'Yan fashin daji sun kashe mutum 10 a Jihar Kaduna

Wasu 'yan bindiga da ake zargin 'yan fashin daji ne sun kashe aƙalla mutum 10 a yankin Zangon Kataf na Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya.
Mazauna yankin sun faɗa wa BBC cewa maharan sun shiga ƙuyukan ne da yawansu ranar Juma'a, inda suka kunna wa gidaje wuta tare da raunata mutane da dama.
Kwamishinan Tsaro, Samuel Aruwan, ya tabbatar da faruwar hare-haren kuma ya ce jami'an tsaro na binciken wasu matasa biyar da suka ɓata a garin Kafanchan.
A ranar Litinin da ta gabata ne 'yan fashin suka sako Sarkin Kajuru Alhaji Alhassan Adamu shi kaɗai bayan sun sace shi tare da wasu 13 a gidansa.
Har yanzu akwai ɗaliban sakandare kusan 120 a hannun 'yan fashin waɗanda suka sace a makarantar Bethel Baptist a Kadunan a farkon watan Yuli.











