Majalisar ministocin Sudan ta amince da wani ƙudiri da zai sanya ƙasar cikin mambobin ƙasashe na Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Duniya (ICC). Lamarin na ƙara matso da matakin Sudan kusa na miƙa waɗanda ake zargi da aikata laifukan yaƙi a yankin Darfur, ciki har da tsohon Shugaba Omar al-Bashir.
    • Masu zanga-zanga sun fito a rana ta huɗu a Indiya game da zargin fyaɗe da kisa da yi aikata wa wata yarinya mai shekara tara Delhi babban birnin ƙasar.
    • An bangaren wasanni kuma, an sanar da tshohon kocin Manchester United, Louis van Gaal, matsayin sabon kocin Netherlands a karo na uku.
    • Labaran rana kenan
  16. Kotu za ta bai wa Jacob Zuma damar barin kurkuku

    Wata kotu a Afirka Ta Kudu ta yanke shawarar bai wa tsohon shugaban kasar Jacob Zuma damar barin kurkuku na wani dan lokaci a mako mai zuwa domin ya bayyana a shari’ar da ake masa kan zargin cin hanci a Pietermaritzburg.

    Masu gabatar da kara sun nemi a gudanar da zaman ta intanet saboda dalilan tsaro da annobar korona.

    Rahotanni na cewa ana sa ran tsaurara matakan tsaro saboda akwai yiwuwar magoya bayansa su hallara a wajen kotun.

    Wannan zai zama karon farko da Mista Zuma ya bayyana a bainar jama’a tun bayan kisan sama da mutum dari uku a lokacin wani rikici da fashe-fashen shaguna wata daya da ya gabata lamarin da ya janyo aka kama shi.

  17. Louis Van Gaal ya zama kocin Netherlands a karo na uku

    An sanar da tshohon kocin Manchester United, Louis van Gaal, a matsayin sabon kocin Netherlands a karo na uku.

    Ɗan ƙasar ta Netherlands mai shekara 69, Van Gaal ya maye gurbin Frank de Boer, wanda ya ajiye aikinsa a watan da ya gabata biyo bayan cire ƙasar da aka yi a zagayen 'yan 16 da Czech Republic ta yi a gasar Euro 2020.

    Van Gaal ya ja ragamar tawagar daga 2000 zuwa 2002 sai kuma a 2012 zuwa 2014, inda daga bisani ya koma Manchester United.

    Bai sake horar da wata ƙungiya ba tun bayan da United ta kore shi a 2016, sai dai ya ce komawarsa tawagar ta Netherlands "girmamawa" ce.

    "Na daɗe ina sha'awar ƙwallon Netherlands kuma horar da ita wani mataki ne na ciyar da ƙwallonmu gaba," a cewar Van Gaal.

  18. Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya killace kansa

    Shugaban Ivory Coast Alassane Ouattara ya killace kansa bayan ya yi mu'amala da wani wanda ya kamu da cutar korona.

    Sai dai ba a bayyana sunan mutumin ba.

    Shugaba Ouattara na ƙarfafa gwiwar 'yan ƙasarsa da su yi allurar rigakafi tare da bin dokokin kariya daga cutar.

    Idan killacewar tasa ta yi tsayi ba zai samu damar halartar bikin Ranar 'Yancin Kai ba a ranar 7 ga Agusta.

  19. Labarai cikin minti ɗaya

  20. NYSC: Ba waɗanda ke cikin sansani ne suka kamu da korona ba – Janar Ibrahim

    Hukumar yi wa ƙasa hidima a Najeriya ta National Youth Service Corp (NYSC) ta musanta rahotannin da ke cewa ɗalibai masu yi wa ƙasa hidimar sun kamu da cutar korona.

    Shugaban hukumar, Birgediya Janar Shuaibu Ibrahim, ya faɗa wa BBC Hausa cewa 'yan NYSC ɗin da aka ce sun kamu ba su kai ga shiga sansanin hukumar ba sannan kuma adadin bai kai wanda aka ruwaito ba.

    A safiyar Laraba ce dai jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa 'yan NYSC 109 ne suka kamu da cutar a jihohi daban-daban yayin da aka buɗe sansanin horarwa a ƙarshen makon da ya gabata don horar da ɗalibai Kashin Farko na Rukunin B na shekarar 2021.

    Janar Shuaibu Ibrahim ya ce ɗalibai 71,000 ne aka ɗiba a wannan sabon rukunin.

    "Ina so na tabbatar muku cewa waɗanda suke cikin sansani ba su da cutar saboda duk waɗanda suka zo sansani sai an yi musu gwaji, har da ni kaina," in ji shi.

    "Batun yawan waɗanda suka kamu kuma, mutum 4,5,6 ne suke kamuwa [a sansanoni] amma na ga wai ana cewa 109 ne. [hukumar] NCDC ce take da wanan bayanin, idan ka je za su ba ka. Kuma idan sun kamu muna kai su wuraren killacewa."