Mata masu ciki sun mutu a turmutsutsun karbar abinci a Borno

Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da makwabtanta da sauran kasashen duniya

Rahoto kai-tsaye

Fauziyya Kabir Tukur and Buhari Muhammad Fagge

  1. Ban kwana

    Buhari muhammad Fagge ke fatan mu kwana lafiya.

  2. An ayyana Talata da Laraba a matsayin hutun Sallah a Najeriya

    The News Nigeria

    Asalin hoton, The News Nigeria

    Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta ayyana ranakun 20 da kuma 21 a matsayin hutun Babbar Sallah wato Eid-el-Kabir.

    Ministan cikin gida Ogbeni Rauf Aregbesola ya bayyana hakan a madadin gwamnatin kasar, ya kuma taya musulmai a fadin duniya da na Najeriya murnanr wannan rana.

    Aregbesola ya ce "Zan yi kira ga Musulmai da su ci gaba da nuna soyayya ga juna, zaman lafiya da kuma mutunta juna, kamar yadda ya zamar musu abin kwatance ga Annabi Muhammad SAW kuma su yi amfani da wannan dama domin yin addu'a ga Majeriya domin samun zaman lafiya da ci gaba da kuma daidaito.

    "Wannan na mayar da hankali ne kan ƙaruwar matsalar tsaro da ake samu a arewa maso yammacin kasar, rikicin 'yan bindiga a arewa maso gabashin da kuma matsalar sace mutane da garkuwa da su da dai sauran laifuka da ake yi a wannan kasa".

  3. An kasa cimma matsaya tsakanin Firaiministan Lebanon da Shugaban kasar

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

    Dan siyasar nan na Lebanon Saad Hariri wanda aka naɗa Firaiminista watanni tara baya, yasanar da cewa ba zai iya kafa gwamnati ba.

    Bayan wata tattaunawa da shugaban kasar Michel Aoun, ya ce abuɗe yake cewa su biyun ba za su iya cimma matsaya ba.

    Mista Hariri ya ce shugaban ya yi kiran kawo wani gagarumin sauyi cikin mukarrabansa da ya zaba.

    Mista Hariri ya miƙa wa shugaban sunan muƙarraban nasa ne a ranar Laraba,

    Lebanon na fama da matsalar tattalin arziki da ya fi kuni cikin sama da shekara 10, kuma matsalolin siyasa na kara ta'azzara lamarin.

    Wasu fisatattun masu zanga-zanga sun rika kunna wuta a kan tituna bayan da Mista Hariri ya ce ba za su iya cimma matsaya ba da shugaban kan samar da gwamnatin haɗaka.

    Reuters

    Asalin hoton, Reuters

  4. Hayaniya ta kaure a zauren Majalisun Najariya kan dokar zaɓe

    Bayanan sautiLatsa nan: ka saurari rahoton Ibrahim Isa

    Hayaniya ta kaure a majalisar dattawa da ta wakilan Najeriya yayin da `yan majalisu biyun suka muhuwara a kan kudurin dokar zabe.

    Batun kada kuri`a tare da sanar da sakamako ta hanyar amfani da laturoni ne ya haddasa rigimar.

    An dai zartar da dokar a majalisar dattawa, amma lamarin ya gagara a majalisar wakilai sai da aka kai ga

    ba wa hamata iska.

  5. An samu karuwar mace-mace saboda korona da kashi 43% a Afrika - WHO

    WHO

    Asalin hoton, WHO

    Hukumar lafiya ta duniya ta ce yawan mace-mace mutane sanadin cutar korona ya karu da kashi 43 cikin dari a makon da mu ke ciki a Nahiyar Afrika .

    Ta ce karuwar da aka samu a yawan mace-macen mutane a cikin makonni biyar da suka gabata, alama ce da ke nuni da cewa asibitoci sun kai matakin da ba za su iya ba da kulawar da ta kamata ba.

    Kasashen Afrika ta dama ba su da na'urar taimaka wa numfashi da dakunan ba da kulawar gaggawa da kuma kwararun ma’aikata.

    An saka dokar hana fita na tsawon kwanaki 10 a wasu sasan Rwanda ciki harda Kigali babban birnin kasar.

    Wannan ya biyo bayan karuwar da aka samu a yawan mutane da ke harbuwa da cutar da kuma wadanda suka rasa rayukansua a cikin mako guda

  6. Mata masu ciki sun mutu a turmutsutsun karbar abinci a Borno

    Human Right Watch

    Asalin hoton, Human Right Watch

    Rahotanni na cewa akalla mata 10 ne wadanda yawancinsu ko dai masu ciki ko kuma masu shayarwa suka mutu a yayin wani turmutsutsu wajen karbar abinci a garin Monguno da ke jihar Borno a arewa maso gabashin Najeriya.

    Wannan mummunan haɗari ya faru ne lokacin da dubban 'yan gudun hijirar da ke sansani suka fara rububin karɓar abinci agaji da aka kai musu.

    Kungiyar Red Cross ce ta rika raba abincin, wadda ta ce ba ta ji dadin abin da ya faru ba na rasa rayuka a wurin, kuma tuni ta kai kayan agaji domin taimaka wa wadanda suka ji raunuka a lokacin.

    Wata majiya ta ce jami'an tsaro sun ce mutane fun firgita suna ta guje-guje bayan an harba hayaƙi mai sa hawaye a wurin domin tarwatsa taron.

    Akwai sama da 'yan gudun hijira 100,000 da ke zaune a Monguno.

    Kuma mafi yawansu rikicin Boko Haram ne ya raba su da muhallansu.

  7. Taliban ta yi wa gwamnatin Afghanistan ta yin tsagaita wuta

    BBC

    Wani babban jamiin Afghanistan ya ce kungiyar Taliban ta yi wa gomnatin kasar tayin dakatar da bude wuta na tsawon watanni uku domin a saki fursnoninta su dubu bakwai.

    Nader Nadary wanda shi ne mai shiga tsakani na gomnati a tattunawar neman sulhu ya ce mayakan masu tayar da kayar baya sun ce suna son a cire sunnayen shugabannin kungiyar daga jerin sunnayen wadanda suka aikata miyagun laifuka na MDD.

    Sai dai y ace sakin da aka yi wa fursononin Talliban sama a dubu biyar a bara shi ne ya sa fadan ya kara rincabewa.

    Tayin baya bayanan na Taliban na zuwa ne ya yinda mayakanta ke cigaba da danawa cikin sauri wadanda kuma suka kwace yankunan da dama a kwanakin baya baya nan yayinda dakarun kasashen waje ke ficewa daga kasar

  8. Bagudu ya ce a biya albashin ma'aikata kafin sallah

    YAHAYA SARKI,

    Asalin hoton, YAHAYA SARKI,

    Gwamnan Jihar Kebbi Abubakar Atiku Bagudu ya yi umarnin a biya albashin ma'aikata na watan Yuli, ga ma'aikatan jiha da kuma na kananan hukumomi a ranar 15 ga watan Yuli 2021.

    Kamar yadda kwamishinan kudi na jihar Alhaji Ibrahim Muhammad Augie, ya bayyana hakan, yana cewa ma'aikatar kudi ta gama shirya wa tsaf wajen biyan wannan kudi ta hanyar aika kudi kai tsaye maimakon bankunan kasuwanci domin gujewa ɓata lokaci.

    Kuma ko wanne ma'aikaci zai samu albashinsa kan lokaci kuma cikin gaggawa.

    Gwamnan ya kuma yi wa kafatanin ma'aikatan jihar fatan a yi bikin salla Eid lafiya.

  9. An hana bai wa ƙananan yara kiwo a Jihar Filato

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Wata tawagar jami'an tsaro ta musamman dake aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Filato ta yi gargaɗi kan kiwon dare da kuma bai wa ƙananan yara kiwo a fadin JIhar.

    Jaridar TheCable ta ruwaito shugaban tawagar Ibrahim Ali shi ne ya yi wannan jan kunne yayin wani taro da masu ruwa da tsaki a karamar hukumar Riyom da ke jihar.

    Ali ya ce daga yanzu an dai na kiwo bayan karfe 6 na yamma, yana gargadin cewa duk wanda aka kama ya karya wannan doka za su yi maganin shi.

    "Dole a dakatar da kiwon dare, daga karfe 6 na yamma dole a daina," in ji shi.

    "Kuma dole a daina bai wa yara kanana kiwo. Ku dakatar da aika yaranku kiwo ba tare da wani babba ba.

    "Duk wanda aka kama da karya wannan doka shima za a hukunata shi.

    Ya kuma yi gargadi kan lalata amfanin gona da sace dabbobin mutane inda ya ce wannan tawaga ta su ba za ta lamunci hakan ba.

    "Ka da ku rika shiga gonar mutane da sunan kiwo, wanda aka samu da haka zai fuskanci hukunci," in ji shi.

    "Haka wanda aka samu da satar shanun mutane zai ɗandana kuɗarsa".

  10. An yi wa masu zanga-zangar da aka daure afuwa a Aljeriya saboda Babbar Sallah

    AFP

    Asalin hoton, AFP

    Shugaban Aljeriya Abdelaziz Tebboune ya yi wa mutum 101 da aka tsare a gidan yaroi afuwa, kan tuhumar hannu cikin zanga-zangar da ta karaɗe kasar a kwanakin baya.

    Za a sake su cikin gaggawa domin a gudanar da sallah Eid Adha da su tare da iyalansu wadda za a yi a makon gobe.

    Zanga-zangar da aka yi wa laka bi da Hirak an gudanar da ita ne a 2019, dsa manufar kawo sauyi kan gagarumin sauyin siyasa a kasar da ke Arewacin Afrika.

    Ita ce dai ta yi sanadin kawo karshen mulkin shugaban kasar da ya jima kan karaga Shugaba Abdelaziz Bouteflika shekaru biyu baya, kuma duk da haka ana ci gaba da tattaki a wasu sassan kasar na bukatar wani sauyi.

    An aike da yawa daga cikin wadanda suka yi zanga-zangar Hirak gidan yari - kamar yadda kungiyoyin kare hakkin dan adam suka bayyana.

    A farkon wannan watan shugaba Tebboune ya yi afuwa ga wasu gwamman dalibai da ake tsare da su a gidan yari sakamakon yin satar jarrabawa.

  11. 'Yan bindiga sun sace wani basarake a jihar Kogi

    Getty Images

    Asalin hoton, Getty Images

    Wasu 'yan bindiga sun sace wani basarake mai daraja ta biyu a Jihar Kogi da ke yankin tsakiyar Najeriya, a karamar hukumar Ajaokuta.

    'Yan bindigan sun sace Alhaji Mohammed Adembe, wanda shi ne Adogu na Eganyi, a kan hanyar Okene zuwa masarautarsa da ke garin Eganyi.

    Satar wannan basaraken ta biyo bayan wanda aka yi wa wani babban dan kasuwa a garin Okene, baya ga sace Sarkin Kajuru a jihar Kaduna ko da yake an sako shi daga baya.

    Wasu rahotanni sun bayana cewa 'yan bindigar sun kira iyalin basaraken kuma sun bukaci a biya su Naira miliyan 30 kafin a sako shi.

    Sai dai wani makusancinsa ya ce kawo yanzu ba su samu kiran waya daga masu garkuwar ba.

    Haka kuma ya bayyana cewa 'yan sanda sun bi sahun masu garkuwar amma ba su yi nasarar kama su ba.

    Sai dai BBC ba ta samu wani bayani daga 'yan sandan ba kawo yanzu.

  12. Minti Daya Da BBC Na Rana

    Bayanan sautiMinti Daya Da BBC Na Rana 15-07-2021
  13. Ambaliyar ruwa ta hallaka sama da mutum 30 a Jamus

    Germany Floods

    Asalin hoton, Reuters

    Mutum sama da talatin sun hallaka a yammacin Jamus ya yin da ambliyar ruwa da ba a taba ganin irinta ba ta afkawa wasu sassan kasar.

    Haka kuma mutane da dama sun bata.

    Iftila'in ya fi shafar jihohin North Rhine da Westphali da Rhineland da kuma Palestine bayan da aka yi ruwan sama kamar da bakin kwarya, abinda kuma ya sa bakin koguna su balle.

    Ambaliyar ruwan ta lalata gidaje da gadoji da kuma hanyoyi.

  14. Zauren majalisar wakilai ya dauki zafi kan dokar man fetur

    Petroleum Industry Bill

    Asalin hoton, Getty Images

    Zauren majalisar ya kaure da hayaniya bayan da wasu 'yan majalisar suka nuna rashin amincewa da rage kason da aka aminta a baiwa yankunan da ake tatso danyen man.

    Da farko majalisar wakilan ta amince da bai wa yankunan kaso 5 cikin 100 kamar yadda dokar PIB ta tanada amma majalisar dattawa ta rage shi zuwa kaso 3 cikin 100.

    Sai dai honourabul Chinyere Igwe na jam’iyyar adawa ta PDP ya nuna kin amincewarsa ta hanyar daga muryarsa yana kokawa kan zargin rage yawan kason da ake bai wa yankunan.

    Ce-ce-ku-cen ya ci gaba har lokacin shigowar kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, kuma ganin haka ya sa shugaban ya bukaci shuwagabannin majalisar su yi ganawar sirri kan batun.

  15. Majalisun dokokin Najeriya na tafka muhawara kan kudirin dokar yin garanbawul ga harkokin zabe

    National Assembly Building

    Asalin hoton, Facebook

    Kwamitin zabe na majalisar dattija da na wakilan Najeriya ya ce ya kammala rahotonsa kan kudirin dokar yi wa harkokin zaben kasar gyaran fuska.

    Ranar Laraba ne kwamitocin zaben biyu suka gabatar da rahotanninsu a zaurukan majalisar kan kudirin dokar.

    Sanata Kabiru Ibrahim Gaya, shugaban kwamitin kula da harkar zabe a majalisar dattijan ya bayyana wa BBC cewa kudirin wani sabon kundi suka yi hade da tsohon kudurin dokar zaben.

    ''Duk wani dan gyare-gyare da a baya aka yi yanzu duk mun hada shi a cikin kundi guda, don haka ba za a ce an je kotu ana waiwaye kan wanda aka gyara a shekarun baya ba,''

    ''A yau ne zan karanta mu kuma tattauna daga shafin farko zuwa karshe,'' ya ce.

    Sanata Kabiru Ibrahim Gaya ya bayyana irin muhimman abubuwan da kudirin dokar sauya fasalin zaben suka kunsa, wadanda ya ce ya tabo duka abubuwan da za a yi don gyara harkokin zaben.

    ''Na farko mun saka dokoki da yawa , kamar misali a wancan kudiri na baya an ce wata uku kafin zabe ake tabbatar da 'yan takara, amma yanzu mun kara lokaci saboda akwai shara'oi da ake yi na kai dan takara kotu, sai ka ga dan takara ya ci zabe amma ana shara'a a kotu,'' in ji sanatan.

    Sai dai kuma wannan kwamiti ya dauki tsawon shekara guda yana shiri kan yadda zai gabatar da rahoton na shi, wanda kuma Sanata Kabiru Gaya ya bayyana dalilan faruwar hakan da cewa saboda wasu ka'idoji ne da ake bi don tabbatar da samun nasarar kammala rahoton.

  16. Majalisar dattijan Najeriya ta umarci hukumomi kasar su mayar wa gwamnati N300bn

    Ahmed Lawan

    Asalin hoton, Twitter

    Majalisar dattijan Najeriya ta umarci hukumomin tarayya da su dawo da sama da Naira biliyan 300 da suka kashe ba bisa ka'ida ba.

    Majalisar ta umarci hukumomin da su dawo da dukkan kudaden da aka kashe ba bisa ka’ida ba daga 2013 zuwa 2015 sannan su aika da su zuwa asusun gwamnatin tarayya cikin kwanaki 60.

    Hakan ya biyo bayan rahoton da kwamitin kula da Asusun Gwamnati ya fitar kan rahoton shekara-shekara na gwamnatin na karshen shekarar 2015.

    Hukumar ta fuskanci cewa hukumar kula da da’ar maaikata ta fitar da N995m ba a bisa ka'ida ba, ma’aikatar kula da harkokin Neja Delta ta kashe Naira biliyan 1.77 ba a bisa ka'ida ba; Hukumar kula da tashar jiragen ruwa kuma Naira biliyan 68.9 da Dala miliyan 2.3 da Euro196,000; shirin inshorar kiwon lafiya ta najeriya,Naira biliyan 4.35; ofishin kasuwancin jama’a Naira biliyan 8.84; ma’aikatar albarkatun man fetur,Naira miliyan 821.9 ; hukumar kula da abinci,gudanar da magunguna da kulawa Naira biliyan 1.88 da bankin mortgage, Naira miliyan 369.

    Shugaban kamitin,sanata Mathew Urhoghide,yace an nemi hukumomin gwamnati 114 a cikin rahoton binciken na 2015,59 daga ciki an ci gaba da tambayoyin su bayan bincike.

    Sanata Ibrahim Gobir ya ba da shawarar a aika da rahoton ga hukumar ya ki da yiwa tattalin arziqi don kwato asusun.

    Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce: "shawarata ita ce za mu sa ido a kan aiwatar da hakan. Bayan daga kafa na kwana 60 za mu dauki matakin da ya dace na gaba."

  17. Lauyan Nnamdi Kanu ya ce an azabtar da shugaban 'yan awaren a Kenya

    Nnamdi Kanu

    Asalin hoton, AFP

    Lauyan Nnamdi Kani, shugaban 'yan aware na IPOB ya ce ya yi magana da shi a karon farko tun bayan da aka daure shi.

    Lauyan ya ce Kanu ya shaida masa cewa an kama shi ne a Kenya sannan aka dawo da shi Najeriya makonni kusan uku da suka gabata don fuskantar tuhumar cin amanar kasa.

    Lauyan na Mista Kanu, Mista Alloy Ejimako ya shaida wa BBC cewa an ba shi damar ganin shugaban 'yan awaren wanda ake tsare da shi a wurin tsare masu laifi na jami'an leken asirin Najeriya.

    Ya ce Kanu ya nuna alamun rashin lafiya kuma akwai raunuka a hannunsa da bayan kansa.

    A cewar lauyan, an tsare Kanu ne a wani wurin ajiye masu laifi a Kenya sannan an daure shi da sarka aka kwantar da shi a tantagaryar kasa tsawon kwanaki. Ya kuma ce an yi masa duka sannan an yi masa ukuba.

    Kawo yanzu gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani kan kalaman lauyan ba.

    Nnamdi Kanu da kungiyarsa ta IPOB, wadda gwamnatin Najeriya ta haramta, na ci gaba da rajin ballewa daga Najeriya su kafa kasar Biafra.

    Ranar 26 ga Yuli za a gurfanar da shi a gaban kotu.

  18. Buhari ya isa Kano don kaddamar da ginin sabon layin dogo

    Shugaba Muhammdu Buhari ya isa Jihar Kano da ke arewacin Najeriya, inda jirgi mai saukar ungulu ya sauke shi a Unguwar Zawaciki a ƙaramar hukumar Kumbutso a yau Alhamis.

    Shugaba Buhari ya je Kanon ne domin kaddamar da ginin sabon layin dogo daga jihar zuwa Kaduna.

  19. Za a girke dakaru 25,000 a Afirka Ta Kudu kan rikicin da ya ɓarke

    SouthA frica

    Asalin hoton, Getty Images

    Gwamnatin Afirka Ta Kudu na shirin girke dakaru 25,000 bayan shafe kwanaki ana rikici da sace-sace.

    An kashe mutum 72 a rikicin sannan an kama mutum 1,700 tun bayan kulle tsohon shugaban ƙasar Jacon Zuma a kurkuku.

    An yi sace-sace a daruruwan shaguna sannan gwamnatin ta ce tana ƙoƙari don hana ƙarancin abinci.

    Ƴan ƙasar na adana makamai da ƙirƙirar ƙungiyoyin sa kai don kare kawunansu da dukiyoyinsu.

    A ranar Laraba an samu rahotannin fasa shaguna 208 da sace duk kayayyakin cikinsu, kamar yadda gwamnatin ta ce.

    Ministar Tsaron ƙasar Nosiviwe Mapisa-Nqakula, ta ce ta gabatar da buƙatar aike dakarun ne zuwa gundumomi biyu da rikicin ya fi ƙamari - KwaZulu-Natal, inda Durban yake da kuma Gauteng, yankin da birnin Johannesburg yake.

  20. Tattalin arzikin China ya habaka

    China

    Asalin hoton, AFP

    China ta fitar da bayanai kan habakar tattalin arzikinta a zango na biyu na wannan shekara.

    Jami'ai sun ba da rahoton tattalin arzikin ya haɓaka tsakanin watan Afrilu da Yuni da maki bakwai da digo tara idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.

    Adadin dai ya ɗan yi ƙasa da hasashen masu hasashe.

    Tattalin arzikin na China da ya kai kashi 18 da motsi daga watan Janairu zuwa Maris na nuna irin farfadowar da kasar ke yi cikin sauri bayan fama da annobar korona.