Yankin arewa maso gabashin Najeriya zai kafa kamfanin sufurin jirgin sama
Gwamnonin yankin arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana cewa suna yunƙurin kafa kamfanin zirga-zirgar jiragen sama domin samar wa 'yan yankin sauƙin tafiye-tafiye.
Gwamnonin sun cimma matsaya ne yayin wani taro da suka gudanar a Jalingo, babban birnin Jihar Taraba ranar Talata.
Mahalarta taron su ne gwamnonin Borno da Yobe da Gombe da Taraba da Bauchi da Adamawa, waɗanda su ne jihohin yankin.
"Mun tattauna game da yadda sha'anin sufuri yake a yankin nan kuma mun yanke shawarar kafa kamfanin jirgin sama ta yadda mutanenmu za su samu saukin zirga-zirga," a cewar Gwamnan Gombe Muhammad Inunwa yayin hira da BBC Hausa.
Kazalika gwamnonin sun tattauna game da matsalolin tsaro da na wutar lantarki.
Saurari cikakkiyar hirar idan kuka danna hoton ƙasa: