Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

'An kama Sunday Igboho a Cotonou yana ƙoƙarin guduwa Jamus'

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, amma zai fi mayar da hankali ne a kan bukukuwan Babbar Sallah.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh

  1. Cutar amai da gudawa ta hallaka mutum 40 a Jigawa

    Hukumomi a jihar Jigawa da ke arewacin Najeriya, sun tabbatar da mutuwar fiye da mutum 40, sakamakon barkewar cutar amai da gudawa a sassan jihar.

    Cutar dai ta bulla ne a kananan hukumomi tara ciki har da Dutse, babban birnin jihar, bayan da wasu mutane suka sha ruwan da ya gurɓata, inda fiye da mutum dubu daya suka kamu da cutar.

    Dr Salisu Mu’azu, shi ne babban sakatare a ma’aikatar lafiya ta jihar Jigawa, kuma ta waya ya yi wa Zahraddeen Lawan karin bayani.

    Ku latsa lasifikar ƙasa don sauraren hirar:

  2. Yau take Ranar Babbar Sallah

    Yau ne Musulmai a fadin duniya ke bikin Babbar Sallah da ake gudanarwa ranar 10 ga watan Dhulhajji, wata na 12 a jerin watannin Musulunci.

    Musulmai da ba su samu damar zuwa aikin Hajji ba kan yi Sallar Idi, kwana daya bayan mahajjata sun yi hawan Arafa.

    Shin wadanne abubuwa ne ake bukatar Musulmi ya yi a wannan rana?

    Tambayar kenan da Yusuf Tijjani ya yi wa Dr Muhammad Sulaiman Adam babban Limamin Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna, inda kuma ya fara bayani kan muhimmancin wannan rana.

    Ku latsa hoton da ke ƙasa don saurare:

  3. Budewa

    Masu bin mu a wannan shafi na bbhausa.com barkanmu da safiya.

    Barkanmu da Sallah.

    Sunana Halima Umar Saleh, kuma ina fatan za ku kasance da mu a yinin yau don karanta labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai dai a yau za mu fi mayar da hankali ne a kan bukukuwan babbar sallah a fadin duniya.