Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.

Koma shafi mai hoto

Samu ƙarin bayani kan shafin tattalin data

Mahajjata sun bar filin Arafa sun tafi Muzɗalifa

Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya, amma zai fi mayar da hankali ne a kan tsayuwar Arfa a yau.

Rahoto kai-tsaye

Halima Umar Saleh

  1. Huɗuba daga Filin Arafa

    Sheikh Dr Bandar Baleelah yana gabatar da huɗuba a Filin Arafa.

    Bayan kammala wannan huɗuba ne kuma za a yi kiran sallar azahar.

  2. Abin da maniyyatan da ba su samu damar zuwa Hajji ba ke ji a ransu

    Wani babban lamari da ya dauki hankalin duniya game da aikin Hajjin bana shi ne yadda hukumomin Saudiyya suka taƙaita adadin masu aikin Hajjin, inda aka bar mutum kimanin dubu sittin kacal mazauna kasar su yi aikin.

    Hukumomin sun ce sun ɗauki matakin ne saboda gudun yaduwar cutar korona.

    Kafin ɓullar cutar a shekarar 2020, miliyoyin mutane ne suke gudanar da Aikin Hajjinda duk shekara a can baya.

    A bara ma an dauki irin wannan mataki.

    Malam Yahuza Sa'idu wani mazaunin Abuja babban birnin Najeriya na daya daga cikin muliyoyin Musulman da suka yi niyyar aikin hajjin, amma matakin takaita adadin cikin shekara biyu a jere ya katse masu hanzari.

    Ishaq Khalid ya tambaye shi ko shin yaya yake ji a wannan rana ta Arfa?

    Ku latsa alamar lasifikar da ƙasa don sauraron hirar:

  3. Ɗan Denmark da ya yi zanen ɓatanci ga Annabi Muhammad, ya rasu

    Mai zanen shaguben nan a jarida dan kasar Denmark Kurt Westergaard, wanda aka fi saninsa saboda zanen da ya yi na Annabi Muhammad (SAW) wanda ya janyo ce-ce-ku-ce, ya mutu.

    Ya mutu yana da shekarun 84.

    An wallafa zanen ne a shekara ta 2006, kuma fafutikar da Musulmi masu raji suka yi ta kai ga zanga-zanga wadda ta rikide ta zamo tashin hankali a kasashe da dama na Musulmai.

    A baya an yi hakon Westergaard don kashe shi, kuma ala tilas ya arasa rayuwarsa a wani mazauni na sirri tare da kariyar 'yan sanda.

    Sake wallafa zanen a mujallar nan ta zambo ta kasar Faransa wato Charlie Hebdo a shekarar 2015 ya sa an kai wa ofishinta hari inda masu kishin Islama suka kashe mutane 12.

  4. Yau take Ranar Arfa

    Yau ce ranar Arfat, ranar da Mahajjata ke zuwa dutsen Arfa a kasar Saudiyya domin ibada ciki har da addu'o'i da kuma salloli daga safiya zuwa kusan faduwar rana.

    Shi ne dai babban jigon aikin Hajji.

    Kamar bara, a bana ma kasar Saudiyya ta takaita yawan Musulman da za su yi aikin hajjin zuwa mutum 60,000, kuma wadanda dama mazauna kasar ne kawai a maimakon mutum kusanm muliyan uku da kan yi a duk shekara.

    Manufar ita ce takaita yaduwar Korona.

    Zahraddeen Lawal ya tattauna da jakadan Najeriya a kasar Saudiyya, Alhaji Yahaya Lawal, wanda ke cikin mahajjatan na bana - domin jin irin shirin da hukumomin kasar mai tsarki suka yi wa wannan rana.

    Ku latsa hoton kasa don sauraron hirar:

  5. Budewa

    Masu bin mu a wannan shafi na bbhausa.com barkanmu da safiya.

    Sunana Halima Umar Saleh, kuma ina fatan za ku kasance da mu a yinin yau don karanta labarai da rahotanni kai tsaye na wasu abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Sai dai a yau za mu fi mayar da hankali ne a kan tsayuwar Arfa da alhazan bana ke yi a Saudiyya.