Wani jirgin saman rundunar sojin Najeriya ya yi hatsari a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin ƙasar, bayan da ƴan fashi suka buɗe masa wuta.
Jirgin yana komawa ne bayan da ya kammala wani aiki mai cike da nasara a tsakanin iyakokin jihohin Zamfara da Kaduna.
Wata sanarwa da rundunar sojin saman ta fitar ranar Litinin ta ce sai dai cikin sa'a matukin jirgin Laftanal Abayomi Dairo, ya fita daga cikinsa.
Bayan da ya tsira daga faɗuwa daga jirgin sai kuma ƴan bindigar suka buɗe masa wuta, amma ya samu sa'ar kauce musu ya kuma nemi mafaka a wani ƙauye har zuwa wayewar gari.
"Daga nan sai ya yi amfani da wayarsa don gano hanyar da za ta fid da shi, inda ya yi sa'ar kauce wa sansanonin ƴan bindigar da dama har ya isa ga wani sashe na rundunar sojin Najeriya, inda daga nan ne ya samu tsira," in ji sanarwar.
Sanarwar ta ƙara da cewa a lokacin da aka samu labarin hatsarin, sai Shugaban Rundunar Sojin Sama Air Marshal Oladayo Amao, ya bayar da umarnin cewa a yi duk ƙoƙarin da za a yi don ceton matuƙin.
"Daga nan ne sai aka yi amfani da hanyoyin leƙen asiri na rundunar sojin saman da helikwaftocin yaƙi da kuma taimakon rundunar sojin ƙasa inda aka gano wajen da hatsarin ya faru tare da ganin lemar da matuƙin ya yi amfani da ita wajen sauƙa.
Sai kuma suka ci gaba da neman matuƙin a kusa da inda lamarin ya faru.
"Abin jin daɗi ne matuƙa yadda Laftanal Dairo ya tabbatar da cewa shawagin jiragen yaƙin a wannan yanki da hatsarin ya faru ya taimaka wajen tsorata ƴan bindigar da suke neman gano shi.
"Hakan ce ta sa ya tsere musu har ya samu mafaka," a cewar sanarwar.
Rundunar sojin sama ta ce mako biyu kenan tun sanda ta fara kai samame ta sama ba dare ba rana a maɓoyar ƴan bidniga, don bin umarnin da Shugaba Buhari ya bayar cewa a zaƙulo su duk inda suke a jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara.