Shugaban Mali da aka sauke ya yi barazanar kai shugaban riko kotu
Lauyan shugaban Mali na mika mulki da aka tsige, Bah Ndaw da Firai Minista Moctar Ouane ya yi barazanar kai shugaban riko na yanzu Kanal Assimi Goita kotu bisa tsare tsoffin jami'an na gwamnati, kamar yadda gidan rediyon faransa, RFI ya ruwaito.
A cewar shafin inatent na Mali, kungiyar kare hakkin bil Adama ta Amnesty International ta yi kira da gaggauta sakin tsoffin shugaban.
An tsare Bah Ndaw da Moctar Ouane a sansanin sojoji na Kati a wajen Bamako biyo bayan juyin mulkin da aka yi ranar 24 ga watan Mayu sannan daga baya aka yi masu daurin talala.
Wasu manyan kungiyoyin kasa da kasa ciki har da majalisar Dinkin Duniya da Hukumar Kasashen Afrika sun yi kira da a sake su.